Ticker

6/recent/ticker-posts

Asalin Suna (Tarihin Samuwar Sunaye)

Yayin da aka ce asali, ana nufin, mafari ko salsala ko tushen kalmar suna, wato lafazin da ake ambaton abu ko abubuwa da shi. Don haka kai-tsaye, za a iya cewa, suna shi ne fasahar farko da ɗandam ya fara mallaka, kuma ya yi amfani da ita wajen ishara (nuni) ko kira ga keɓantaccen abu ko abubuwa ko mutum. Allah Mahalicci da kanSa ya cusa sanin sunayen abubuwa ga halittarSa ta farko, wato Annabi Adamu (A. S.), a inda ya yi masa ilhami daban-daban. Alƙur’ani Maitsarki ya tabbatar da hakan, a inda Allah Yake cewa:

Kuma Na sanar da Adamu sunaye dukkansu” (2:31).

Abin nufi a nan shi ne, Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi wa Annabi Adamu (A. S.) ilhamin sunayen abubuwan gaba ɗayansu, kamar ƙwarya da masaki da ludayi da sauransu, kamar yadda Sheikh Nasiru Kabara ya nuna a tafsirin wannan ayar.

Hadisai da dama sun yi ƙarin bayani game da nau’o’in sunayen da aka sanar da Annabi Adamu (A. S). An ruwaito daga Ibn Abbas yana cewa:

Sunayen abubuwan da Allah Ya sanar da Annabi Adamu (A. S.) sun haɗa da: Sunayen ‘yan Adam da sauran gungun abubuwa, da suka ƙunshi dabbobi kamar giwaye, zakoki, raƙumma, jakuna da kuma nau’o’in ƙasa da sararin ƙasa da tsaunuka da sauransu. (Al-Ahmad, 1999 p. 13)

Shi kuwa Mujahed cewa ya yi: “Allah Ya sanar da Annabi Adamu sunayen komai, wanda Sa’ed bin Jubair da Ƙatadah da wasu suka yi muwafaƙa a kan haka.

Yayin da Al-Rabee ke da ra’ayin cewa, an sanar da Annabi Adamu sunayen dukkan Mala’iku ne.

Abdul-Rahaman Ibn Zaid cewa ya yi, an sanar da Annabi Adamu sunayen Zuriyarsa, kamar yadda Al-Ahmad, (1999 p. 13) ya nuna.

Bayan da aka sanar da Annabi Adamu (A. S.) sunayen abubuwan. Shi ke nan sai aka gitta su (abubuwan) ga Mala’iku, aka nemi su faɗi sunayensu, sai suka kasa. Yayin da suka gaza, sai Allah Ya umurci Annabi Adamu da ya faɗi sunayen abubuwan, kamar yadda ya zo cikin Alƙur’ani Mai tsarki, inda Allah Yake cewa:

Ya kai Adamu! Ba su labarin sunayensu. Sannan lokacin da ya ba su labarin sunayensu (2: 33).

Waɗannan ayoyin sun tabbatar mana asalin samuwar sunayen abubuwa daga Allah ne da kansa. An yi haka ne bayan halittar Annabi Adamu (A. S), sai Ya sanar da shi sunayen da za a riƙa ambaton abubuwa da su (kiransu), tare da bayyana masa ilmomi masu yawan gaske a cikin yardarSa.

Hadisi ya nuna cewa, bayan an halicci Annabi Adamu, an kori Iblisu daga gidan Aljanna, sai ya kasance yana zaune cikin kaɗaici, yana ragaita gaɗau-gaɗau a cikinta, sai ya kwanta barci. Da ya falka, ya ga mace tare da shi, da aka halicce ta daga sashen jikinsa yayin da yake barci. Adamu ya tambaye ta, ke wace ce? Ta karɓa masa da cewa: “Ita mace ce. Ya sake tambayar ta dalilin halittarta ta ce: “Saboda kai, don in samar maka natsuwa da hutawa! Da Mala’iku suka tambaye shi, suka ce: “Ya Adamu mene ne sunanta? Ya amsa musu da cewa: “Sunanta Hauwa’u”. Suka ce don me? Ya bayyana musu cewa: “Saboda an halicce ta ne daga abu mai rai, Al-Sadi ya ruwaito daga Abi Saleh da Abi Malik daga Ibn Abbas, kuma, Murrah ya ruwaito daga Ibn Mas’ud, kamar yadda Al-Ahmad (1999 p. 19) ya zo da bayanin.

Wannan ma wata hujjace da take ƙara tabbatar mana irin ilimin da Allah Ya hore masa. Sakamakon yana barci ne aka ciri sashen jikinsa aka halicce ta don ya sami abokiyar zama. Ibn Abbas ya ce: “An halicci Hauwa’u daga sashen awazar Annabi Adamu ta hagu a yayin da yake barci, sai aka cike gurbin da aka ɗibi awazar, da tsokar nama. (Muhammad bin Isyaka ya ruwaito, kamar yadda Al-Ahmad (1999 p. 19) ya zo da bayanin.

Yayin da aka saukar da Annabi Adamu (A. S.) da matarsa a doron ƙasa, sun cigaba da ambaton abubuwan da aka halitta domin amfaninsu. Lokacin da suka hayayyafa, sun sanya wa ‘ya’yan da suka haifa sunayen da Allah Ya sanar da su cikin ikonSa. Misali: Ƙabila, da Habila da Shisu da sauransu. Duk waɗannan sunayen da ya raɗa wa ‘ya’yansa suna daga cikin ilimin da Allah Ya sanar da shi.

Akwai hujjoji da yawa da za a iya samu daga cikin Alƙur’ani Maitsarki da ke ƙara tabbatar mana da asalin samuwar sunaye daga Allah Maɗaukakin Sarki ne. Misali, lokacin da matar Imrana, mai suna Hannatu ɗiyar Faƙuz, ta kasance bakarariya (wadda ba ta haihuwa), sai wata rana ta ga tsuntsuwa tana ciyar da ɗanta, sai ita ma ta yi nuni ga buƙatar samun ɗa nata na kanta. Ta roƙi Allah Ya ba ta ɗa; tare da mijinta Imrana. Yayin da Imrana ya sadu da ita, sai ta sami juna-biyu. Bayyanar cikin ke da wuya, sai ta ɗauki alwashin idan ta haifi ɗa namiji za ta sanya shi ga hidimar Baitul-Muƙaddisi. Alƙur’ani ya tabbatar da haka, a inda Allah Yake cewa:

A lokacin da matar Imrana ta ce: “Ya Ubangijina! Lalle ni, na ɗauki alƙawali na bin da yake cikin cikina, gare ka ya zama ‘yantacce, to ka karɓa daga gare ni. Haƙiƙa kai mai ji ne masani. ” (3:35).

Yayin da ta haihu, sai ta ga ‘ya mace ta haifa ba ɗa namiji ba, wanda ta fi buƙata a ranta, domin shi ne zai fi dacewa da hidimar Baitul-Muƙaddisi. To, amma tun da ta yi alƙawali, kuma ta fito daga babban gida ba damar ta warware, sai ta sanya wa ɗiyar suna MARYAMU. Kalmar “Maryamutana ɗauke da ma’anar: “Mai Ibada”. Allah kuwa Ya karɓa mata roƙonta, sai ta kasance mai ibadar. Alƙur’ani Maitsarki ya tabbatar da haka, a inda Allah Yake cewa:

To a lokacin da ta haife ta, sai ta ce: Ya Ubangijina! Lalle ne ni na haife ta, mace! Kuma Allah ne mafi sanin abin da ta haifa. Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma ni na yi mata suna Maryamu, kuma lalle ne ni ina nema mata tsari gare ka, ita da zuriyarta daga shaiɗan jefaffe (3:36).

Idan aka dubi wannan ayar da idon basira, za a tarar cewa, Hannatu ce da kanta ta sanya wa ɗiyar da ta haifa suna Maryamu, da ke ɗauke da ma’anar Mai Ibada. Zai yiwu Allah ne cikin ikonSa ya yi mata ilhamin sunan, kuma ta sanya mata shi. Hasali ma sai sunan ya kasance tamkar addu’a, shi ne dalilin da ya sa Maryamu ta zama ma’abuciyar ibada a Masallacin Baitul-Muƙaddisu. Abin la’akari a nan shi ne, suna yana tasiri ga wanda aka ba shi. Idan aka sa wa abin haihuwa sunan kirki, sai ya yi naso ga halaye da ɗabi’un wanda aka ba shi. Haka abin yakan kasance ga wanda aka ba mummunan suna. Wanda aka sa wa sunan dabba, zai kasance mai halaye da ɗabi’u irin nata.

Yayin da Maryamu ta girma, ta kai munzilin ta aiwatar da ibada tare da hidimar Baitul-Muƙaddisu, sai mahaifiyarta ta tura ta can, kamar yadda ta ɗauki alƙawali. Mutane suka yo ca, kowa yana son ya ɗauki takalihun kula da Maryamu. Ganin irin yadda ake rige-rige wajen ɗaukar nauyin kula da ita, sai aka tsayar da shawarar aiwatar da yin ƙuri’a. An yi haka ne domin samun wanda ya fi dacewa a lokacin da ta tare a Baitul-Muƙaddisu, don gudanar da ibada tare da hidimar Masallacin. Yin ƙuri’ar ke da wuya, sai ƙuri’ar ta faɗa ga Annabi Zakariya’u (A. S.) wanda shi ne limamin Masallacin. An aiwatar da ƙuri’ar ne a lokacin da ba ya nan. Alƙur’ani ya tabbatar da haka, a inda Allah Yake cewa:

Kuma ba ka zamanto a wurinsu ba lokacin da suke jefa ƙuri’unsu, game da wane zai yi renon Maryamu. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba lokacin da suke jayayyar renon ta (3:44).

A ƙarshe dai sai Annabi Zakariya’u ya ɗauki nauyin renon Maryamu. Ita sai ta riƙa zama a Masallacin. Kowane lokaci tana kula da tsabtar Baitul-Maƙaddisu, tana bauta wa Allah. Ana cikin haka, sai wata rana aka yi ƙamfar abinci, amma duk lokacin da Annabi Zakariya’u ya tafi wurinta sai ya tarar da nau’o’in abinci a inda take ibada. Ya yi mamakin haka, ya tambaye ta daga ina take samun wannan abinci? Ta shaida masa daga Allah ne. Domin yana arzutta wanda Ya so, ba da wata wahala ba. Alƙur’ani ya tabbatar da haka a inda Allah Yake cewa:

“…Ko da yaushe Zakariya’u ya shiga wurinta a Masallaci sai ya sami arziki (abinci) wurinta, sai ya ce: “Ya Maryamu daga ina wannan ya miki?” (sai) ta ce: “Daga wurin Allah yake”. Haƙiƙa Allah Yana arzutta wanda Ya so ba da wani bincike ba” (3:37).

Wannan ya sa Annabi Zakariya’u ya tabbatar Allah Ya karɓi aikinta, abin ya ba shi sha’awa, sai ya gurace shi ma ya samu ɗa nagari kamar Maryamu. Nan take sai ya duƙufa yana roƙon Allah Ya ba shi ɗa nagari. Allah kuwa Ya karɓi addu’arsa, ya yi masa bushara da samun ɗa mai suna Yahaya. Alƙur’ani ya tabbatar da haka a inda Allah Yake cewa:

Sai Mala’ika ya yi kiransa a lokacin shi yana a Masallaci. Ya ce: “Haƙiƙa Allah Yana yi maka albishir da Yahaya” Mai gaskatawar kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakakke, kuma Annabi daga salihai”(3:39).

Daga wannan ayar za a tabbatar da cewa, Allah ne da kanSa Ya sanya wa ɗan da Annabi Zakariya’u zai haifa suna Yahaya tun kafin a sami shigar cikinsa. Hujja a nan ita ce, an bayyana masa sunan abin da zai haifa tun kafin a haifi abin, tamkar yadda ayar da ta gabata ta tabbatar.

Wata hujjarmu ta cewa, dukkanin sunaye sun samo asali ne daga Mahaliccin sammai da ƙassai ita ce, Allah Maigirma da Ɗaukaka Ya aika Mala’ika Jibrilu wurin Maryamu, domin ya yi mata busharar ɗan da za ta samu, aka kuma faɗa mata sunansa. Alƙur’ani ya tabbatar da haka, a inda Allah ke cewa:

Lokacin da Mala’ika ya ce: “Ya Maryamu, haƙiƙa Allah yana yi miki albishir da kalma daga gare shi, sunansa Almasihu Isa ɗan Maryamu, maidaraja a duniya da lahira, kuma yana daga cikin makusanta. (3 p. 45).

A nan za a ga bayan an faɗi sunan abin da za a haifa da jinsinsa, wato namiji. Allah kuma Ya yi masa laƙabi da Almasihu, saboda idan ya shafi maras lafiya sai ya warke. Wannan ya nuna cewa, yi wa mutum laƙabi da wani aiki da yake gudanarwa, muddun aikin ba haramun ba ne, to bai da laifi.

Wata hujjar kuma ita ce, inda Allah Ya aiki Mala’ika domin ya yi wa Annabi Ibrahima tare da matarsa Saratu busharar haihuwar Annabi Is’ma’ilu. Alƙur’ani ya tabbatar da haka a inda Allah Yake cewa:

Sai muka yi mata bushara (da haihuwar) Ishaƙa da Yakubu (11: 71).

A wannan ayar har ma Ubangiji Ya bayyana musu sunan ɗan da za su haifa, (wato, jikan da zai haifa musu). Duk waɗannan hujjoji ne da suke ƙara tabbatar mana da cewa asalin sunaye daga Allah ne, Shi ke ba da su ga bayinsa.

Yayin da aka duba a cikin Alƙur’ani, za a ga wuraren da Allah S. W. A. Ya kira Annabi Muhammadu S. A. W. da sunaye (laƙubba) masu yawa a cikin mabambantan surori kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya:

 

1. An kira shi da laƙabin MUNDHIR (منذر) a Suratul Ra’ad, a inda Allah Yake cewa: …إنما أنت منذر. . . (… Abin sani kawai, kai mai gargaɗi ne… (13:7)

2. A wata ayar da take cikin Suratul-Taubah, Allah Ya yi masa laƙabi da HARIS (حريص) Ya kuma kira shi da suna RA’UF ((رؤف da RAHIM (رحيم) (9:128).

3. A cikin Suratul Hijr da Suratul Hajji kuwa, an kira Annabi S. A. W. da suna NADHIR(نذر) (15:89) da (33:45).

4. A cikin Suratul Namli, an yi masa laƙabi da HADI (هادى) (27:81).

5. Yayin da a Suratul Ahzab kuma, Ubangiji Maɗaukakin Sarki Ya kira shi da laƙabin ALKHATAM (الخاتم) (33:40), a wata ayar kuma aka yi masa laƙabi da SHAHID (شاهد) da MUBASSHIR (مبشر) aka kuma kira shi da NADHIR(نذر).

6. An kuma yi masa laƙabi da ADDA’I (الدعى) da SIRAJUN (سراجا) da MUNIRAN (منيرا) (33:46).

7. A Suratul Muddathir, Allah Ya kira shi da laƙabin MUDDATHIR (مدثر) (74:1).

8. A Suratul Muzzammil, an kira shi da MUZAMMILU (مزمل) (73:1).

9. A Suratul Tak’wiri kuwa sai aka kira shi da laƙabin AMINا(امن) (81:21).

10. A Suratul Ghashiyah, Allah Ya kira Annabi S. A. W. da laƙabin MUDHAKKIR (مذكر) (88:21).

Wata hujjar da take ƙara tabbatar mana asalin sunayen an samo su ne daga Allah Ubangijin talikai ita ce, a inda Allah Ya sanar da Annabi Isa (A. S.) sunan Annabin da zai biyo (zo) bayansa, mai suna AHMAD (أحمد). Alƙur’ani ya tabbatar da haka a inda Allah Yake cewa:

Kuma a lokacin da Isa ɗan Maryamu ya ce: “Ya ku Bani Isra’ila lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni, na Attaura, kuma mai bayar da bushara da wani manzo da ke zuwa a bayana, sunansa Ahmad” (61:6).

A nan za a fahimci, tabbas Allah bai taƙaita a kan faɗar sunan Annabin da zai zo bayan Annabi Isa (A. S.) ba. Yakan bayyana irin yadda za a yi ta faɗar kalmomi daɗaɗa ga Annabi (S. A. W.), waɗanda Allah Ya fayyace su a cikin Alƙur’ani, kamar yadda aka gani da farko. Hasali ma za a ci gaba da ambatonsa da waɗannan kalmomin har zuwa ranar tashin Alƙiyama. Wannan ne ya sa ake fassara Kalmar Ahmad da ma’anar Mashayabo.

Daga waɗannan laƙubban ne da Allah Ya yi wa zaɓaɓɓen halittarsa, shugaba kuma cikamakin Annabawa (S. A. W.), al’ummomin da suka karɓi addinin Musulunci, ciki kuwa har da Hausawa, suka rinƙa sa wa ‘ya’yansu maza da aka haifa musu, wasu daga cikin laƙubban. Akan haɗa su da Muhammad a raɗa wa abin da aka haifa, don fatan Allah Ya albarkaci abin haihuwar albarkar mai sunan na asali. Misali, Muhammadu Nazir da dai sauransu, kamar yadda za a gani nan gaba, insha Allah.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments