Daga
Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Matsayin Laƙabi a
Addinin Musulunci
Sanya laƙabi sunna ce a addinin Musulunci a yi wa yaro tamkar yadda shara’a ta shata. Laƙabi yana iya ɗaukar ABU wato “Baban” a haɗa shi da wani suna.
Sanya laƙabi ga ‘ya’ya yana haifar da fa’idoji masu amfani ga rayuwar al’umma, irin waɗannan
fa’idojin sun haɗa da:
i. Sanya tunani da ladabi da
mutumci a cikin zukatan al’umma.
ii. Bunƙasa kyawawan ɗabi’un zama da jama’a, har
yaro ya riya a zuciyarsu shi babba ne.
iii. Yana sa yaro ya tashi da son
al’umma tare da jin daɗi
ta hanyar kiransa da wannan kyakkyawan laƙabi.
A sakamakon irin waɗannan fa’idoji da ke
tattare da laƙubba ne, ya sa Annabi S. A. W. yake yi wa yara tare da
ambatonsu da su. Hadisi ya tabbatar da haka, a inda aka nuna cewa:
An karɓo daga Anas R. A., ya ce: “Manzon Allah S. A.
W. shi ne mafi kyawon ɗabi’u.
Ina da ɗan’uwa da ake
kira Abu-Umayr,, wanda nake tunanin sabon yaye ne. Duk lokacin da aka kai shi
gun Annabi S. A. W. Manzon Allah S. A. W. yakan ce masa: “Ya kai Abu-Umayr! Me
An-Nughayr (yautai) ya aikata?
Haƙƙin
Sanya Suna Da Laƙabi
A tsarin addinin Musulunci,
kowane al’amari an aza shi a bisa wani tsari na musamman, ba a bar abubuwa haka
kurum kara zube ba. Wannan ne ya sa Musulunci ya shimfiɗa ƙa’idar
zaɓar wa abin da aka
haifa sunan da za a raɗa
masa tare da laƙabin da za a iya yi masa.
A shara’ar Musulunci, uba ne aka
ba haƙƙin
sa wa ɗansa suna, ba
uwa ba. Kamar yadda nassin Alƙur’ani
Maitsarki ya zo da shi. A inda Allah Maɗaukakin
Sarki Yake cewa:
Ku kira su ga ubanninsu, shi ne
mafi adalci a wurin Allah, (Alƙur’ani,
33:5).
Haka kuma nassin hadisi ya
tabbatar mana da cewa, uba ne ke da alhakin zaɓar
wa ɗansa suna ba uwa
ba. Kamar yadda wannan hadisin ya zo da bayani. A inda aka bayyana cewa:
An ruwaito daga Anas R. A. cewa:
“Manzon Allah S. A. W. ya ce:An haifa mini ɗa
namiji yau da yamma, na sa masa sunan kakana Ibrahim”, (Muslim ne ya ruwaito
shi).
Duk da wannan damar da aka ba uba
na zaɓar wa abin da
aka haifa masa suna, bai halatta ga uban ko wani maga’isarsa ya sanya wa abin
da aka haifa mummunan suna ba. Irin waɗannan
munanan suna su ne kamar: AWAR (Mai’ido-ɗaya)
ko ARAJ (Gurgu) ko makamancin waɗannan
sunayen, tamkar yadda Allah Ya hana a inda Yake cewa:
… Kuma kada ku jefi juna da
miyagun sunaye na laƙabi. Tir da suna na fasicci a bayan Imani. . . (Alƙur’ani, 49:11).
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.