Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Intanet Ga Hausawa

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

A yau, intanet ya yi matuƙar tasiri ga rayuwar Hausawa. Wannan tasiri ya shafi ɓangarori daban-daban, tun daga harshen kansa, har zuwa adabi da al’adun al’ummar. Al’ada da harshe da adabin Hausawa duk sun samu sauye-sauye a sakamakon tasirin zamani, musamman intanet. Dansabe (2019 p. 138) yana da fahimtar cewa, kafafen sada zumunta suna taimakawa wajen haɓaka al’adun da suka haɗa da “abinci da sutura da sana’o’i da bukukuwa da tarbiyya da kuma zamantakewa.”

Shi kuwa Tahir (2016) yana ganin cewa, ta hanyar adana adabin baka a duniyar intanet ne kaɗai adabin harshe zai ci gaba da dauwama. Koma-bayan haka, sannu a hankali za a neme shi a rasa. Ya ƙara da cewa, matakin da za a iya ɗauka shi ne na adanawa da yaɗa adabin baka ta hanyar fasahar intanet. Ta haka ne za a samar da wani kandamin kundin adabin bakan (Tahir, 2016 p. 133).[1]

Wamba (2019 p. 97) ya bayyana cewa: “Bayan sauyin zamani mai ƙarfi na samuwar intanet, waƙoƙin baka sun samu haɓaka sosai.” Haɓakar waƙoƙin baka da aikin Wamba (2019) yake magana a kansa zai iya shafar:

a. Kafafen intanet da na sada zumunta da ake yaɗa bidiyoyi da odiyo-odiyo na waƙoƙin,

b. Yadda ake iya tura odiyo da bidiyoyin waƙoƙin cikin sauƙi a wayoyi da sauran na’urori dangin kwamfuta ko memori,

c. Yadda ake iya samar da manhajojin waƙoƙin sannan a ɗora su cikin rumbunan manhajoji kamar PlayStore da makamantansu

d. Yadda ake ɗaukar hannu (kwaikwayo) daga salon waƙoƙi da kayan aikin haɗa waƙoƙi na waɗansu al’umma sakamakon kallo a kan intanet

Wani abin lura shi ne, binciken matakan adanawa da bunƙasa harshe da al’ada da adabi yana da matuƙar alaƙa da juna. Lura da tasirin da zamananci yake da shi a kan intanet, Yakasai (2010 p. 126) yana ganin: “... a fili yake cewa matsalolin harshe a Nijeriya na buƙatar a yi wani abu na gaggawa domin adana harsunan gida, cikin ƙalubalen shirin zamanantar da duniya.” Ya nuna cewa, ta wannan hanya ce kawai za a iya tabbatar da cigaban harshe da kuma al’adunsa. Ya jaddada cewa: “... duk ƙasar da ba ta ga fa’idar adana harsunanta ba, to kuwa ba za ta iya adana al’adunta ba, musamman ma da yake ta hanyar harshe kawai za a iya tabbatar da ɗorewar al’ada.” Yakasai (2010 p. 123).

A ɓangare guda kuwa, yana da kyau a fahimci yadda intanet yake da gurbi na musamman a harkar tsaro a yau. Hasali ma, ƙoƙarin da ya fara samar da intanet an yi shi ne ƙarƙashin hukumar tsaro a Amurka kamar yadda binciken Gerf (2004 p. 1360) da Mukoshy, (2015 p. 21) suka tabbatar. Tasirin intanet a yau a bayyane yake. Muhimmin bagire ne na yaɗa farfagandar siyasa da yaƙin sunƙuru.

A fannin tasirin intanet a kan kasuwanci da sana’o’in Hausawa kuwa, abin kullum gaba yake ƙara yi. Ko a bayyane ana iya lura da hakan ta yadda sitatus-sitatus ɗin ‘yammata da samari da dama suke cika da tallace-tallacen hajoji daban-daban. Almajir (2013 p. 9) da Rambo (2014 para. 26) sun kawo yadda Hausawa suke ƙulla kasuwanci a kan intanet tare da amfani da katin banki wajen tura kuɗin sayayyar kaya. Aikin Mukoshy (2016) ma ya kawo yadda intanet yake taimakawa wajen samar da aikin yi da ba da damar gudanar da kasuwanci da biyan kuɗi ta kan intanet.

Lura da duk waɗannan bayanai da alƙaluma, ana iya zayyano amfanin intanet kamar haka:

1. Intanet yana taimakawa wajen samun tallafi daga masu aikin jinƙai a faɗin duniya, dangane da wata annoba ko wani aikin da ake son aiwatarwa.

2. Intanet yana taimakawa wajen yaɗa bayanai cikin gaggawa.

3. Intanet yana ba da damar bayyana ra’ayoyi cikin sauƙi, waɗanda suka shafi siyasa da zamantakewa da makamantansu.

4. Intanet yana ba da damar kallon abubuwan da suke gudana kai-tsaye a waɗansu wurare na kusa ko na nesa ta hanyar fasahar nuna faruwar abu kai-tsaye (livestreaming).

5. Intanet yana ba da damar kauce wa hasarar kuɗi da dukiya ta hanyar adana kuɗi a bankunan zamani tare da amfani da tsarin taransifa.

6. Intanet yana ba da damar samar da makarantu da halartar su a sauƙaƙe ba tare da wahalar da jiki ko neman wurin zama da bayyanannun kayan aikin koyarwa ba.

7. Intanet yana ba da damar samun bayanai masu muhimmanci game da fannonin rayuwa, kamar kiwon lafiya da tarihi da al’adu da al’ummomi da makamantansu.

8. Intanet yana ba da damar samun shawarwari daga abokai ko waɗansu mutane da suke ba da haske da ƙarfafa guiwa a kafafen intanet daban-daban.

9. Intanet yana samar da ayyukan yi ga mutane da dama.

10. Intanet yana samar da hanyoyin adana bayanai cikin sauƙi tare da kaiwa gare su a duk lokacin da ake buƙata.

11. Intanet yana samar da hanyoyin gudanar da kasuwanci a sauƙaƙe.

12. Intanet yana taimaka wa lafiyar ƙwaƙwalwa a matsayin wani abokin hira da ɗebe kewa.

13. Intanet yana taimakawa a ɓangaren tafiye-tafiye, ta hanyar taswirorin wurare kamar Google Map da makamantansu.

14. Intanet yana taimakawa a ɓangaren tsaron ƙasa da na yankuna da na ma’aikatu.

15. Intanet yana taimakawa wajen adana muhimman bayanai da suka shafi al’adu da adabi da harshe da tarihi da sauran nau’o’in ilimummuka daban-daban.

16. Intanet yana taimakawa wajen aikin haɗin guiwa cikin sauƙi tsakanin mutanen da suke da nisa da juna.

17. Intanet yana taimakawa wajen duba yanayi tare da tsara gudanar da lamura ta la’akari da yanayin da ake sa ran fuskanta, kamar ruwan sama ko iska da sauransu.

18. Intanet yana taimakawa wajen gwagwarmayar neman ‘yanci, musamman ta hanyar shirya zangazangar lumana da tattauna ra’ayoyi da mafita game da waɗansu ƙalubalen danniya ko wariya ko rashin adalci da al’umma take fuskanta.

19. Intanet yana taimakawa wajen kai saƙo ko samun saƙo daga wata uwa duniya, ko tura buƙatar wani abu kamar kiran direban mota da makamantansu.

20. Intanet yana taimakawa wajen rage cunkoson ababen hawa yayin da ya kasance mutane na ayyuka daga gida a maimakon zuwa ofisoshi.

21. Intanet yana taimakawa wajen sadarwa a sauƙaƙe.

22. Intanet yana taimakawa wajen samar da dandali da gidajen nishaɗantarwa.

23. Intanet yana taimakawa wajen samun ƙwararrun ma’aikatan wucin-gadi (freelancers) domin gudanar da ayyuka masu buƙatar ƙwarewa da fasaha.

24. Intanet yana taimakawa wajen samun sababbin abokai.

25. Intanet yana taimakawa wajen sanya ido ga gida ko wurin aiki yayin da ake wani wuri na daban, ta hanyar kyamarorin zamani da suke tura hotuna da sautuka da bidiyoyi ta intanet.

26. Intanet yana taimakawa wajen fahimtar al’adun al’ummomi cikin sauƙi.

A ƙasashen da suka ci gaba, kusan ana dogaro da intanet a wajen aiwatar da komai, tun daga sayan abinci da shiga mota da hawa jirgi da kwatance da neman bayanai game da wani abu da kusan dukkanin sauran lamuran rayuwa.

Duk waɗannan (da ma waɗansu da wataƙila tunani bai kai kan kansu ba) suna daga cikin nau’o’in alfanun da intanet ya zo da su, waɗanda kuma Hausawa suna daga cikin al’ummomin da suke cin gajiyarsu.



[1] A Ingilishi ya rubuta cewa: “The possible action that we take is to preserve and promote our oral traditions by the use of digital technology, creating a comprehensive database of our oral traditions.”

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments