Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
A yau, intanet ya zama wani ɓangare na rayuwar al’umma. A cikin giraf na 1.1 da 1.2 da aka kawo a ƙarƙashin 1.2.5 a wannan babi na ɗaya, za a ga cewa a shekarar 1991 ne aka samar da kafar intanet ta farko. Ya zuwa shekarar 2017, adadin kafafen intanet sun kai biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai da sitting (biliyan 1.76). Adadin ya sauka a shekarar 2018 da 2019. A 2019, adadin kafafen intanet ya kasance kimanin biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai da ashirin (biliyan 1.72). Adadin na kafafen intanet ya ƙara yawa a shekarar 2020 da kuma 2021. A shekarar 2021, adadin kafafen intanet sun kai biliyan ɗaya da miliyan ɗari takwas da tamanin (biliyan 1.88). Duk waɗannan alƙaluma suna nuni ne ga yadda duniya ta rungumi al’amarin intanet.
A ɓangare
guda kuwa, sama da rabin mutanen duniya ne suke amfani da intanet. An samu
wannan rahoto daga ƙididdigar da Statista ta yi a farkon shekarar 2020. A
yayin rubuta rahoton a kafar Statista, Clement (2020
para. 2)
ya bayyana cewa:
Almost 4.54
billion people were active internet users as of January 2020, encompassing 59
percent of the global population.
Fassara
Ya zuwa watan
Janairu na shekarar 2020, masu amfani da intanet sun kai kimanin biliyan 4.54,
wanda hakan ya kai kashi 59 na adadin mutanen duniya.
Giraf 1.3: Adadin Masu Amfani da
Intanet a Watan Janairu na Shekarar 2020
Madogara: Climent, (2020 para. 2)
Ko bayan adadin mutanen da suke
amfani da intanet, masu cuɗanya
da duniyar intanet a kullum abin dubawa ne. Kowace kafa aka ɗauka za a tarar da akwai
adadin mutane da suke ziyarta tare da gudanar da al’amura a kowace rana (wata
ta fi wata yawan maziyarta kwatankwacin ficenta da amfaninta). Wannan bincike
ya yi yunƙuri
ɗauko hadahadar
duniyar intanet da yake wakana a yanzu (shekarar 2024). Wannan yunƙuri ya
ci tura sakamakon bayanan kai-tsaye daga kafar da aka dogara a kanta wajen
samun waɗannan alƙaluma
sun ƙafe
a wannan lokaci, kamar yadda za a gani a cikin hoton da yake ƙasa:
Chen et al. (2002
p. 6)
sun nazarci ayyuka daban-daban da aka gudanar game da tasirin intanet a kan
al’ummomi. Ayyukan da suka nazarta sun haɗa da na Nie (2001) da Wellman (2001) da Nie et al. (2002). Bayan nazartar ayyukan, sun
fitar da nau’o’in tasirin da intanet yake yi kan al’umma kamar haka:
i. The Internet decreases
community (Intanet yana samar da koma-baya ga al’umma)
ii. The Internet transforms
community (Intanet yana kawo sauye-sauye ga rayuwar al’umma)
iii. The Internet supplements
community (Intanet yana samar da wata al’umma ta daban)
Koma-baya da intanet yake
haifarwa ga al’umma ya shafi fannonin rayuwarsu daban-daban. Daga cikinsu akwai
yadda al’amuran nishaɗi
da ɓata lokaci da intanet
yake ƙunshe
da su suke ɗauke wa
mutane hankali da shagaltar da su. A haka ne al’umma take rungumar intanet a
maimakon yin amfani da lokutansu wajen aikata ayyukan da za su taimake su a ɗaiɗaikunsu, ko a matakin al’umma.
Intanet ya zo da manyan sauye-sauye guda biyu,
masu amfani da waɗanda
suke mazaunin ƙalubale.[1]
A ɓangare guda kuwa,
al’umma ta daban da intanet yake samarwa yana nufin al’amura da hulɗa da suke wanzuwa a duniyar
intanet. Haka kuma, ya shafi yadda halaye da ɗabi’un mutane suke sauyawa
sakamakon hulɗa da intanet.
Za a ƙara fahimtar tasirin
intanet yayin da aka nazarci tasirin kafafen sada zumunta ga zamantakewar yau.
A duniyar yau, kafafen sada zumunta sun zama wani ɓangare na rayuwar al’umma. Kusan za a iya
cewa, duniyar mafi yawan mutane ba za ta iya rayuwa ba sai da su. Dalili kuwa
shi ne, rayuwar mutanen ta dogara kacokan a kan ire-iren waɗannan kafafe. Nan ne cin
su, nan ne shan su![2]
Binciken Ceci (2019 para.
3)
ya nuna cewa, masu amfani da kafar Whatsapp a watanni kaɗan bayan samar da kafar sun kai kimanin
biliyan guda da miliyan ɗari
biyar (1,005,000,000). Binciken da Jayasekara (2015) ya gudanar kuwa, ya nuna
cewa, ana samun ƙaruwar masu amfani da kafafen sada zumunta matuƙa a
kullum wayewar garin Allah Ta’ala.
Masana da manazarta da dama sun
yi bincike da rubuce-rubuce game da tasirin kafafen sadarwa a zamantakewa.[3]
Misali, Siddiqui & Singh sun bayyana cewa:
Nowaday’s social
media has been the important part of one’s life from shopping to electronic
mails, education and business tool. Social media plays a vital role in
transforming people’s life style. (Siddiqui &
Singh, 2016 p. 71)
Fassara
A yau, kafafen
sada zumunta sun zama wani muhimmin ɓangare
na rayuwar ɗan’adam
tun daga kan sayayya da tura saƙonni da ilimi har zuwa kasuwanci. Kafafen
sada zumunta suna taka muhimmiyar rawa dangane da salon rayuwar mutane.
Lallai wannan batu haka yake,
domin kuwa ko a ƙasar Hausa akwai mutane da dama da suka raja’a matuƙa kan
kafafen na sada zumunta. Akwai muhimman ɓangarorin
rayuwa da waɗannan
kafafe suka fi shafa. Daga ciki akwai:
i. Biɗa
da tanadi
ii. Ilimi da karantarwa
iii. Nishaɗantarwa
iv. Sada zumunta
v. Tattaunawa a matakin ɗaiɗaiku ko ƙungiyoyi
Tun farko dai waɗannan kafafe an samar da su
ne domin sada zumunta. Misali, Facebook da aka samar a wajajen 2004, ya kasance
hoɓɓasa ne na ɗalibin Jami’ar Harvard mai
suna Mark Zuckerberg. Ya ƙirƙiri Facebook ne a matsayin kafar sada zumunta tsakanin ɗaliban makarantar ta
Harvard. Sannu a hankali ɗaliban
wasu makarantu na daban suka fara amfana da ita.[4]
A shekarar 2006 ne kuma aka fitar da ita a matsayin kafar sada zumunta da
duniya gaba ɗaya za ta
iya amfani da ita (Baruah, 2012 p.
4; Ceci, 2019 para.
2).
A zuwa yau, Facebook ne yake kan gaba a duk cikin kafafen sada zumunta. Ga wasu
fitattun kafafen sada zumunta tare da adadin mutanen da suke da akawun da su:
Jadawali Na 1.2: Kafafen
Sada Zumunta da Adadin Masu Akawun a Kansu
|
Kafa |
Masu Akawun |
|
Facebook |
2,980,000,000 |
|
YouTube |
2,500,000,000 |
|
WhatsApp |
2,240,000,000 |
|
Instagram |
2,350,000,000 |
|
TikTok |
1,090,000,000 |
|
Snapchat |
750,000,000 |
|
Twitter (X) |
540,000,000 |
|
LinkedIn |
950,000,000 |
|
Pinterest |
465,000,000 |
|
Reddit |
430,000,000 |
Madogara: Chukwuere (2021)
da Leventhal, et al (2021)
[1] Sauƙaƙa sadarwa da kasuwanci da sauran nau’o’in hulɗoɗin al’umma
cigaba ne da ya samu a sakamakon intanet. A ɓangare guda
kuwa, akwai al’amuran da intanet ta zo da su waɗanda suka
kasance koma-baya ko cikas ga al’adu da kuma zamantakewa. Sun haɗa da
satar bayanan sirri da yaɗa alfasha da mugun aiki da cusa miyagun aƙidu da makamantansu.
[2] A shekarar 2019, kafar intanet ɗin nan mai suna Sitatista da take
adana bayanai dangane da kafafen intanet ta fitar da ƙididdigar ma’aikatan Fesbuk. Ta bayyana cewa, a shekarar 2018, ma’aikatan sun kai dubu ashirin da biyar
da ɗari ɗaya da biyar (25,105). Ko bayan
Fesbuk akwai manyan kafafen sada zumunta da suke da ɗimbin
ma’aikata. Daga ciki har da Tuwita da TikTok da makamantansu.
[3] Wasu
daga cikin rubuce-rubucen sun haɗa da na Baruah (2012) da Korkmaz et al. (2014) da Owusu-Acheaw & Larson (2015) da Siddiqui & Singh (2016) da Dansabe (2019).
[4]
Makarantun da suka fara amfani da kafar sun haɗa da Columbia
da Yale da Stanford (Ceci, 2019 para. 2).
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.