Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfarar Soyayya a Kan Intanet (Romance Scam)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Wannan wani nau’in damfara ne da ake gudanarwa a kan intanet. Masu wannan damfara sukan fito wa wanda suke son damfara ta fuskar soyayya. Idan mace za su damfara, za su fito mata a matsayin namiji wanda yake son ta. Idan kuma na miji za a damfara, za a fito masa a matsayin mace ce. A nan za mu bayar da misali da damfarar soyayya da ake yi wa maza.

‘Yan damfara sukan yi amfani da dabarun jan hankali daban-daban da za su sa a yarda cewa mace ce kyakkyawa take son soyayya da wanda suke shirin damfara. Ana iya tuntuɓar wanda za a damfara ta imel ko kafafen sada zumunta kamar Facebook ko WhatsApp, da makamantansu. Za a iya tura masa hotuna waɗanda aka ɗauka a lokuta daban-daban (hotunan mace) domin dai a ja hankalinsa ya yarda cewa da mace yake tattaunawa.

Idan an tuntuɓe shi ne da sunan cewa Baturiya ce daga Turai, ana iya masa ƙaryar cewa matar tana sha’awar baƙaƙen fata ne. Ana kuma iya masa ƙaryar cewa matar tana son aure ne daga Afirka domin samun damar kawo ziyara. Wani lokaci kuma ƙaryar takan kasance cewar matar ta gaji da soyayya da ‘yan uwanta Turawa saboda mayaudara ne. A wasu lokutan kuma, za a iya ƙaryar cewa matar tana da kuɗi ne masu yawa, duk masoyanta suna son ta ne saboda kuɗinta, wanda hakan ya sa ta nemo wani salihin bawa a kan intanet domin samun soyayyar gaskiya.

Burin ire-iren waɗannan ‘yan damfarar zai iya kasancewa tatsar bayanai. Idan a nan suka taƙaita, cikin sauƙi suna iya samun bayanan da suke nema yayin da wanda aka tuntuɓa ya yaudaru. A ɓangare ɗaya kuwa, za ta iya yiwuwa kuɗi ake son tatsa daga mutumin.

Wannan littafin ya ci karo da Hausawa biyu da suka faɗa komar ‘yan damfarar soyayya a kan intanet a shekarar 2024. Ɗaya a jahar Bauchi yake, ɗaya kuma a jahar Kebbi.[1] Dukkanninsu biyu an tuntuɓe su ta Facebook da sunan Baturiya ce wadda ta faɗa soyayya da su. Bayan sun ɗan tattauna da ita, sai ta buƙaci su yi kiran bidiyo da wata manhaja (video call). A nan suka nuna mata cewa ai ba su da kwamfutar da za su iya yin hakan.

Matar ta jinjina lamarin sannan ta ce za ta turo musu kwamfuta da babbar waya saboda soyayyar da take tsakaninsu. Bayan bai fi kwana ɗaya ba, ta ɗauki hoton sabuwar kwamfuta da sabuwar waya ta turo musu, har ma da bidiyo tana bayanin cewa wannan kyauta ce zuwa gare su. Daga nan kuma ta nuna cewa ta turo saƙon domin a kawo musu Nijeriya.

Bayan kamar kwana ɗaya, sai aka tuntuɓe su da lambar Nijeriya cewa daga filin jirgi ne a Legas. Saƙonsu ya iso, akwai buƙatar su turo kuɗin rajistar karɓar saƙo (clearance fee). An turo musu hoton takardar saƙon kaya ɗauke da sunayensu da bayanansu na tuntuɓa da adireshi, tamkar dai na gaske. Dukkanninsu biyu an sanar da su kuɗin da bai fi dubu ashirin ba (20,000).

Cikin zumuɗi suka tura kuɗin da aka buƙata. Bayan sun tura ne kuma aka dawo musu da saƙon cewa ai ba abin da ake nufi ba ke nan. Akwai kuɗin da za su biya wanda ya kai kimanin dubu arba’in da biyar (45,000). A wannan gaɓar ma, ‘yan damfarar sun ɗauki hoton kwamfutar da waya a cikin kwali domin su tabbatar wa waɗanda suke son yi wa damfarar cewa zancen gaskiya ne.[2]

Wannan labari yana nuni da yadda ‘yan damfarar kan intanet suke shirye tsaf domin yaudarar mutane. Wani zai yi mamakin ta yaya har ita Baturiyar ta yi bayanin cewa ga saƙo ta aiko, kuma a cikin bidiyo? Sannan ta yaya ta turo musu hotunanta a lokacin da suke tattaunawa a kan Facebook? Wannan abu ne mai sauƙi. Za su iya ɗauko bidiyon wata mata a kafafen sada zumunta kamar TikTok ko Facebook da sauransu, a inda take wannan bayani na tura saƙo. Suna ma iya yanko wani ɓangare na fim. Daga nan za su gyara bidiyon yadda zai dace da abin da suke son aiwatarwa. Dangane da hotuna kuwa, za su bi akawun ɗin matar a Instagram ko wani wurin da ake ɗora hotuna domin su tattaro hotuna daban-daban waɗanda aka ɗauka a lokuta mabambanta.



[1] Waɗannan su ne waɗanda aka samu damar tattaunawa da su. Littafin ya samu labaran Hausawa daban-daban waɗanda aka tunkara da irin wannan damfarar. Waɗansu sun faɗa tarkon, wasu kuma sun tsallake.

[2] A wannan gaɓar ne kuma Allah ya sa zancen ya kai gare mu, inda muka tabbatar musu da cewa damfara ce.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments