Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Intanet fage ne mai matuƙar jan hankali sakamakon tasirinsa a duniya. Masana da manzarta sun gudanar da rubuce-rubuce masu yawa dangane da tarihin samuwar intanet da bunƙasarsa cikin harsuna mabambanta. Daga cikin rubuce-rubucen da suka kawo tarihin intanet akwai Leiner et al. (1997) da Romualdo & Alessandro (2007) da Jonathan (2008) da Mukoshy (2015). Sake bibiyar tarihin tiryan-tiryan zai kasance tamkar maimaici ne ga ayyukan baya kawai ba tare da gabatar da wani sabon al’amari ko ilimi ba. Lura da haka, a nan za a fi mayar da hankali wajen zaƙulo sauye-sauye da cigaba da aka samu a harkar intanet tun bayan ƙirƙirarta.
Bincike da dama da suka gabata
sun danganta tarihin intanet da yunƙurin wata hukumar tsaro da take Amurka.
Binciken Gerf (2004 p.
1360)
ya bayyana cewa, a shekarun 1970s ne aka samu hoɓɓasa
na kafar intanet na farko mai suna ARPANET. Wannan bayani ya yi daidai
da wanda Mukoshy, (2015 p. 21) ya rawaito daga Deitel da Deitel, (2009).
Mukoshy ya yi ƙarin bayani da cewa, kafar intanet ta ARFA ta samu ne bayan
hukumar da aka fi sani da The Advanced Research Project Agency (ARPA) ta
gudanar da taro a shekarar 1969. Wannan hukumar ta kasance ƙarƙashin Department
of Defense in United States. A ƙasar Hausa kuwa, intanet ya fara shigowa
a wajejen 1990 kamar yadda Mukoshy (2016 p. 27) ya rawaito daga Almajir (2009).
Duk da haka, bai bunƙasa ba sai a wajejen 1998.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.