Ticker

6/recent/ticker-posts

Manhajar Fansa Domin Damfara a Kan Intanet (Ransomeware)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Wannan tsarin damfara ne inda ake tura wata manhajar kutse zuwa na’urar mutum. Manhajar za ta kulle masa wasu muhimman fayilolinsa ko ta jirkita aikin na’urar. ‘Yan damfarar za su buƙaci ya biya wani kuɗin fansa kafin su buɗe masa. A ƙasa an kawo misalan wasu manhajojin fansa da shekarun da aka yi amfani da su:

a. Conti (2020 – 2022)

b. CryptoLocker (2013)

c. DarkSide (2021)

d. GandCrab (2018 – 2019)

e. Locky (2016)

f. Maze (2019 – 2020)

g. Petya/NotPetya (2016 - 2017)

h. REvil (Sodinokibi) (2019 – 2022)

i. Ryuk (2018 – har yanzu ana amfani da shi)

j. WannaCry (2017) - Wannan ɗaya ce daga cikin manhajojin fansa da suka fi yaɗuwa a lokacinsu. Ta yi tasiri a kan na’urori kimanin dubu ɗari biyu (200,000) a ƙasashe daban-daban a faɗin duniya da suka kai ɗari da hamsin (150).

Ana iya bin hanyoyi daban-daban domin tura ire-iren manhajojin kutsen nan zuwa na’urar mutane. Ana iya tura shi a matsayin saƙo ta imel ko wasu manhajojin tura saƙonni na daban. Wannan ne ya sa yake da matuƙar muhimmanci mutum ya riƙa takatsantsan da ire-iren saƙonnin da yake buɗewa a kan na’urorinsa.

Daga cikin rubuce-rubuce da aka yi dangane da manhajojin fansa da tasirinsu a duniya, akwai ayyukan Li & Liao (2021) da Couture (2024). Ana iya duba su domin samun ƙarin bayani.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments