𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salam Malam Ina kwana ya family. Malam Dan Allah ina son Karin bayani akan Wanda zai ɗauki alkawari amma sai ya ƙi cikawa, misali zai ce rana kaza zan ba ki Abu kaza kuma in lokacin ya yi sai ya ki badawa, Dan Allah mlm Ina son jin karin bayane akan haka.
HUKUNCIN SAƁA ALKAWARI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusalam
warahmatallahi wabarakatuh
Allah Ya ce: ku cika
alkawarin da kuka dauka, domin shi alkawari abin tambaya ne a ranar alkiyama.
Ma'ana Zai zama Azaba ga wanda bai cika Alkawarin da ya ɗauka
ba. Sannan Allah ya kara Cewa; Sune Waɗanda
Suke Cika Bakance/alkawari domin suna tsoron wata rana da sharrin wannan ranar
abin gudu ne. Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa babu
imani ga wanda ba shi da amana, babu addini ga wanda bashi da alkawari.
Sabida haka kenan Indai ba
Akasi Aka samu ba. Akwai Matsala ga wanda ya kasa cika alkawarin da ya ɗauka.
Domin Sai ya ba da Ba'asi a gaban Allah a Ranar Alkiyama.
Sannan Kuma ga wanda yana da
ikon cika Alkawarin da ya ɗauka Kuma ya ki Cikawa.
Lalle akwai dangin Azaba a gare shi a Ranar Alkiyama. Allah ya Kare Mu.
Sabida haka Jama'a ya kamata
Muna cika Alkawari. Shi Cika Alkawari wani Suffa ce ta Ubangiji. Wanda idan ya
yi alkawari akan wani Abu. Sai ya Cika Wannan Alkawarin Kamar yadda ya Riga Ya
Zartar. Kuma Muma Ya Umarce mu da cika wannan Alkawarin.
Allah ya yi Alkawarin Ba zai
Tashi Alkiyama ba, har sai lokacin da ya yi Alkawari ya cika. In ba dan haka
ba. Da lefuffukan da Ake yiwa Ubangiji, Da yanzu ya tashi wannan Duniyar Gabaki
Ɗayanta. Sai dai kuma alkawarinsa yana
nan. Ba zai Saɓa ba. Shiyasa ma Allah ya ke cewa. lalle
Allah ba ya saɓa alkawari.
Sabida haka Jama'a Muna Yin
Taka Tsan-tsan Akan duk Wani Alkawari da Muka ɗauka.
Idan ka cika Alkawari ka sauke Nauyin da ka ɗaukarwa
Kanka. Sannan ka Kyautatawa wanda ka yiwa wannan Alkawarin. Matukar dai ba wani
akasi aka Samu ba. Idan Kuma Mutum ya san ba zai Iya cika Alkawari Ba. To kar
ma ya ɗauka.
Gudun Kar Allah ya kama shi da Saɓa
alkawarin.
Daga Cikin Misalan Alkawari.
Akwai alkawari akan Aure, duk wanda aka yiwa Alkawari shi za a Baiwa. Bai
kamata a Saɓa Wannan Alkawarin Ba.
Akwai Alkawari Akan
kasuwanci. Duk wanda Ka Kulla Alkawari da shi a Kasuwarka, Wajibi ne ka Cika
Masa Wannan Alkawarin.
Akwai alkawari biyan Bashi.
Duk wanda ka yiwa Alkawari za ka Biya shi Bashinsa Lokaci kaza. Wajibi ne ka
Kawo masa a wannan Lokacin. Matukar dai ba Akasi Aka samu ba.
Akwai Alkawari Akan Aikin
Gwamnati Ko Company. Wajibi ne Mutum ya cika Aiki yana zuwa akan Lokaci. Yana
yin komi Daidai Gwargwadon Iyawarsa. da dai Sauransu.
Allah Shi ne Masani.
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa Da Tunatarwa a Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.