Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Shimfiɗa
Kamar yadda duniya ba a wuri guda take tsaye ba,[1] haka ma al’amuran da suke cikinta kullum suna kan sauyawa. Waɗannan sauye-sauye sun shafi dukkannin ɓangarorin rayuwa da wanzuwar dukkannin halittu.[2] A ɓangarori da dama na rayuwa, sababbin abubuwa da zamani yake zuwa da su sukan kasance hanjin jimina, wato akwai na ci sannan akwai na zubarwa. Hakan ne kuma ya sa yake da matuƙar muhimmanci a riƙa nazartar sababbin abubuwan da zamani ya samar. Yin hakan zai ba da damar cin gajiyar alfanun da yake tattare da sauye-sauyen tare da samar da nagartattun matakan fuskantar ƙalubalen da suke tattare da su.
Fannin neman kuɗin
Hausawa babban bigire
ne da har kullum yake sanya rigar zamaninsa. Ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ21) ya zo da sauyi na musamman a wannan fannin. A ƙarnin ne aka samu bunƙasar intanet. Sannu a hankali intanet ya mamaye ɓangarorin
rayuwa, ciki har da lamarin neman kuɗi. Abin ya
kai ga matakin da a yau wasu harkokin kasuwanci da sana’o’i da ƙwadago ba sa bunƙasa
sai masu su sun rungumi duniyar intanet.
Hausawan wannan zamani ba a bar su a
baya ba wajen tsunduma cikin harkokin neman kuɗi
da suke da alaƙa da
duniyar intanet. Wannan babin ya mayar da hankali kan tattauna yadda al’amuran
neman kuɗin Hausawa suke a duniyar intanet. Hakan zai bayar da
damar ankara a duk lokacin da aka ga wani abu da yake da alamar tambaya, wato a
iya gane kura a cikin fatar akuya. Wannan zai taimaka wajen kare kai daga
damfarar da suke da alaƙa da neman
kuɗi a kan intanet.
Hanyoyin
Neman Kuɗin Hausawa
Idan ana maganar neman kuɗi a kan intanet, za a iya cewa “tun kafin a haifi uwar
mai sabulu balbela take da farinta.” Tun kafin shigowar intanet, Hausawa sun daɗe
suna neman kuɗi. Suna gudanar da sana’o’i daban-daban tare da sayar da
hajojinsu ga mutane na kusa da na nesa. Sukan yi cinikayya ko musanye/furfure[3] da
al’ummomin da suke nesa ta hanyar fatauci. A gargajiyance, manyan hanyoyin
neman kuɗi na halal ana iya raba su zuwa manyan rukunoni guda huɗu
kamar haka:
a. Sana’a
b. Kasuwanci
c. Ƙwadago
d. Fatauci
A – Sana’a
Kalmar sana’a ararriya ce daga harshen Larabci (Jangebe a
cikin Wushishi, 2011 p. 23). Ibrahim (2023 p. 218) ya
tabbatar da wannan inda ya bayyana cewa, asalin kalmar a Larabci tana da
furucin assana’atu. A Larabci tana da ma’anar yin dabara “ta yin amfani
da hikima da basira domin samar da wani abu, domin jama’a su amfana” (Ibrahim,
2023 p. 218).
A fahimtar Tanko (2000), “Sana’a
hanya ce ta amfani da azanci da hikima na sarrafa albarkatu da ni’imomi da ɗan’adam[4]
ya mallaka don buƙatun yau da kullum... Sana’a aba ce wadda ta danganci tono
albarkatun ƙasa
da sarafa[5]
hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da ɗan’adam da sha’anonin kasuwanci na saye-da-sayarwa da
ciniki da sauransu” (Tanko, 2000 p.
35).
A taƙaice ana iya cewa, sana’a ita ce hanyar amfani da fasaha da hikima da kayan aiki
domin sarrafa wani abu, musamman dangin albarkatu domin samar da wani abin
amfani da za a iya sayarwa ko musanyawa da wani abu mai daraja, ko kuma gyara
wani abin amfani da ya lalace ko tsaftace muhalli ko jiki, ko gudanar da
ayyukan samar da warakar jiki da gamsuwar zuciya domin samun kuɗi ko wani abu mai dajara kwatankwacin na kuɗi.
B – Kasuwanci
Kasuwanci yana nufin saye da sayarwa ko musanyar abubuwa
masu daraja domin samun riba, ta hanyar bin matakai da dabarun da suka haɗa da gano wurin ɗauko kaya cikin sauƙin farashi da amfani da dabarun
talla da jan hankali da tarairayar abokan hulɗa
da fikirar daɗin baki a zantukan cinikayya.
Buhari (2021) ya kawo ma’anar kasuwanci a inda yake cewa:
Kasuwanci dai yana nufin saye da
sayarwa na wani abu ko kuma haja wanda abun nan yana iya kasancewa wanda ake
gani ne kuma wanda ba a gani ne kamar mutum ya yi wani aiki a biya shi to duka
suna ɗaukar ma’anar kasuwanci. (Buhari,
2021 para. 3)
A nan za a iya lura da cewa Buhari (2021) yana da fahimtar
cewa yin aiki domin a biya mutum ma yana ɗaukar ma’anar kasuwanci. Hakan
ya faru ne a sakamakon shigar giragizai da waɗannan
kalmomin neman kuɗi suke yi wa juna.
C – Ƙwadago
A ma’ana ta ƙamusu, Sa’id et al. (2006 p. 289) an bayyana ƙwadago
da cewa shi ne “...
yi wa wani aiki don ya
biya kuɗi, musamman aikin gona.” A
fahimtar wannan ma’ana, duk wani aikin da za a aikata, sannan wanda aka yi wa
aikin ya biya kuɗi, to sunansa ƙwadago. Wannan fahimtar ta yi daidai da
wadda Umar (1983 p. 5-6) ya bayar, a inda ya ce ƙwadago “wani salo ne na sanya mutum ya yi aiki a biya shi.”
Kabakawa (2012) ya bayyana ma’anar wannan kalma
da cewa:
Kusan kowane irin aiki mutum zai
yi don a ba shi ladarsa ƙwadago
ne, amma duk da haka, ma’anar aikatau ko ƙwadago ta fi ƙarfi a kan aikin da bai wuce na
yini ɗaya ba. Saboda haka an fi samun
‘yan ƙwadago daga cikin matafiya,
kamar almajirai da ‘yan-cirani da ‘yan kakkaɓar raɓa, su ne kan kewaye gari suna neman aikin da za su yi a rana
a biya su. Kabakawa (2012 p. 41)
Za a iya lura da cewa, wannan
ma’anar ta jaddada batun cewa ƙwadago yana nufin aikin da mutum zai
yi a biya shi. Nuhu (2020 p. 198) ya bayar da ma’ana
makamanciyar wannan. Ya nuna cewa ƙwadago yana nufin “yi wa wani aiki domin biyan kuɗi.”
Lura da dukkannin waɗannan ma’anoni da aka bayar, ana iya cewa ƙwadago
nau’in aiki ne inda ma’aikacin ba shi da takamaiman
albashi da ranakun aiki ko yarjejeniyar aiki ta dindindin da wani kamfani ko ma’aikata. A maimakon haka,
yakan gudanar da ayyuka ne ga waɗanda
suka buƙaci
ya yi musu aiki, sannan a
wuraren da aka buƙaci ya yi.
D – Fatauci
Akwai ra’ayoyin da suka ginu a kan cewa, kalmomin sana’a da
kasuwanci da ƙwadago da
fatauci suna da makamanciyar ma’ana, sannan akan yi amfani da wasu a
madadin wasu. A shekarar 2018, an samu nazarin da ya ginu a kan irin wannan
ra’ayi. Abdullahi
(2018 p. 22) ya nazarci ma’anonin ƙamusu
na kasuwanci da ƙwadago da
fatauci. Daga ƙarshe
ya bayyana cewa, duk da bambancin da yake tsakaninsu ta fuskar ma’ana da yanayi da sigar aiwatarwa, Hausawa suna ɗaukar su ne a matsayin abu guda. Ma’ana a nan ita ce,
binciken Abdullahi (2018) yana da fahimtar cewa, Hausawa sukan ɗauki sana’o’i ko nau’o’in kasuwanci da fatauci
a matsayin abu guda.
Ƙamusun
Jami’ar Bayero ya kawo ma’anar fatauci da cewa: “(fataucìi, sn., nj.,) (i)
ciniki daga wannan wuri zuwa wancan. (ii) neman abu” (Sa’id, et al., 2006 p.
138). A wannan ma’ana ma ana iya lura da cewa an danganta fatauci da ciniki.
Ciniki kuwa siffa ce daga cikin siffofin kasuwanci.
A taƙaice
ana iya cewa, fatauci kasuwanci ne da ake yi da al’ummomin da suke nesa da
ainihin wurin da fataken suke. Fatake sukan ɗauki
kaya su fita fatauci zuwa wani wurin da kayan suke daraja. Yayin da suka sayar,
za su sayo wasu kayan da suke da sauƙi
a can, sannan su dawo da su garuruwansu domin sayarwa.
[1] Ilimin
kimiyya da addini da al’ada duk sun tabbatar da cewa duniya tana kan juyawa
cikin waɗansu nau’o’i da salailan
tafiya da kowanne yake da tasiri ko sakamako da yake samarwa. Domin ƙarin bayani, ana iya
duba Hukumar Binciken Tarihi Da Al’adu Ta Jihar Katsina da ‘Yar Ƙyaure (n.d.).
[2] Babu
wata halitta da lokaci ba ya tasiri a kanta. Nau’o’in tasirin da ake iya samu
yana iya kasancewa waɗanda halittun suke da
iko a kansu (misali ƙirƙire-ƙirƙire da ƙere-ƙere), ko waɗanda ba su da iko a
kansu (misali raguwar girman jikin ‘yan’adam da raguwar yawan shekaru da suke
yi a duniya).
[3]
Musanye ko furfure yana nufin tsarin ba ni gishiri in ba ka manda. Wannan
tsari ne na bayayyeniya abubuwa masu amfani musamman a lokacin da ba a amfani
da kuɗi domin yin sayayya.
[4] Haka
[5] Haka
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.