Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfarar Kudaden Intanet (Cryptocurrency Scams)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Kuɗin intanet ko kirifto (cryptocurrency) nau’in kuɗaɗe ne da kadarori da ake samu a duniyar intanet. Ana iya mallakar su ta hanyoyi da daban-daban kamar haƙa ko saye, da sauransu. Kasancewar harkar kuɗin intanet sabon al’amari kuma mai sammatsi, ‘yan damfara suna amfani da wannan dama domin damfarar mutane. Sukan yi amfani da rashin cikakken ilimi da mutane suke da shi game da kuɗin intanet domin damfarar su.

Nau’o’in damfarar kan intanet da suka shafi kuɗaɗen intanet sun haɗa da bin hanyoyin yaudara domin kwashe kuɗaɗen mutane. Haka kuma, sun haɗa da sanya mutane su yi wani aiki a kan intanet da tunanin za a ba su kuɗin intanet. Sai bayan sun kammala kuma a yi musu wala-wala.

A babi na biyar a wannan littafin an tattauna wannan nau’in damfarar.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments