Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfarar Karbar Tallafi a Kan Intanet (Fake Charity Scam)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Akwai ƙungiyoyi masu yawa a duniya waɗanda suka shahara a ɓangaren karɓar tallafi daga hannun mutane domin tallafa wa al’ummomi da suke fama da matsaloli ko waɗanda wani iftila’i ya faɗa musu. Wasu fitattu daga cikin ire-iren waɗannan ƙungiyoyi da hukumomi su ne:

a. Abu Dhabi Fund for Development (ADFD) – (https://www.adfd.ae)

b. Islamic Development Bank (IsDB) – (https://www.isdb.org)

c. International Islamic Charity Organization (IICO) – (https://iico.org)

d. Qatar Charity – (https://www.qcharity.org)

e. King Abdullah bin Abdulaziz Program for Charity Works (KAAP) – (https://www.isdb.org/kaap)

f. King Faisal Foundation – (https://www.kff.com/en/)

g. Islamic Relief Worldwide – (https://www.islamic-relief.org)

h. Islamic Center Charity Society (ICCS) – (https://www.iccs.org.jo)

i. Muslims Around The World (MATW) Project – (https://matwproject.org)

j. Islamic Relief USA – (https://irusa.org/middle-east/)

Yayin da wani iftila’i ya faru a duniya, akan samu ‘yan damfara sun fito da ƙungiyoyin boge da sunan karɓar tallafi don kai wa mutanen da abin ya shafa. Za su karɓi tallafi daga hannun mutane ta wannan hanyar yaudara. Ba kowa ba ne ya damu da bibiya ko binciken ingancin ƙungiya ko hukuma kafin tura mata tallafi. Hakan ne kuma ya sa mutane suke tura kuɗaɗe zuwa asusun ‘yan damfara.

Wani lokaci kuwa, kafaffun ƙungiyoyi da suka shahara ne sukan gurɓace. A maimakon aikin tallafi kamar yadda suke nuna wa duniya cewa suna yi, sai su ɓuge da azurta kansu. Wasu daga cikin fitattun ƙungiyoyin tallafi da aka kama da irin wannan sun haɗa da:

a. Cancer Fund of America – (Ba a samu kafar intanet ɗinsu ba.) An wargaza wannan ƙungiya.

b. Kids Wish Network – (https://www.kidswishnetwork.org)

c. Help the Vets – (Ba a samu kafar intanet ɗinsu ba.) An dakatar da wannan ƙungiya a dalilin damfara.

d. The Breast Cancer Society – (Ba a samu kafar intanet ɗinsu ba.) An wargaza wannan ƙungiya.

e. Children's Cancer Fund of America – (Ba a samu kafar intanet ɗinsu ba.) An wargaza wannan ƙungiya.

Domin ƙarin bayani game da wannan nau'in damfara, ana iya duba SmartAsset (2020) da Consumer Reports. (2021) da Federal Trade Commission (2021) da New York Post. (2024).

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments