Ticker

6/recent/ticker-posts

Illolin Intanet Ga Hausawa

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Intanet hanjin jimina ne, akwai na ci akwai na zubarwa. Duk da ɗumbin alfanun da yake tattare da intanet, ya zo da tarin matsaloli da ƙalubale. Daga cikinsu akwai waɗanda suka kasance gama-gari. Akwai kuma waɗanda suka shafi al’ummar Hausawa kai-tsaye (da sauran al’ummu da suke da al’adu da falsafa irin na Hausawa).

Rambo (2014 para. 42-56) ya kawo waɗansu illolin intanet ga Hausawa da suka haɗa da taɓarɓarewar tarbiyya da yaɗa ƙarya da haddasa gaba da kuma tonon silili. Haka kuma, yana da fahimtar cewa intanet yana daga cikin dalilan da Hausawa suka rungumi rayuwar ƙarya a yau, musamman domin burgewa a kafafen sada zumunta. Wannan fahimta ta yi daidai da ta Umar (2012 p. 119-127) inda har ya jaddada cewa, wayoyin zamani suna daga cikin dalilan mace-macen auren Hausawa a yau.

Masana da manazarta daban-daban sun bayyana yadda intanet yake da tasiri a kan Hausa da Hausawa. Aikin Dansabe (2019) ya fi mayar da hankali a kan yadda intanet yake tasiri a kan al’ada da adabi. Dansabe (2019 p. 143) ya zayyano illolin intanet musamman kafafen sada zumunta kamar haka: (a) gurɓata tarbiyya da (b) koyar da shigar fitsara da (c) koyar da fasiƙanci da (d) durƙusar da adabin Hausa.

Gobir & Sani (2021 p. 117-120) sun nuna yadda intanet da kafafen sada zumunta suke haifar da dusashewar wasannin gargajiya na Hausawa, musamman wasannin kwaikwayo. Hakan yana faruwa ne yayin da hankula suke karkata a kan wasannin zamani da suke kan na’urori. Dusashewar wasannin kuwa yana haifar da gushewar danƙon zamantakewa da cuɗanya tsakanin yara. A hannu ɗaya kuwa, yana haifar da dusashewar waɗannan al’adu masu matuƙar taimakon yara a fannin motsa jiki da fasaha da ilimantarwa da koyar da lissafi da sauran dabarun zaman duniya.

Ta la’akari da waɗannan ayyukan da suka gabata, ana iya zayyano illolin intanet ga Hausa da Hausawa kamar haka:

1. Intanet yana iya kasancewa hanyar damfara da zamba. Ma’ana a nan ita ce, intanet ya samar da sabuwar hanyar damfarar al’umma musamman waɗanda ba su naƙalci yaya al’amuransa suke ba.

2. Akan yi amfani da intanet domin cin mutunci ko ɓata suna ga wani mutum ko waɗansu mutane.

3. Ana iya dogaro sama da ƙima a kan intanet wanda hakan naƙasu ne ga bunƙasar basirar mutum. Wannan ya haɗa da neman kowane nau’in bayani ko mafita a kan intanet kai-tsaye ba tare da amfani da basira wajen ƙoƙarin samun mafita ba.

4. Aurar intanet yana iya haifar da naƙasu ga koyon muhimman lamuran zamantakewa, kamar jawabi ga mutane ko zurfafa tunani da yanke hukuncin da ya dace game da abubuwan da suke buƙatar nazari.

5. Yana iya zama ƙalubale ne ga sirrin duk wani mai amfani da ita.

6.  Yana haifar da salwantar waɗansu abubuwa/sassa na adabin baka.

7.  Yana haifar da taɓarɓarewar zamantakewa.

8.  Yana iya haifar da matsalolin da suka shafi rashin barci yayin da yake ɗauke wa mutum hankali daga bin tsarin hutun da ya dace a bisa yanayin halittar ɗan’adam.

9.  Yana janyo ɓata lokaci da koma-baya ga gudanar da ayyuka yadda suka kamata.

10.  Yana kame zuciya ta yadda har akan ƙwallafa rai da rungumar ta ba-ji-ba-gani.

11. Ƙwallafa rai a kan intanet yana iya haifar da ƙaurace wa al’umma da zaman kaɗaici sama da ƙima wanda hakan ka iya shafar lafiyar mutum.

12. Labaran ƙarya suna da saurin yaɗuwa sakamakon intanet.

13. Mutane suna hasarar kuɗaɗe a kan intanet yayin da suka ɓata datarsu ba ta hanyar wani abin da yake mai amfani a gare su ba.

14. Tarbiyya tana iya gurɓacewa ta dalilin intanet.

15. Tasirin intanet yana haifar da mutuwar al’adu.

16. Yawan amfani da intanet yana iya illata lafiya, misali yin ƙiba sama da ƙima yayin da aka auri intanet, ko kuma ciwon ido na ɗan lokaci yayin da aka tsananta kallon fuskar na’ura.

17. Tsabagen neman suna ko tirendin ta hanyar kafar intanet yana iya jawo aikata wasu ayyuka na assha da yawan baɗala da batsa, a wasu lokuta har ma da abubuwan da za su iya illata rayuwa, kamar shan ruwan kwata ko zuba toka ko gawayi a jiki. Ire-iren waɗannan abubuwa suna iya kai mutum ga halaka ko kuma mutum ya ci na jaki a banza wajen neman suna.

Naɗewa

Intanet yana da matuƙar tasiri ga rayuwar alummar duniya baki ɗaya. Kusan dukkannin al’amuran duniya a yanzu suna da alaƙa da intanet ko ana alaƙanta su da shi domin sauƙaƙawa. Intanet ya zo da sauye-sauye masu yawa a rayuwa. Daga cikinsu akwai da dama waɗanda suka kasance alfanu yayin da suke sauƙaƙa lamura ta hanyar janyo nesa kusa da game-duniya. A kullum Hausawa suna sake rungumar lamarin intanet a inda ake samun ƙaruwar kafafen intanet da suke buɗewa. A ɓangare ɗaya kuwa, lamarin intanet yana tattare da ƙalubale. Ɗaya daga cikin manyan ƙalubale da ya zo da su, shi ne damfarar duniyar intanet. Yanzu tun da an ga maanar damfara da kuma maanar intanet da tasirinsa a kan Hausawa, babi na gaba zai mayar da hankali a kan lamuran neman kuɗi a intanet. Wannan batu ne mai muhimmanci, domin yawanci ta hanyar neman kuɗi ne ake samun damar damfarar mutane.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments