Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunaye a Tsarin Addinin Musulunci

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

A daidaitacciyar hanyar shiriya ta addinin Musulunci, an umurci iyaye ko maga’isa (waliyya) da shugabannin iyali da su yi kaffa-kaffa (taka-tsantsan), wajen zaɓar wa ’ya’yansu kyawawan sunaye masu ma’ana da za su gamsar da kowane salihin masani. Ana buƙatar kowane Musulmi ya sanya wa abin da aka haifa masa sunaye kyawawa masu daraja da kuma albarka. Ana buƙatar sunayen su kasance ta hanyar bin koyarwar Annabi S. A. W. Misali, kamar sunayen Manzannin Allah da Annabawa da na Sahabbansu da na Shaihunan malamai da sauransu. Akwai hadisai da suka ƙarfafa haka. Daga cikin waɗanda aka ruwaito sun haɗa da:

Abu-Al-Darda’u ya ce: “Manzon Allah S. A. W. ya ce: “Ranar tashin alƙiyama za a kira ku da sunayenku da sunayen iyayenku, don haka ku zaɓi sunaye na gari” (Abu-Dawud ne ya ruwaito Hadisin).

Ba a ranar hisabi ba, ko a sararin wannan duniyar, akwai sunan da mutum zai ƙaƙaba wa kansa, amma ya ƙyamaci a kira shi da shi a wasu wuraren, ballantana a gaban Ubangiji, ga Manzanninsa da Annabawa da Auliya’u da sauran al’umma. Sakamakon haka, al’ummar Musulmi su guji yi wa kansu sunayen da suka saɓa wa dokokin addini.

Kyawawan Sunaye a Musulunci

Kasancewar addinin Musulunci ya ƙunshi rayuwar yau-da-kullum da ke tattare da hanyoyin ilmantarwa da faɗakarwa ga dukkan mabiyansa. Wannan ne ya wanzar da samuwar bayanai game da sunayen da suka dace a raɗa wa al’umma. A tsarin Musulunci, an bayyana mafi ƙayatarwar sunayen da suka kamata Musulmi su raɗa wa ‘ya’yansu su ne waɗanda aka danganta abin haihuwa da mahaliccinSa. Wato ta hanyar kiran mutum bawan Allah. Masali, Abdullahi, ko Abdulkarim da sauransu. Hadisi ya tabbatar da haka. Misali:

Ɗan Umar R. A. ya ce: “Manzon Allah S. A. W. ya ce: “Mafi soyuwar sunaye a wajen Allah su ne: “Abdullahi da Abdurrahman. ”Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin. (Muslim: 2132)

Sakamakon haka, iyaye Musulmi su guji sanya wa ’ya’yansu miyagun sunaye, domin suna yana rage martabar mai shi. Haka kuma yakan zama abin dariya da muzantawa ga mai karɓa sunan a tsakanin al’umma. A bisa wannan dalili ne Annabi S. A. W. yakan sauya munanan sunaye, kamar yadda hadisai suka nuna. A’isha, R. A. ta ruwaito cewa:

Annabi S. A. W. ya kasance yana sauya munanan sunaye. Tirmidhi da Sahihah ne suka suka rawaito wannan hadisin. (Tirmidhi:2839 da Sahihah:207).

Su sunayen banza da muggan sunaye sukan zamo abin gatse da kunyatawa a kowane muhalli da lokaci. Yayin da shara’ar Musulunci take ƙoƙarin kare mutunci da irlin al’ummar Musulmi.

An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar R. A. ya ruwaito cewa: “‘Yar Umar, an raɗa mata suna ASIYAH da ke ɗauke da ma’anar mai saɓo ko mai zunubi, sai Annabi S. A. W. ya sauya sunan, ya kira ta Jamila(Kyakkyawa). ”Muslim da Tirmizi ne suka ruwaito shi. (Muslim:2139 da Tirmizi:2828 da Ibn Majah)

Haka kuma Abu-Dawud ya ce: “Manzon Allah S. A. W. ya sauya sunayen AL-AZIZ da SHAYTAN, da UƘLAH, da AL-HAKAM, da GHURAB, da HABBAB. Haka kuma ya sanya SILM (Aminci /Lumana/Zaman Lafiya) ga wanda ake kira HARB (Yaƙi), AL-MUNBAITH ga wanda ake kira AL-MUDAJI, BANI AL-RISHDAH, ga zuriyar da ake kira BANI AL-ZINYAH. Haka ya sanya suna BANI RISHDAH da zuriyar da ake kira BANI-MUGHWIYAH. (Abu-Dawud: 4956)

Hani da Sanya Sunayen Mugun Fata

Addinin Musulunci, addini ne da yake ɗora mabiyansa bisa hanya madaidaiciya. Wannan ne ya sa Annabi S. A. W. yake tsawatar da al’ummarsa game da aikata duk abin da zai cutar da su a rayuwarsu ta duniya da lahira. Sakamakon haka ne yake jan kunnen al’ummarsa a kan sanya sunayen da ma’anoninsu suke ƙunshe da muguwar fata, don gudun kada irin waɗannan sunayen su yi tasiri ga ɗabi’un ‘ya’yansu. Akwai hadisai da suka yi nuni da haka, kamar yadda za a gani kamar haka:

An ruwaito Sa’id Ibn Almusayyibi ya ce: “Mahaifinsa ya bayyana abin da kakansa ya ce: “Na tafi wurin Annabi S. A. W., sai ya ce: “Mene ne sunanka? Na ce: “HAZNU” (maikaushi da tauri). Sai Annabi ya ce: “A kira ka SAHL (Sauƙi da rangwame). Shi kuma ya ce: “Ba zan sauya sunan da mahaifinsa ya raɗa mini ba. Ibn Almusayyib ya ce: “Har yanzu kaushi ya kasance a tare da mu. Buhari ne ya ruwaito hadisin (Buhari: 6190).

Haka kuma Yahaya bin Sa’id R. A. ya ce:

Umar ɗan Khattab R. A. ya tambayi wani mutum, ya ce: “Mane ne sunanka? Mutumin ya ce: “Jamrah” (kwalmaiƙuna). Umar ya ce: Me sunan mahaifinka? Mutumin ya ce: “Shihab” (ɗan harsashen wuta) Umar ya sake tambayarsa: Me sunan ƙabilarku? Ya ce: “Hurƙali” (Ƙone a Wuta). Umar ya sake tambayarsa: “Ina kuke zaune? Ya ce: A Harra-Tun-Nar (Yankin Wuta). Umar R. A. ya sake tambayarsa, ya ce: “A wane kware? Ya ce: “Dhat Laza (kwaren harshen Wuta). Sai Umar ya ce: “Yi hanzari ka ceci iyalanka, wuta ta ƙone su ƙurmus.

Wanda ya ruwaito labarin ya ce, dukkan gidansa da iyalansa sun ƙone ƙurmus sun zama hanburki (habɗi), kamar yadda Sayyidina Umar ya ambata, (Muwatta Imam Malik: 1871).

Wannan wata manuniya ce da ke faɗakar da al’ummar Musulmi game da yadda sunayen da sukan sanya wa ‘ya’yansu suke matuƙar shafuwar lamurran rayuwarsu ta yau-da-kullum a wannan zamani da muke ciki. Idan muka koma baya, ta tsinkayar sunayen da zuri’o’i daban-daban suke amfani da su a ƙarnonin da suka shuɗe. Bayan zuwan Musulunci ƙasar Hausa, har zuwa ƙarshen ƙarni na ishirin, ana maimaita sunayen magabatan wannan zuri’ar ne domin kada su ɓata. Hasali ma za a tarar sunayen Annabawa ne da Sahabbai da na matansu.

Akwai buƙatar Musulmi su kauce wa sanya wa ‘ya’yansu sunayen da suke bayyana alamomin siffofin Allah Mahalicci, kamar Ahad, Samad, Khaliƙ, Razzaƙ da sauransu. Abu- Dawud a cikin littafinsa SUNAN ya ce:

Yayin da Hani ya tafi Madina wurin Annabin Rahama S. A. W. tare da jama’arsa, ya kasance ana kiransa Abdul-Hakam, sai Manzon Allah S. A. W. ya kira shi ya ce masa: “Haƙiƙa, Allah shi ne HAKAM kuma yana hukunci, me ya sa ake kiran ka Abdul-Hakam? Sai ya ce: Mutane ne sukan zo wurina yayin da suka sami saɓani a tsakaninsu, kuma idan na zartar musu da hukunce sukan aminta da shi. A nan, sai Manzon Allah S. A. W. ya ce: “Wannan ya yi kyau. Kana da ‘ya’ya? Ya ce: E, ina da ‘ya’ya da suka haɗa da: Shurayh, Muslim, da Abdullahi. Annabi ya tambaye shi, wane ne babba a cikinsu? Sai ya ce: Shurayh. Manzon Allah ya ce: A kira ka: Abu-Shurayh.

Daga wannan hadisin za a fahimci cewa, ba za a yi wa mutum alkunya da sunayen miƙa-wuya ga Allah ba, kamar yadda aka yi wa mai hukuncin da Abdul-Hakam. Akwai rangwamen a yi masa wani suna na daban kamar da na babban ɗansa, tamkar yadda Annabi S. A. W. ya zartar. Hakan wata manuniya ce da take tabbatar da adalci a tsakanin zuriya. Domin sauran ‘ya’yansa da suka tarar a sararin duniya, wato an haife shi kafin haihuwarsu. Yin haka zai sanya musu son junansu tare da mutuntawa a tsakaninsu.

Hani da Sanya Sunayen Kyautata Zato

A tsarin addinin Musulunci, an hori Musulmi da kauce wa sanya wa ‘ya’yansu sunayen da suke ƙunshe da ma’anar kyakkyawan tsammani. An yi haka ne domin guje wa ɓacin rai, a sakamakon amfani da kalmar korewa (musu), wato ba ko babu kamar a sunaye irin su: Aflahb, Rabah, da, Yasar.

Hadisin Annabi S. A. W. ya tabbatar da haka a inda aka ruwaito cewa:

An karɓo daga Sumrah Ibn Jubdub, ya ce: “Manzon Allah S. A. W. ya ce musu: “Mafi soyuwar jumloli wurin Allah huɗu ne: “SubhanalLahi Walhamdulillah” Wala’ilahaillallahu” Wal-lahu Akbar”Kada ka kira ɗanka “Yasar”, Rabah ko Aflah”, domin idan aka ce:“Ina yake”? Yayin da ba ya nan, za a mayar da jawabin musu (korewa) wanda ya kasance ake sanin ma’anar sunansa”.

Daga wannan za a iya fahimtar cewa, ya wajaba ga duk wanda zai sanya wa ɗansa suna, idan ba daga cikin tsarin sunayen Annabawa ko Manzannin Allah ko sahabbansu ko wasu shaihunnan Malamai magabata ba ne, ya tabbatar ya san ma’anarsa. Domin gudun saɓa wa umarnin Annabi S. A. W.

Hani ga Sunayen Miƙa-Wuya ga Wanin Allah

A Musulunci an tsawaci Musulmi da su guji amfani da sunayen da ke nuni ga bayar da kai ga wanin Allah. Wato sunayen da suke nuni da zama bawan wani abu, wanda ba Allah ba ne, kamar yadda Larbawan jahiliyya suka yi. Misali, a sanya wa mutum suna kamar: Abdul-Uzza, Abdun-Nabi, Abdul-Hussaynu da makamantansu. Hasali ma malamai sun haɗu a kan haramcin sanya irin waɗannan sunayen.

Umurni da Sanya Sunayen Miƙa Wuya ga Allah

Akan samu wasu al’ummomi da sukan yi amfani da sunayen da suke ishara ga tausasawa ko masu kama da sunayen mata, da masu ishara ga sha’awar saduwar namiji da mace (jima’i), kamar: Huyam, da Nihad, da Sausan, da Mayyadah, da Nariman, da Ahlam da sauransu. Yayin da addinin Musulunci ya bayyana, sai aka tsawaci Musulmi da su kauce wa amfani da irin waɗannan sunayen, domin ‘ya’yansu su zamanto masu kyakkyawan hankali da ɗabi’u ɗauke da kwarjini. Wannan dalili ya sa Annabin Rahama S. A. W. ya umurci muminai (waɗanda suka ba da gaskiya kuma suke bin dokokin Musulunci kamar yadda suke), da su sanya wa ‘ya’yansu sunayen Annabawa da kuma wasu kamar Abdullahi, Abdur-Rahman da makamantansu. Irin waɗannan sunaye suna ƙunshe da: Abd-haɗe da ɗayan sunayen Allah kyawawa. Hasali ma hadisi ya tabbatar da hakan:

An karɓo daga Abu-Wahb Al-Jushamiy R. A. ya ce: “Manzon Allah S. A. W. ya ce: Ku sanya wa kanku sunayen Annabawa. Mafi kyakkyawan sunayen da Allah Ya fi so su ne: Abdullahi da Abdur-Raham. Mafi gaskiyar sunaye su ne: “Harith da “Hammam. Mafi munin sunaye su ne: “Harb” da “Murrah”(Abu-Dawud da An-Nasa’i suka ruwaito).

A wani hadisin kuwa da Ibn Umar ya ruwaito, an nuna cewa:

Annabi S. A. W. ya ce: “Mafi soyuwar sunayenku wajen Allah su ne Abdullahi da Abdur-Rahman, (Muslim: 2132).

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments