Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Wannan yana kama da ‘damfarar soyayya’ wanda aka tattauna a ƙarƙashin 3.3.9 a sama. Babban bambancinsu shi ne, a wannan nau’in damfarar, ‘yan damfaran suna mayar da hankali ne kan tattauna batutuwan batsa tare da tura bidiyoyi da hotunan batsa. Za su ja hankalin wanda suke shirin damfara ta yadda za a amince da su har a fara irin wannan alfasha a kan intanet.
Idan mace ake ƙoƙarin damfara, waɗanda suka tuntuɓe ta a matsayin za su bayyana mata a
matsayin kyakkyawan saurayi mai dukiya. Sannu a hankali zai riƙa tura
mata hotunan tsiraici, sannan ya buƙaci ita ma ta yi hakan. Idan namiji ne ake
shirin damfara, za a tuntuɓe shi
a matsayin mace kyakkyawa. Shi ma za ta riƙa tura masa hotuna
sannan ta buƙaci nasa hotunan. Sannan a hankali har a haɗa da bidiyoyi.
Tsiyar Nasara sai za shi gida! Za su adana dukkannin waɗannan hotuna da bidiyoyi da aka tura musu.
Su kuwa ta ɓangarensu,
da ma hotuna da bidiyoyin wata shashasha a uwa duniya za su tattaro su riƙa tura
wa mutum a hankali. Kwatsam za su buƙaci a tura musu maƙudan kuɗi ko kuma su saki hotuna da bidiyoyin a
duniya.
A watan Satumban shekarar 2024, sai da aka kama tare da kulle wasu ‘yan
Nijeriya guda biyu masu suna Samuel da Samson Ogoshi a kurkuku. An kulle su ne
a Amurka biyo bayan damfarar batsa a soyayya da suka yi wa wani ɗan Amurka. Matashin da suka damfara ya
shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi wanda har ya kai ga kashe kansa. Binciken ya nuna cewa sun yi
irin wannan damfarar a sama da mutane ɗari a duniya. Hakan yana nuni da yawaitar wannan
nau’in damfarar. Domin samun ƙarin bayani game da wannan labari, ana iya duba
Brenner (2024) da Luscombe (2024) da Tidy (2024).
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.