Ticker

6/recent/ticker-posts

Samuwar Kafafen Intanet (Websites, Blogs, Social Media)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Ɓullar kafafen intanet sun samar da wani sabon al’amari a duniya. Intanet wani gida ne ko farfajiya ko rumbu da akan ƙirƙira. A cikinsa ne ake ajiye bayanai iri-iri. Za a riƙa bin wasu tsararrun hanyoyi wajen kaiwa ga wannan gida tare da ta’ammuli da kayayyakin da suke cikinsa. Binciken Armstrong (2019) ya tabbatar da cewa, an ƙirƙiri intanet na farko a shekarar 1991. Tim Berners-Lee da yake aiki a CERN (European Organization for Nuclear Research) a Siwizalan (Switzerland) shi ya fara ƙirƙirar kafar intanet a shekarar 1991. Ƙunshiyar kafar ta kasance game da intanet da yadda ake amfani da ita. Liƙau ɗin da ya yi amfani da shi a wancan lokaci shi ne http://info.cern.ch. Domin ƙarin bayani dangane da kafafen intanet, ana iya duba Armstrong (2019 para. 1).

Daga wancan lokaci aka ci gaba da samun ɓullowar kafafen intanet da bunƙasarsu. Ya zuwa shekarar 2016, kafafen intanet sun kai biliyan guda. Giraf da yake ƙasa yana ɗauke da ƙarin bayani.

Giraf Na 1.1: Adadin Kafafen Intanet a Duniya

Madogara: Armstrong (2019 para. 1)

A giraf na 1.1 da aka kawo a sama, za a ga tarihin samuwar kafafen intanet a taƙaice. A shekarar 1991 kafar intanet guda ɗaya aka samu. A 1992 adadinsu ya kai goma. A wajajen 2016, wannan adadi ya kai biliyan guda. Bayan haka, giraf ɗin ya nuna shekarun da aka samar da wasu muhimman kafafen intanet kamar su:

a. Yahoo (Yahu) a shekarar 1994

b. Google (Gogul) a shekarar 1998

c. Facebook (Fesbuk) a shekarar 2004

d. YouTube (Yutub) a shekarar 2005

e. Instagram (Insitagiram) a shekarar 2010

A shekarar 2021, Armstrong ya faɗaɗa wannan bincike. Sabon binciken ya nuna cigaba da aka samu ta fuskar ƙaruwar adadin kafafen intanet da ake da su a duniya. A duba sabon giraf ɗin da ya samar a ƙasa:

Giraf Na 1.2: Adadin Kafafen Intanet a Shekarar 2021

Adadin Kafafen Intanet a Shekarar 2021

Madogara: Armstrong (2021)

Yayin da aka nazarci giraf na 1.1 da 1.2 da aka kawo a sama, za a tabbatar da cewa duniya tana ƙara rungumar lamarin intanet. A shekarar 2019, akwai ƙiyasin kafafen intanet miliyan dubu ɗaya da ɗari bakwai da biyu (biliyan 1.72). Ya zuwa shekarar 2021 kuwa, sai ga adadin ya ƙaru zuwa miliya dubu ɗaya da ɗari takwas da tamanin (biliyan 1.88). Wannan ya nuna cewa, a cikin shekaru biyu kacal, an samu ƙaruwar kimanin kafafen intanet miliyan ɗari da sittin (miliyan 160) a duniya.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments