Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Masu iya magana sukan ce: “Idan an bugi jaki, sai a bugi taiki.” A wannan gaɓa, ya kyautu a fahimci cewa tasirin da ake samu bai taƙaita ga wanda intanet yake yi a kan Hausa da Hausawa ba. Su ma Hausawa suna da tasiri a kan intanet. Ana iya fahimtar hakan tun daga yadda ake samar da gurabu da ba da kulawa ta musamman ga Hausa da Hausawa a intanet.
A fannin kasuwancin kan intanet, an sanya Hausa a matsayin ɗaya daga cikin harsunan da ake mu’amala da su a kan kafar
hadahadar kuɗin intanet ta Paxful (https://paxful.com) a farkon shekarar 2021. Wannan yana nuni ga muhimmancin harshen
Hausa da al’ummar Hausawa a kan wannan kafa da tasirin da suke da shi na yin
ciniki a cikinta. A duba hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 1.5: Zaɓin Harshen Hausa a Kan Kafar
Paxful
Madogara: Shafin shiga akawun ɗin Paxful (https://accounts.paxful.com/login/)
Tasirin Hausa a duniyar intanet
ya kai wani mataki inda har ta samu shiga cikin jerin harsunan da ake amfani da
su a kafar Facebook. “Yanzu haka masu amfani da shafin da dama suna yi ne ta
hanyar amfani da harshen Hausa a matsayin harshen umurni” (Morison a cikin ’Yartsakuwa, 2017 p. 26). Masu amfani da Facebook suna
da damar mayar da saitin akawun ɗinsu
cikin harshen Hausa.
Bayan haka, kamfanin Facebook yana
ba da dubban ɗaruruwan
rubuce-rubuce da aka yi a kan Facebook domin a fassara su zuwa harshen Hausa.
Duk wani rubutu da aka yi kan Facebook cikin wasu harsuna daban, mutum yana da
damar duba fassarorinsu cikin harshen Hausa. Idan ya kasance ba a fassara su
zuwa Hausa ba a daidai lokacin da aka duba, injin Facebook zai yi ƙoƙarin
fassara su ta hanyar amfani da ilimin makamantan fassarori da suka gabata.
Hoton da yake ƙasa ya kawo misalin akawun ɗin
Facebook cikin harshen Hausa:
Hoto 1.6: Tsarin Facebook
Cikin Harshen Hausa
Madogara: Akawun Ɗin Abdulrahman Muhammad Manga na Facebook
A hoto na 1.6 da yake sama, za a
iya lura da cewa akawun ɗin
Facebook ɗin cikin
harshen Hausa yake. Dukkanin ɓangarorin
akawun ɗin an rubuta
su cikin harshen Hausa. Haƙiƙa wannan ci gaba ne sosai ga harshen. Hakan kuwa ya samo asali
ne sakamakon tasirin da Hausawa suke da shi a wannan kafa ta Facebook,
sakamakon yawansu da yanayin amfaninsu da kafar.
Yayin da aka binciki jerin harsunan da
ake iya amfani da su a kan Facebook, za a tarar da cewa ba su kai ɗari da hamsin (150) ba (har
ya zuwa ranar 17 ga watan Fabarairu na shekarar 2024). Kada a manta da cewa,
harsunan duniya ba su gaza dubu bakwai (7,000) ba (Bunza, 2019 p. 7). Ko Yoruba da Igbo da suke bin
Hausa cikin harsunan Nijeriya ba su da gurbi a Facebook.
Bugu da ƙari, kamfanin Gogul ya daɗe da bai wa Hausa
muhimmanci. Yakan fitar da dubban ɗaruruwan
jumloli da kalmomi a-kai-a-kai domin fassara su zuwa Hausa. Kamfanin yana da
injin fassara wanda aka fi sani da Google Online Translator (Injin Fassara
na Gogul na Kan Intanet). Daga cikin harsunan da suke kan wannan tsari
har da Hausa. Kasancewar harshen Hausa a kan wannan kafa na nuni da tasirinta a
duniyar intanet. Manyan kamfanonin da suke ire-iren waɗannan
muhimman ayyuka, ba sa yi har sai idan akwai wani alfanu da za su samu daga
hakan.
Gazawar injin fassara na Gogul
shi ne, yana iya kasancewa a ci karo da fassarar da ba ingantacciya ba. Hakan
yana faruwa ne kasancewar yayin da jumlar da aka bincika ba ta da fassara a
cikin injin, to injin zai ƙirƙiri fassararta. Zai ƙirƙiri fassarar ne ta hanyar amfani da
ilimin fassarori makamantanta da suke kan injin. A kullum kamfanin yana ƙara
inganta tsarinsa na fassara. A ƙasa an ba da misalin fassara mai inganci
da marar inganci waɗanda
aka ɗauko daga injin fassara
na Gogul ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2024:
Hoto 1.7: Fassara Mai
Inganci Daga Injin Fassara na Gogul
Madogara: https://www.google.com/search?q=english+to+hausa
A hoto na 1.7 da yake sama, za a
iya lura da cewa fassarar da injin na Gogul ya bayar tana da inganci. A ƙasa an
kawo misalin fassara mai rauni (a duba hoto na 1.8):
Hoto 1.8: Fassara Marar
Inganci Daga Injin Fassara na Gogul
Madogara: https://www.google.com/search?q=english+to+hausa
A hoto na 1.8 da yake sama, za a
iya lura da cewa, fassarar da injin na Gogul ya bayar tana da rauni. Ya fassara
“liar” a matsayin “karya” a maimakon “maƙaryaciya”. Bayan haka, bai yi amfani da baƙin /ƙ/ mai ƙugiya
ba. Ko bayan haka, an yi amfani da Bagwariyar Hausa (suka ce) wanda hakan yake
nuni da fassarar injin ce kai-tsaye.
Ko bayan Gogul, akwai waɗansu injunan fassara a
kafafen intanet waɗanda
Hausa take ɗaya daga
cikin harsunan da suke kansu (supported languages). Wasu kuwa ƙamusoshin
fassara ne daga cikin harshen Hausa zuwa wasu harsuna daban, ko kuma daga wasu
harsuna zuwa harshen Hausa. A ƙasa an kawo misalan wasu daga ciki:
1. Bargery Online Dictionary (Ƙamusun
Bargery na Kan Intanet). Adireshinsa shi ne: http://maguzawa.dyndns.ws/.
2. Hausa Dictionary (Ƙamusun
Hausa). Adireshinsa shi ne: http://hausadictionary.com/Main_Page.
3. Stars 21 (Taurari 21).
Adireshinsa shi ne: https://www.stars21.com/translator/english_to_hausa.html.
4. Translation 2 (Fassara 2).
Adireshinsa shi ne:
https://translation2.paralink.com/English-Hausa-Translator/.
5. Translator (Mai fassara).
Adireshinsa shi ne:
https://imtranslator.net/translation/hausa/to-english/translation/.
Bugu da ƙari, akwai manhajojin
fassara daban-daban da ake iya amfani da su a kan wayoyin salula. Ana iya sauƙe
ire-irensu daga rumbunan manhajoji kamar PlayStore ko F-Droid da sauransu,
kamar yadda za a ga misalansu a nan ƙasa:
Hoto Na 1.9: Misalan
Manhajojin Fassara Zuwa Harshen Hausa
Madogara: Rumbun Manhajoji na PlayStore.
A ɓangare
guda kuwa, kafar Wikifidiya (Wikipedia) fitacciya ce a duniyar intanet.[1]
Da wuya a binciki wata kalma a injin nema na Gogul ba tare da an ci karo da zaɓin Wikifidiya ya fito a
shafin farko ba. Rubuce-rubucen wannan kafa sun shafi dukkanin ɓangarorin rayuwa tun daga
kan siyasa da zamantakewa da addini da tarihi har zuwa kiwon lafiya da harsuna
da al’adu da dai sauransu. A yanzu haka, wannan kafa ta fara samar da bayanai
cikin harshen Hausa.[2]
Babu makawa wannan kafa za ta taimaka wa harshen matuƙa wajen yaɗuwa da yayatuwa a duniya.[3]
A ƙasa
an kawo misalin shafin farko na wannan kafa cikin hoto.
Hoto 1.10: Kafar Wikifidiya ta Hausa
Madogara: Shafin farko na Wikifidiyan Hausa (https://ha.wikipedia.org/wiki/Babban_shafi)
A hoto na 1.10 da yake sama, za a
iya lura da cewa wannan shafi na Wikifidiya cikin harshen Hausa yake. A zuwa
lokacin da aka ɗauki
hoton (ranar 28 ga watan Fabrairu, shekarar 2024), an ɗora
rubuce-rubuce da Hausa guda dubu talatin da takwas da ɗari biyar da sittin da bakwai (38,567) a kansa. Wannan ya
nuna yadda shafin yake ci gaba sosai. Dalili kuwa shi ne, a ranar 25 ga
watan Maris na shekarar 2020, maƙalun da suke kan shafin sun kasance dubu
huɗu da ɗari bakwai da tara (4,709)
kawai.
Za a iya fahimtar wani tasirin
Hausawa a kan intanet daga al’amarin da ya faru na dakatar da ayyukan Tuwita
(Twitter) a Nijeriya (5 ga watan Yunin shekarar 2021 zuwa 13 ga watan Janairun
shekarar 2022). Duk da cewa wannan ya shafi Nijeriya ne baki ɗaya, ba Hausawa kawai ba, Hausawan suna daga cikin waɗanda ake yawan kallon rubuce-rubucensu a kan wannan kafa.
Katse harƙallolin
Tuwita a Nijeriya ya janyo
wa kamfanin hasarar kuɗaɗe
masu tarin yawa.[4]
Adadin Hausawan da suke kan
manhajar TikTok ma suna nuni da tasirinsu a kan intanet. Dubban Hausawa maza da
mata ne suke amfani da wannan kafa. Suna gudanar da harkoki daban-daban tun
daga kan abin da ya shafi barkwanci da nishaɗantarwa
da wa’azantarwa har zuwa kan koyar da nau’o’in ilimi daban-daban.[5]
[1] Domin ƙarin bayani a kan wannan kafa ana iya duba https://wikipedia.org.
[2] Shafin
farko wanda ake kira “gida” (home page) na Hausa da yake kan kafar Wikifidiya
yana da adireshi kamar haka: https://ha.wikipedia.org/wiki/Babban_shafi.
[3] Ya
rage ga masana da manazarta Hausa da su shiga a dama da su cikin harkar bunƙasawa da inganta wannan kafa. Koma bayan haka, kafin a farga, ɓarnar
da za a yi wa Hausa a ilimance ba za ta misaltu ba!
[4] Domin
samun ƙarin bayani, ana iya duba BBC Hausa (2022).
[5] Za a
kawo cikakken bayanin harkokin Hausawa a kan TikTok a babi na huɗu.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.