Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
An ƙirƙiri intanet ne a shekarar 1983. Wannan yana nuna cewa, intanet baƙon al’amari ne a duniya baki ɗaya. A bisa haka, “kalmar intanet baƙuwa ce a fannin nazarin Hausa” (Mukoshy, 2015 p. 19). Asalin kalmar a Ingilishi ita ce “internet.” An samu bambancin fahimtar kalmar da ta fi dacewa a yi amfani da ita a Hausa. Akwai waɗanda suke ganin ya fi dacewa a yi amfani da yanar gizo ko yanar gizo-gizo. Daga cikin masu amfani da wannan fahimtar akwai ’Yartsakuwa (2017) da Gana (2020) da CMG Hausa (2022).
A ɓangare guda kuwa, akwai masana
da manazarta da suke da fahimtar a Hausantar da ita zuwa “intanet.” A.H.
Amfani (keɓantacciyar
tattaunawa, wajajen 7 zuwa 28 ga watan Mayu 2019) yana da irin wannan fahimtar.
Ya jaddada cewa “Furta intanet ai ba ta gagari Bahaushe ba da har za a
tsaya ana kame-kame.”
Wannan littafin ya fi karkata a kan amfani da kalmar intanet a maimakon yanar gizo. An yi wannan zaɓin ne ta la’akari da dalilai kamar haka:
a. Ta fi riƙe
bakin Hausawa.
b. Ta fi hasko hoton
abin da ake nufi kai-tsaye domin kamancen sauti da take da shi da furucin
kalmar internet a Ingilishi.
c. Ta fi zagaya kafafen intanet da manhajojin fassara na ƙasa-da-ƙasa. Rubuce-rubucen da suka yi amfani da kalmar intanet sun haɗa da BBC Hausa (2010) da Umar (2012) da Rambo (2014) da Mukoshy (2016) da Muryar Hausa24 Online Media (2020).
Muhimmanci da tasirin intanet ga rayuwar ɗan’adam ya sa a kullum ake samun ƙaruwar rubuce-rubuce a wannan fanni (wanda ya shafi intaent) cikin harsuna daban-daban. A shekarun baya-bayan nan an samu ƙaruwar rubuce-rubuce a cikin Harshen Hausa game da intanet. Masana da manazarta da dama sun yi ƙoƙarin ba da ma’anar kalmar intanet. Umar ya ce:
Intanet kafa ce
wadda ta haɗa bayanai
daban-daban, kuma an sauƙaƙa hanyoyin amfani da waɗannan
bayanai yadda kowa zai iya miƙa hannayensa a kowane lokaci a ko’ina. (Umar, 2012 p. 48)
Wannan ma’ana ta yi ƙoƙarin
hasko yadda intanet yake ɗauke
da tarin bayanai da kuma yadda bayanan suke da sauƙin amfani. Wani ɗan raunin da yake cikin
wannan ma’ana shi ne, ba kowane lamarin intanet ba ne yake da sauƙi. A ɓangare guda kuwa, ma’anar
ta karkata kawai a kan bayanan da ake samu a duniyar intanet ba tare da mayar
da hankali kan salailai da sigoginsu ko hanyoyin samar da su da sarrafa su ba.
Mukoshy (2015) ya nazarci wasu daga cikin ma’anonin intanet da masana da
manazarta suka bayar.[1]
Daga ƙarshe
ya bayyana tasa ma’anar
da cewa:
Intanet kafar
sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk duniya. Tana ba da damar sadar
da bayanai kowaɗanne
iri, kuma zuwa ko’ina a duniya cikin ɗan
ƙanƙanin
lokaci. (Mukoshy, 2015 p.
20).
Da alama Mukoshy ya yi aron hannu
daga gun Umar, (2012) wajen fitar da wannan ma’ana ta intanet. Duka ma’anonin
biyu (Mukoshy da Umar) suna nuna cewa, kowa yana da damar yin amfani da
intanet, daga kowane wuri. Ma’anar da Mukoshy ya bayar ta zo da ƙarin
batun “na’urori” waɗanda
suka kasance gishiri cikin lamuran duniyar intanet.
Haƙiƙa waɗannan
ma’anoni sun ba da haske kan abin da ake nufi da intanet. Duk da haka, akwai
muhimmin al’amari da ya kamata bayani game da kalmar ya ƙunsa. Wannan kuwa shi ne
nuna bagire ko farfajiyar kafar sadarwar wadda ta kasance bisa hanyoyin iska waɗanda ba a iya ganin su. Tun
a shekarar 2010 Amfani ya kawo wannan cikin ma’anar da ya bayar inda yake cewa:
Intanet tsari ne
da ya haɗa duniya, ta
haɗakar layin iska na kwamfutoci
waɗanda ke amfani da
tsare-tsaren yanar gizo don biya wa biliyoyin masu amfani buƙatu a
faɗin duniya. (Amfani (2010) a cikin Umar (2012 p. 48)).
Yayin da aka nazarci waɗannan ma’anoni da ma
makamantansu, za a tarar da cewa akwai muhimman abubuwan da suka taru suka
samar da kafar intanet. Za a iya kallon su a matsayin siffofin intanet. Ko ma
wace ma’ana ce ta fi kwanciya a ran manazarci, yana da kyau a fahimci cewa:
- Intanet al’amari ne da ya samu a zamanance.
- Intanet ya kasance al’amari mai faɗi da ban mamaki. Yana ƙunshe da dukkanin wasu fannoni da ake samu a duniyar rayuwar yau-da-kullum.
- Intanet ba ya gudanuwa sai da taimakon na’urori masu ƙwaƙwalwa (nau’o’in kwamfuta daban-daban).[2]
- Hulɗayyar intanet aba ce wadda ba a gani, amma ana kallon sakamakonta ta fuskokin kwamfutoci. Akwai kuma sakamakon da yake bayyana a gan shi a zahiri ko a ji sautinsa ko ɗuminsa, da sauransu.
- Intanet yana da yaruka daban-daban. Yayin da aka tura saƙo bisa intanet, sai ya fassaru cikin yaren da intanet yake ganewa. Daga nan kuma sai ya sake fassaruwa zuwa yare ko sigar da masu neman sakamakon suke iya fahimta.
- Babu wani al’amari na intanet da ke da damar yin kansa. Komai aka gani a duniyar, to yin sa aka yi. Duk da haka, ana iya bai wa wani al’amari a duniyar intanet damar maimaita kansa ko sarrafa kansa zuwa wasu sigogi mabambanta.
- Intanet al’amari ne da ya jawo nesa kusa,[3] ya mayar da abu mai yawa ya zama kaɗan,[4] ya mayar da abu kaɗan ya zama mai yawa,[5] sannan ya tsuke faɗin duniya.
- Intanet haɗaka ce ta tsauraran al’amura daban-daban. Daga ciki akwai yarukan intanet da gine-ginensa da hanyoyin shigarsa da sabis ko netwok wanda shi yake ba da damar kaiwa gare shi.
Lura da waɗannan, ba da kammalalliyar ma’anar intanet da
za ta bayyana dukkanin siffofinsa aiki ne ja. Duk da haka, ta bin sawun zaren
tunanin magabata wajen ba da ma’anarta, za a iya cewa: Intanet fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar tsauraran al’amura da
suka haɗa da yaruka da
na’urori da sabis waɗanda
haɗuwarsu take samar
da al’amari ko bagire da yake tattare da hadahada da fannoni tamkar waɗanda suke duniyar
yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da
bankuna da kasuwanni da shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi
da waninsu.
[1]
Ma’anonin intanet da ya nazarta sun haɗa da waɗanda suka fito daga
ayyukan Almajir (2008) da Muhammad (2011) da kuma Umar (2012).
[2] Yana
da kyau a tuna cewa, kwamfuta tana zuwa cikin sigogi da dama. Wayoyin hannu da agogunan
dijital da talabijin ɗin dijital duk suna iya shiga cikin jerin nau’o’in kwamfutoci da ake da su.
[3]
Misali, wanda yake zaune a ƙasar Hausa zai iya yin
magana da wanda yake birnin Sin suna kuma kallon juna. Zai kuma iya taya shi
wani aiki da yake gudanarwa a kan intanet a wannan lokaci.
[4]
Misali, kafar intanet guda za ta iya ɗaukar dubban miliyoyin manyan
littattafai waɗanda idan da ɗakin karatu za a gina domin adana su, abin sai wanda ya gani.
[5] Idan
za a ba da wata sanarwa ta amfani da jarida ko wasiƙa, ana buƙatar buga takardu masu matuƙar yawa domin rarrabawa ko lilliƙawa a
wurare domin amfanin saƙonnin su kai ga jama’a. Ta
hanyar amfani da intanet, rubutu guda zai iya wadatarwa ba tare da an yi ta
maimaitawa ba.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.