Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarkon Rajista Domin Damfara a Kan Intanet (Subscription Traps)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Akwai tarin manhajoji da kafafen intanet da suka kasance na kyauta. Ire-irensu ba sa buƙatar a biya kuɗi kafin yin rajista. Akwai kuma manhajoji da kafafen intanet da suka kasance na kuɗi, waɗanda ba a iya amfani da su har sai an biya. Wasu kuwa, suna da tsari biyu, akwai na kyauta akwai kuma na kuɗi. A masu tsari biyu, na kyauta yakan kasance ba cikakke ba. Ma’ana dai, akwai wasu abubuwa da ba a sanya a ciki ba (alhali an saka su a wanda aka biya kuɗi). A wasu lokuta kuma, akan cika na kyauta da tallace-tallace waɗanda sai mutum ya gan su kafin ya ci gaba da amfani da manhajar ko kafar intanet ɗin.

‘Yan damfara sukan ja hankalin mutane ta hanyar sauƙaƙa kuɗin rajistar wata kafa mai ƙayatarwa. Suna kuma iya saka tsarin yin rajista na gwaji bisa kyauta (free trial). Wurin da tarkon yake shi ne, idan damar rajistar gwaji suka bayar, za su saka tsari mai wahalar fita yadda dole sai an caji wanda ya yi rajistar gwajin kuɗi kafin ya samu damar fita. Idan kuwa sassauci suka yi a shekara ko wata ko zangon farko na yin rajista, to za su ƙara kuɗi mai yawa yayin sabunta yin rajista. Idan mutum ya riga ya gina kasuwancinsa a kan rajistar da ya yi, zai zamo masa dole ya biya wannan kuɗi mai tsada don gudun rasa kwastomomi.

A wasu lokutan, har kafafen da ba na damfara ba sukan bi tsari makamancin wannan. Babban misali a nan shi ne, Sashen Harsuna da Al’adu (FUGUS) (http://delac.fugus.digital) da Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya (YUMSUK) (https://www.yumsuk-hausa.digital) sun sayi sunan kafafen (domain names) laburarensu bisa farashi mai rahusa, dala tara ($9). A shekarar sabunta rajista, sai kuɗin ya koma dala talatin da tara da ɗigo goma sha shida ($39.16).

Fitattun misalai a ƙarƙashin wannan nauin damfarar kan intanet sun haɗa da:

1. Ɓoyayyen Tarkon Biyan Rajista Na Adobe (Adobe’s Hidden Fee Subscription Trap)

Yana da kyau a tuna cewa, Adobe (https://www.adobe.com) yana ɗaya daga cikin amintattun kamfanonin da ake yawan amfani da kayayyakinsu a duniya. Da wuya ka samu Bahaushen da yake amfani da kwamfuta ba tare da ya san sunan wannan kamfani ba. A watan Mayu na shekarar 2024, Hukumar Kula Da Harkokin Kasuwanci wato Federal Trade Commission (FTC) ta tuhumi kamfanin Adobe cewa suna yaudarar mutane ta hanyar ƙaƙaba musu wani ɓoyayyen kuɗin rajista. Wannan yaudarar tana tilasta wa mutane biyan kuɗin rajista alhali ba a son ransu ba. Domin samun ƙarin bayani, ana iya duba Rayo (2024).

2. Rajistar Boge Ta Taimako a Fannin Intanet Da Na’urori Na Kamfanin Tech Live Conncet (Tech Live Connect's Tech Support Subscription Scam)

An tuhumi kamfanin Tech Live Connect (https://www.techliveconnect.com) kan wani tsarin rajista na yaudara. Kamfanin ya fitar da wani tsarin yin rajista na wata-wata wanda ya shafi taimakon mutane game da matsalolin da suka shafi intanet da na’urori. An kawo wannan bayani a kan FTC News on Tech Support Scams (https://www.ftc.gov/news-events/news/press-releases/2024/03/ftc-settles-tech-support-case) da Scamwatch Report (https://www.scamwatch.gov.au/types-of-scams/remote-access-scams).

3. Imel Ɗin Damfara Mai Alaƙa Da Geek Squad Ɗin Kamfanin Best Buy (Best Buy Geek Squad Email Scam)

Best Buy (https://www.bestbuy.com) amintaccen kamfani ne wanda yake a kasuwar duniyar intanet. Geek Squad wani reshe ne da yake aiki da wannan kamfani. An tura wani saƙon imel na damfara mai alaƙa da rajistar Geek Squad ga wata mata da take zaune a Kolorado. An nuna mata cewa wata rajistar da ta yi ta lalace, sannan aka ba ta lambar da za ta kira. Wannan alamari ya haifar mata da hasarar kuɗin da ya kai dalar Amurka dubu ashirin ($20,000). Domin samun ƙarin bayani, a duba Cruz (2024).

Wannan nau’in damfarar ba zai zama baƙo ba ga waɗanda suke aiki da imel. Sau da dama akan turo ire-iren saƙonnin nan da sunan cewa daga wasu kamfanoni amintattu suke. Faɗawa tarkonsu zai kai mutum ga hasarar kuɗaɗe masu yawa.

4. Damfarar Da Ta Shafi Aika Kaya Daga Amazon (Amazon Fake Order Scams)

Amazon (https://www.amazon.com) amintacciyar kasuwar kan intanet ce. Ita ce kasuwar intanet mafi girma a duniya. Kamfanin Amazon ya gargadi mutane da su yi hattara da ire-iren saƙonnin imel na damfara waɗanda ‘yan damfaran kan intanet suke turawa da sunan Amazon. Yawanci sukan tura saƙon ne a matsayin cewa an samu wata matsala game da kayan da ake ƙoƙarin tura wa mutum daga amazon. Daga nan sai su buƙaci mutum ya tura wani kuɗi ko wasu keɓantattun bayanai da za a iya amfani da su domin damfarar sa ko damfarar waninsa. Domin ƙarin bayani, ana iya duba Tatananni (2024).

5. Damfarar Tatsar Bayanai Da Sunan Netflix (Fake Netflix Phishing Scams)

‘Yan damfarar kan intanet sukan tura saƙonnin imel a matsayin cewa daga kamfanin Netflix ne. Sukan yi hakan domin tatsar keɓantattun bayanan mutane musamman waɗanda suke da alaƙa da biyan kuɗi (misali, bayanan katin banki da sauransu). Sukan fake da cewar mutum ya samu matsala a rajistarsa ta Netflix, don haka yana buƙatar saka wasu bayanai. Domin ƙarin bayani game da wannan nau’in damfarar, ana iya duba Proctor (2024).[1]



[1] Domin samun ƙarin bayani game da matakan kare kai daga damfara a kafar Netflix, ana iya ziyartar https://help.netflix.com/en/node/13243.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307 

Post a Comment

0 Comments