Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Lallai Hausawa suna ci gaba da karɓar sauyin zamani ta fuskar neman kuɗi a duniyar intanet. Wani abin lura shi ne yadda har yanzu wasu suke ɗaukar ɗaukacin hanyoyin samun kuɗi a kan intanet a matsayin yaudara. Akwai dalilan da suka haifar da wannan fahimta a tsakanin al’ummar Hausawa. Ɗaya daga ciki shi ne rashin karɓar sauyi. Wannan yana faruwa a sakamakon ƙarancin ilimi dangane da sauye-sauyen zamani da kuma ita duniyar intanet kanta. Haka kuma, akwai tsarin halittar ɗan’adam wanda yawanci yakan fi son ya yi riƙo da tsohuwar hanyar da ya saba da ita a maimakon karɓar sauyi.
Dalili na biyu shi ne yadda harkokin
neman kuɗi a duniyar intanet suke cike da ƙalubale iri-iri. Ɗaya
daga cikinsu shi ne damfara. ‘Yan damfara a kan intanet suna amfani
da ƙarancin ilimin intanet da mutane suke
da shi domin damfarar su. Yawan damfara da ake samu yakan jefa shakku da wasuwasi a
zukatan mutane, musamman waɗanda suke da ƙarancin
bincike dangane da al’amuran. Daga nan ne kuma ake samun waɗanda
suke yin kuɗin goro cewa duk harkokin samun kuɗi a
kan intanet caca ne.
Zamani dai ya riga ya kawo intanet. Ƙasashen duniya sun karɓi
wannan sauyi. Duk wata al’umma da ta yi sake aka bar ta a baya game da neman kuɗi a
duniyar intanet, hakan zai kasance komabaya da naƙasu ga tattalin arzikinta. Bugu da ƙari, zai shafi al’adunta da adabinta da ma shi kansa
harshen. Dalili kuwa shi ne, duk al’ummar da aka bar ta a baya a wannan
fannin, to wasu mutane ne na daban za su wakilce ta a intanet. Su ne za su riƙa ɗora bayanai game da harshen da al’adun masu harshen a kan
intanet. Ƙari da ƙarau, su ne za su riƙa gudanar da ƙwadagon
kan intanet masu alaƙa da
harshen, kamar fassara da tafintanci da fassarar kan sikirin da sauransu.
Kamar yadda
aka kawo a cikin wannan babi na biyu, akwai damarmaki masu yawa na samun kuɗin a kan
intanet. Tuni wasu Hausawa suka shiga aka fara damawa da su. Wani abin da ya
kamata a mayar da hankali a kansa shi ne yadda ayyukan damfara da zamba suke ƙara yawaita a kan intanet. Dole ne mutane su yi ƙoƙarin samun ilimi game da hanyoyin kare kai daga damfarar intanet,
musamman idan suna gudanar da sana’o’i ko kasuwanci ko ƙwadago a kan
intanet. Babi na gaba zai mayar da hankali kan tattauna wasu nau’o’i da
hanyoyin damfara a kan intanet.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.