𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malan dan Allah inada tambaya? Na kusan yin aure to Amma na fahimci Wanda zan aura mutun ne Mai son mace Mai yalwar gashi nikuma Banda shi dayawa kamar yadda na fahimta to Ina iya siyan hulunan gashi domin indinga yimishi ado dasu bayan munyi aure ?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To baiwar Allah ai
ita kanta hular gashin haramun ne sanyata kamar yadda malamai sukace matukar
mace ba gwagwuyayyen kaine da ita ba ma'ana kanta babu gashi to be halatta ta
sanya hular gashin ba Sabida haka matukar karancin gashinki be zama aibu a
garekiba cikin sauran mata babu wani bukatar sai kin sanya hular gashin domin
shi gashi halittane wata tafi wata yalwar gashi kinga kuwa ba dole sai gashinki
ya zamo irin na wacce tafiki yawan gashi ba, idan ma kina son gashinki sai ya
kara tsawo to kawai kibi halattatun hanyoyin karin gashi da ake bi domin kara
tsawon gashi kamar amfani dasu coconut oil dasauransu.
An yiwa majalisar
koli na malamai masu fatawa na duniya tambaya game da Hukuncin sanya hular
gashi ga matar aure domin yin kwalliya ga majinta, Sai suka bada amsa da cewa:
Ma'aurata ya kamata su janyo hankalin junansu ta hanyar da shari'a ta amince
gwargwadon yadda Zamantakewarsu zata kara karfi, saidai banda aikata abubuwan
da suka haramta a shari'a suka cigibada da cewa; Sanya hular gashi ya samo
asaline daga gurin matan da suke ba musulmaiba, sune aka sani suna amfani dasu
kuma wannan ɗaya ne daga cikin
nau'in canza halittarsu. Idan mace ta sanya hular gashi tayi ado ma kanta koda
tayi hakan domin mijinta ne wanda kuma manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya hana kwaikwayon su, duk wanda yake kwaikwayon wasu mutane to shima
yana cikinsu, sanya hular gashi itama tana daga kwaikwayonsu Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hana kwaikwayonsu kuma yayi tsinuwa ga wanda
yake yin hakan. (Fataawa al-Lajnah al-Daa’imah, 5/191.)
Sabida haka mu wannna
zauren muna kan fahimtar majalisar koli ta malaman lajhan Al'daa'imah ta kasar
saudiyya, Kenan muma a wajenmu baya halatta ki sanya hular gashin domin kiyiwa
mijinki kwalliya da ita, akwai hanyoyin jan hankalin miji masu yawa da shari'a
ta amince dasu basai ta hanyar sanya hular gashi ba, koda kunyi auren idan ya
umarceki da aikata hakan to sai kiyi kokarin fahintar dashi illar yin hakan
cikin ladabi sanyayawa, girmamawa da tausasawa in sha Allahu zai fahimceki
fahimta mai kyau.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.