Ticker

6/recent/ticker-posts

Lakubban Sunayen Yanka

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

A ƙasar Hausa, akan yi wa sunayen yanka laƙubba, irin waɗannan kuwa ba Hausawa kaɗai suke aiwatar da su ba. Misali:

Dodo: Laƙabi ne da yake nuna waibuwa tare da nuna wasu halaye da ɗabi’un da suka saɓa wa al’ada. Wannan sunan ya samo asali ne tun daga lokacin Annabi Muhammadu S. A. W. maƙiya ne suka saka masa sunan, saboda mu’ijizojinsa da ya nuna na annabta, sai suka ce, wannan dodanci ne da nuna sihiri. Tun daga nan ne sai aka rinƙa kiran mai suna Muhammadu da laƙabin Dodo, kamar yadda Gusau (1987 p. 35) ya nuna. Ba nan kaɗai ta tsaya ba, akan yi wa mai suna Muhammadu laƙabi da Tambari ko Zangina sai a taƙaita a ce: Zangi, wasu su ce Inuwa.

Jad. na 11: Laƙubban Sunayen Yanka a Sunayen Hausawa

 

Sunan Yanka

Laƙabi

1.       

Audu

Dumaa

2.       

Bello

a.      Ɗibgau

b.      Ɗimau

3.       

Faɗimatu

a.      Faji

b.      Zara

c.       Zara’u

d.     Zaratu

4.       

Balkisu

Gado

5.       

Abubakar

a.      Gagarau

b.      Gagara

c.       Garba[1]

d.     Sadauki

e.      Zaki

6.       

Ahmadu

a.      Guruza

b.      Gwadabe[2]

7.       

Aliyu

Zaki[3]

8.       

Hadijatu

Gadangama

Banzo

9.       

A’ishatu

Indo

10.   

Aminatu

Tako

Daguyau

Kura

Tushen Bayani: CNHN, (2006 p. 255)


[1]An yi masa laƙabi da Garba ne saboda an rufe shi a yamma da kabarin Annabi Muhammadu S. A. W. A Larabci akan ce ALGARBIYYU daga nan ne aka samo kalmar Garba.

[2]Ana yi wa mai suna Ahmadu laƙabi da Guruza, akan kuma kira shi da Gwadabe, musamman a Kano.

[3]Ana yi wa mai suna Aliyu laƙabi da Zaki, musamman a ƙasar Zamfara da wasu wurare.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments