Ticker

6/recent/ticker-posts

Sunaye a Tsakanin Al’ummomi

Idan aka zurfafa bincike za a tarar da cewa, kusan kowace al’umma da take raye a farfajiyar wannan sararin duniya ba ta rasa sunayen gargajiya da take amfani da su, saboda matuƙar muhimmancinsu ga rayuwarsu. Ire-iren waɗannan sunaye an gaje su ne tun daga kakannin-kakanni. Irin waɗannan sunaye sun sha bamban daga wannan ƙabila zuwa waccan, kamar yadda al’adu da ɗabi’u da launin fata da abinci da yanayin sutura da harsuna da tsagen fuska da ita kanta kamannun fuskoki suka bambanta. Haka sunayen gargajiya suka sha bamban a tsakanin wannan al’umma zuwa waccan. Hasali ma za a tarar cewa, kowace al’umma tana da nata al’adu da ta shahara da su, haka lamarin ya kasance ta fuskar sunayen gargajiya.

A gargajiyance za a tarar cewa, duk sunan da aka kira wani da shi, idan aka bi diddigi sosai za a ga yana ƙunshe da wata ma’ana ta musamman da dalilin da ya sa aka sanya wa mutum ake kuma kiran sa da shi. Misali, a zamanin jahiliyya, Larabawa sukan sanya wa ‘ya’yansu munanan sunaye, kamar KALBU (kare) da DARAR (cuta) da ZI”IBU (kura). Yayin da sukan sa wa bayinsu kyawawan sunaye, kamar: MARZUƘ (abin arzutawa), kamar yadda Sufi, (1993 p. 97)ya kawo. Hadisai da dama sun kawo ire-iren waɗannan sunaye, kamar: ASIAHعاصية (Mai Zunubi) da AL-‘AASالعاص (Mai Fitina) da GHURAB غراب (Hankaka) da SHIHABشهاب (Harshen Wuta) da HARB حرب(Yaƙi), Muslim: 2139 da Tirmidhi: 2828, suka kawo shi.

Sun yi haka ne domin ‘ya’yan nasu su sami tasirin abubuwan nan da aka ba su sunayen su, ta yadda za su kasance masu aiki da halayya da ɗabi’u abin tsoro. Kamar yadda abubuwan da suka karɓi sunayen nasu suke a tsakanin al’umma, kuma a fagen fama (yaƙi) su zama gwarzaye. Yayin da bayinsu sukan zama masu sanyaya zukata da biyayya ga umarnin iyayen gidansu. Hadisai da dama sun nuna Annabi S. A. W. ya sami Larabawa suna amfani da irin waɗannan sunaye. Yayin ba wa abin da aka haifa suna, sukan yi la’akari da nau’in halittar da ba kasafai ɗan’adam yakan fuskance su ya wanye lafiya ba. Wannan ne ya sa suke ba ‘ya’yansu irin sunayen abubuwan domin su yi tasiri ga rayuwarsu, musamman ma idan aka yi la’akari da yanayin wancan zamani da suke tattare da yaƙe-yaƙe a tsakanin ƙabilun Larabawa. Zuwan addinin Musulunci bai hana Larawa sanya wa ‘ya’yansu irin waɗannan sunaye ba, kamar:

Jad. na 1: Waɗansu Sunayen Larabawa da Ma’anoninsu

 

Suna

Ma’ana

1.       

Asad

Zaki

2.       

Fahad

Dare

3.       

Ghazala

Barewa

4.       

Hamamatu

Tantabara

5.       

Hamman

Masai/Banɗaki

6.       

Khatam

Zobe

7.       

Laila

Dare

8.       

Mal’una

Tsinanniya

9.       

Ni’aal

Takalmi

10.   

Saddam

Mairushewa

A babukan da ke biye, za a mayar da hankali wajen kawo yadda lamarin sunaye ya kasance tsakanin waɗansu al’ummu makusanta ga Hausawa.

 Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments