Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
1. Allah mai mutane, Jaɓa ta ga bakin mijinta
2. Ana tsoronmu ni da iya, in ji ɗiyar mayya
3. Allah sutturi buƙwi in ji kishiyar mai doro
4. Abin da kamar wuya, gurguwa da aure nesa
5. A so uwa a so ɗanta,
don kowa da ranarsa
6. Amfanin abin ado ɗaurawa
7. Arha, aure bashi
8. Allah na dawo, in ji matar ɗan
ci rani
9. Akwai abu ƙasan danga boboniya da cikin ɗansarki
10. Agola mai wuyar ban nama, sai dai a ba shi ƙashi
11. A taɓa
ni a ji ni, mummuna ta je gidan biki
12. Abin nema ya samu, matar falke ta haifi alfadari
13. Angulu in ta biya muradi, Zabuwa ta tafi da zanenta
14. An yi ba a yi ba, mace ta haifi mace
15. Ango mijin Amarya, kada ka sha mai ya ruɗe ka
16. A sauƙaƙe, azumin gwauro, kada dai a yi lullubin
uwar daɗi
17. Asiri rufe, an kama uwar amarya da ango
18. Abin dibi, dibin matar mutane
19. Abin nema ya samu, an bai wa ‘yar kauye toshin gatari,
da ma baba yana nema
20. Agola mai wuyar ban nama, kaɗan an ba shi tsoka, sai ya cinye da sauri sai
ya ce ba a ba shi ba.
21. Abin daga Allah ne, tsohuwa ta samu autan ‘ya’ya
22. Amarya in ba ta hau doki ba, ba ta ɗaukar kaya
23. Aure yaƙi ‘yan
mata
24. Aure tagomashin babba da yaro
25. A lallaɓa
auren zamani
26. A haifi ɗa
da arziki ya fi a (mutu) a bar masa gado
27. A ƙi maraya da rigar buzu, a gan shi da ta ƙarfe
28. A hana ka mata a gan ka da goyo
29. A ci, a haihu, an kai wa baba tuwon suna
30. Asiri da mamaki, matar albarka
31. Abin tsana, amarya a bayan kare
32. Abin daga Allah yake, mai takaba ta yi ciki
33. Aure maganin talauci
34. Abin nema ya samu, an jefi ‘yar manomi da fartanya
35. Abin na yi ne, an biya wa bazawara hajji
36. Abin al’ajabi, ango ya kwana da kunzugu
37. Aure babu haihuwa wahala ne
38. An ƙi maraya da rigar buzu, wata rana za a gan shi da rigar saƙi
39. Arziki mutai biki, ta ce can na kwan
40. A ranni mu je biki, mijina ba ya faɗa
41. Abin mamaki bazawara da sai da maganin mallakar miji
42. Allah ya yi aure da mara kwabo
43. A rashin sani ya sa karen gwauro ya kori bazawararsa
44. Aure ya tashe, wai an doke bora da kaya
45. Allah ya yi abin, inji mafaɗin aurensa
46. A rashin uwa akan yi uwar ɗaki
47. Aure baya, shi ne sadakin na gaba
48. A ja mu a dosa, an kai uwar makaho kashi
49. Allah maganin ‘yar sadaka, ‘yar mai kuɗi, ubanta ɓarawo
50. Abin daga Allah ne, matar takaba ta yi ciki
51. Abin kunya, uwar ‘ya ta cinye suruki ranar aure
52. Allah ya kai yaro matsayin babba
B:
1. Bari mu taɓa
mu ji, mayya ta je barkar haihuwa
2. Biyayya bayan rai inji wanda babarsa ta mutu
3. Ba Kukana ba, uwar kishiya ta mutu
4. Ba ci ba sha, auren matsiyaci
5. Ba kaina farau ba, mace ta yi cikin shege
6. Ba laifi! An yi wa yan biki duka
7. Ba rabo ba, ɗan
wabi ya faɗa wuta
8. Barewa ba ta gudu, ɗanta
ya yi rarrafe
9. Bar taƙama da samun dangi, nemi naka
10. Ban zata ba, malama da cikin shege
11. Ba ki yi gashin wance ba, ba ki yin kitson wance
12. Ba laifi, ɗa
a bayan uwatai
13. Bikin ‘yar kujina
14. Bikin magaji, ba ya hana na magajiya
15. Basaja fitsarin maijego, in ta yi ta ce ɗan ne ya yi
16. Bawa ba ya gasa da ‘ya’ya
17. Ba ni na fara ba, mace da cikin shege
18. Ba a ɗaukar
jika don tuwon maƙwabta
19. Ba aure ke da wuya ba, biɗar
kuɗi
20. Babban abu mace ta riga mijinta fitsari
21. Ba na jikoki, sai dai na ‘ya’ya
22. Ba kullum take ɗaya
ba, inji matar ɓarawo
23. Ba haka aka so ba, ƙanen miji ya fi miji kyawo
24. Ba laifi ango ya kwana da durwa (ɗanbante)
25. Bawan magaji mai kamar ɗa
26. Ba ji ba gani, auren kurma da makaho
27. Barantaka ba bauta ba
28. Bakin gado – faharin maigida
29. Baiko ba aure ba, yaro in kana da hali sake wata
30. Ba a rabu da bukar ba, an haifi abu
31. Babbar mace wadda ba a sai mata gishiri
32. Banzar banza, aure babu soyayyar zuci
33. Ba ni tsoron amarya da ango balle ‘yan zaman ɗaki
34. Bakinka naka, ‘yan matan birni
35. Ban gane ba, an daki ɗan
kishiya
36. Ba don ka tafi ba, zan yi begenka
37. Bazawara uwar son banza
38. Ba ni kafawa ɗan
kishiya gado ya hau
39. Ban so haka ba, ɗa
shi fi uba daɗin kwana
40. Baran mace ya sha ruwa, miji bai sha ba
41. Baran mace wawa bai san za ta ƙi shi ba
42. Baran mace wawa bai san abin da za shi ya zo ba
43. Boɗoɗuwa mata a kan miji
44. Babbar mace sai kin ga dama ake miki cefane
45. Ba wayau ango da amarya bisa gado
46. Ballagaza matar banza
47. Budurwa da safe maɗacci
da marece zuma
48. Bora shingen mowa
49. Ba ki jimu ba, ɗa
da ya harbi ubansa
50. Bunsurun barkono, mai hana mata yaji
51. Babban wa uba
52. Bawa ba ya wasa da ɗa
53. Bureɗe
an sa wa bazawara rana
54. Bari mu taɓa
mu ji, mayya ta je karɓar
haihuwa
55. Ɓarti sana’a
ci da kai, uwa na yi yaro na ɓatawa
56. Barewa ba ta gudu ɗanta
ya yi rarrafe
57. Ba neman aure ke da wuya ba, shiga ka fito
58. Ba zafi barkonon taro a idon kishiya
59. Ba ni da ta cewa, mai gida ya yi tsegumi
60. Ba kullum guɗa
ba, inji matar ɓarawo
61. Ba sabon ba, ɓera
ya je zance
62. Ban sa a ka ba kare da guɗar
gara
63. Baƙin karen masoyinka ya fi farin ragon maƙiyinka
C:
64. Ciwon mace na ‘ya mace ne
65. Ci bakinka naka, inji ‘yan matan garko
66. Cinnaka tsakar gida, hana mata takangani
67. Cas Surhen dawar lami
68. Cab!, Aan ce da budurwa ta auri tsoho.
D:
1. Daga wajen wa; aure da duka
2. Dole/Tilas a bai wa ɗan
mata hura
3. Da zaman banza, gara aikin kishiya
4. Da zaman banza gara aikin uwar kishiya
5. Da wasu mazan, gara indomi da miyar kuka
6. Da auren karuwa, gwamma kiyon zakara
7. Duniya mace da ciki ne, ba a san abin da za ta haifa ba
8. Duniya rawar ‘yan mata na gaba ya koma baya
9. Dole a ba ɗan
mata fura
10. Daɗi
bisa daɗi amarya bisa
ango
11. Dalili tsegumin babban gida
12. Daka, niƙa, mafarkin gwauro
13. Dakan ɗaka
shiƙar
ɗaka, tankaɗen bakin gado
14. Da yadda aka yi, maigida gode wa kwarto
15. Dalili mai sa kama gindin sarakuwa
16. Dara ta ci gida, matar kwarto da cikin shege
17. Dole a zo, ɗaki
ya faɗa da gurguwa har
da ɗan masu gida
18. Duhun dare mai hana yaro kwaraka
19. Duniya miya, damun mace da hannu
20. Dauɗar
mata ta mace ce
21. Dokin madokala, ɗa
daga ciki rokon uba wuri
22. Don ka ga buduwar bana da kyau, ta baɗi ta fi ta kyau
23. Da haihuwar raggo, gara zubar ciki nasa
24. Da haihuwar yuyuyu gara guda ɗaya ƙwaƙƙwara
25. Darajar ɗa
namiji sai da mata
26. Darajar ‘ya mace ko gidan mijinta
27. Darajar mace miji
28. Da motsi, farautar mata
29. Da ma lissafi, budurwa da cikin ubanta
30. Dukiyarka wuri ta fi ta uba, ta fi ta uwa zambar dubu
31. Ɗan da zai mutu, laya ba ta yi masa
32. Ɗan tsamiya ba shi zama ɗan
kuka
33. Ɗan kuka mai ja wa uwatai jifa
34. Ɗan’uwa
rigar ƙaya
ne, in ka sa ya soke ka, ba ka da damar ka ɗebe
shi ka yar
35. Ɗan’uwa
rabin jiki ne
36. Ɗa da mahaifi ba a raba su
37. Ɗan mai gona ya fi ɗan
mai gayya
38. Ɗan asali ya fi shigagge
39. Ɗan dangi tuwonsa ba shi yin ruwa
40. Ɗan banza shi ke haihuwar ɗan
banza
41. Ɗan kwaraka ba shi kyautar mara
42. Ɗa farin gilashi ne
43. Ɗa ba bawa ba ne.
44. Ɗanka ɗirka,
mace maiciki da kaya a kai
45. Ɗawainiya ɗaukar
ɗan wani
46. Ɗan mai rowa nauyi
47. Ɗa wanda ya yi daɗin
kai, wanda ya yi kama da uba ne
48. Ɗa shina ga mace
49. Ɗan sarki yi abin da ka so, ubanka na gado
50. Ɗawainiya zuwa makka da ciki
51. Ɗa mai muni uwata ba ta ƙi ni ba
52. Ɗauki kurma ta ga miji
53. Ɗa ɗaya
mai wuyar yardawa
54. Ɗa ɗa
ne, shege ko sai mai shi
55. Ɗan mugu, mugu ne
56. Ɗa duka na kowa ne, wanda ya haife shi ba shi kaɗai ke da shi ba
57. Ɗa mai zuciya kamar ta
kashe shi
58. Ɗungurungun haihuwa da hanji
59. Ɗaya matar yaro, in ka ga ta biyu shi ya yi abu tai
60. Da wannan don wannan, an sa wawa biko
61. Da alheri kishiya ta hau kura
62. Da sani, karuwa ta taka matar aure
63. Ɗa abun ne, matar maigishiri ta zuba a kunu
64. Ɗan tsakon da Allah ke so, ko ba uwarsa ya girma
65. Ɗan ba-ƙara, gurguwa da aure nesa
66. Dole a ce da mijin iya baba, ko da kare ne
67. Dutse, maganar saurayi
F:
68. Fira sabuwa, amarya ta sake miji
69. Futun biki ‘yar matsiyaci ta mutu ranar biki
70. Farar mata, abar shiga tsara
71. Faɗan
gwaggo a ƙofa
G:
72. Gado ba na uwa ba, ba na uba ba, in ka sami allura ka
gode.
73. Gishirinki jikin ki
74. Gara kowa da ni, inji matar bebe
75. Garban toka, abin baga iyali
76. Garban toka, gama gida
77. Ganin waɗayi,
sallar gidan biki
78. Gaikau maganin uwar tagwai
79. Garin masoya ba ya da nisa
80. Gwauro ya sha
fura, balle mai mata
81. Gaza haƙuri shi ya kawo budurwa da cikin shege
82. Gandan, kai ba dawa ba, amma kana taya maza riƙon
gida
83. Gode Allah wanda ya fi gode uwar mata, ko taka ta fita
Allah zai baka wata ka aura.
84. Girma ga ɗan
farin gado ne
85. Gwargodon kadaran aure darajar mace
86. Gwatsine aikin mata
87. Ga mu ga Allah mai takaba ta taka gawa.
88. Gindin banza! Matar gardi ta haifi allo
H:
89. Haihuwa maganin annoba
90. Haihuwa maganin mutuwa
91. Haiyaratata, dariyar mai mata tara
92. Haihuwa maganin wulaƙancin duniya
93. Haɓaka,
namiji da niƙa
94. Hamburki ango ba ƙoshi
95. Haihuwar tsakar dare munafukai na bacci
96. Haihuwa ɗaya
huron gutso
97. Haihuwa mai rana
98. Haka tara inji kishiyar mai mageɗuwa
99. Haihuwa mai rana
100. Haɗa
kai ya fi haɗa gida
101. Hayya – rattata” inji mai ‘ya’ya tara.
I:
102. In kana raka mace gidansu, wata ran ka raka ta gidan
kwarto
103. In mutum bai yi kuwa ba, uwarsa ba ta mutu ba
104. In Allah ya hana maraya rigar saƙi ai sai ya bashi rigar ƙarfe
105. Ina ruwan shege da alheri
106. Ina ruwan maza da wankan jego
107. Idan maye ya mance, uwar ɗa
ba ta mance ba
108. Ina mata ga miji, inji shekararren gwauro
109. In ana dara fidda uwa akai
110. Ina ruwan maza da wankan biƙi
111. Ina tsoron kai na da gari, inji matar mai kureci
112. Ina ruwan gwari da miji, ta ce baba ya isa
113. In an ƙi bare, a biɗi ɗan’uwa
114. Ina ruwan ci buki, ta ce can na kwana
115. In mutum ba ya kuka, uwarsa ba ta mutu ba
116. Ilin amarya ta ci ƙanen miji
117. In ka ga tsohuwa da kuɗi,
aure ta domin ba za ta bar ka da yunwa ba.
118. Ina ruwan maijego da guru da tsakiya
119. In mutum ya ƙi ka da mata wata rana sai shi ganka da
jika
120. Ikon Allah! Mai gari gwauro, talaka da mata huɗu har da ƙwarƙwara
121. In ka ga babbar kaza kasuwa, in ba gurdumun, to da shan
kwai
122. Idan so cuta ne, haƙuri magani ne
123. Ina zan sa kaina, mummuna ya ga mata
124. In ka ga mace ta zanna wuri ɗaya ba ta da sutura ne
125. In kaga kaza tana taka ‘ya’yanta, ba don ta ƙi su
ba ne
126. In ka ga goɗiya
da sirdi wani ta kayar
127. In aure bai kawo shi ba, saki ya kawo shi
128. Icce tun yana ɗanye
ake lanƙwasa
shi
129. Ina sane, karuwa ta taka matare aure
J:
130. Jiya ba yau ba, tsohuwa ta tuna kwanan gida
131. Je-ka-na-yi-ka auren bashi
132. Jinkirin jinkira, bazawara jiran karsa
133. Jinjina mai ta da maza har mata su falka
134. Juriya namiji ce, raki ko mace ce
135. Jirbo aikin surukai, a gudu da kunya, a tsaya a sha
wuya
136. Jahilar mace yawan gareta
137. Jiya ba yau ba, tsohuwa ta tuna tsarince
138. Jiya ba yau ba, tsohuwa ta ga kuɗin zance
K:
139. Ko oho saurayi na zagin wanda ya kasa shi aure
140. Ƙarambanin kaza auren muzuru
141. Ƙirmisisi Tusa gaban miji
142. Kishiya ta goje ba ki da haushi
143. Kurum baka amarya ta haɗe
kashi
144. Kowa shina son mata, sai in aljihunsa bai wuri
145. Kurum baka, amarya ta ci ɗan
masu gida
146. Ko yaro ya san matar nema daga gajeruwa sai funtuwa ko
shege da ranarsa
147. Ka ɗan
uba ya yi sheri babu mai rufewa sai ɗansa
148. Kone zafin roƙo ba a ba da ɗan masu gida
149. Karuwa ba ta kiyon kaza
150. Ko mai aka yi wa ɗa,
ya rama
151. Kowa ya ci shinkafar mace, tasa ya ci
152. Kumburin saka tusa, ko tsofuwa ta sha wuya ta haifa
153. Kada ka kula da nonan sarakuwa, kai dai yarda da
matarka
154. Ku kuka sha ta furar Naito
155. Kan mace na miye ne
156. Kyawun ɗa
ya gaji ubansa
157. Kwaraka ganin dame ce, ko a ɗakin uwarka sai ka yi
158. Kyawon mace bin miji
159. Ka haifi ɗiya
mata, su mutu, ka turbuɗe
hutawa ne
160. Kamawa ba sayarwa ba, inji yar budurwar birni
161. Komai tsakad dare mace ta san mijinta
162. Karfin mace sai yawan magana
163. Kome bukatar rai ne, abota da makauniya
164. Kome za a yi a sa gishiri, an yi wa maigida kuru
165. Kuyanga iya magana, ba ki ƙara kai taki bakin
marmaro
166. Karambanin baƙo rab da matar maigida
167. Kwanta in ga sauran, kwanciyar mai ciki da mijinta
168. Ka so ni in so ka maganin ƙiyayya rabuwa
169. Ko tsohuwa ta sha wuya ta haihu
170. Kome wayon amarya a sha manta a tandu
171. Kariyan mace kuɗɗi
172. Kowa ya ce namiji uba ne zai mutu maraya
173. Kyawun ɗa
shi guji abin kunya
174. Kundumi ga macce ƙanƙanci ne
175. Kyawun haihuwa jinƙai
176. Kishi kumallon mata
177. Kullun ɗa
kyakkyawa ne a idon ubansa
178. Kishi wuta ne, wadda ba ta warkewa
179. Kissar mata goniya tara da tara, guda ɗaya ta cikon ɗari ibilis bai san ta ba
180. Kowa da al’adar garinsa, ango ya rufe kai da turmi
181. Ko ba daɗe
dukiyar mace namiji ne zai cinye ta
182. Kowa ya mutu domin mace, ya mutu banza
183. Kowa ya haifi mace, ya haifi ɗa namiji
184. Komai mai sauƙi ne a tsakanin dangi
185. Kowa ya ce duniya uwata sai ya tabbata maraya
186. Kwana nawa ne? Maye ya yi amarya
187. Kowa ya yi haihuwa ashe ya huce
188. Kashe mani kwarkwata, in kashe maki amre
189. Kamar gobe, aure da wuri
190. Kwaram! Rigima! Barin mai ɗaki
191. Kai ma nan, mace ta rena miji
192. Kowa ke bin shawarar mace, wata rana zai halaka
193. ƙuli ƙuli kan bai wa yara, kan kutuma sai uwar gida
194. Karancin iyali wadata ne
195. Ƙaiƙai koma kan masheƙiya
196. Kauyanci amarya hawan gado da zani
197. Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa maye ya ga makashin ɗansa
198. Ƙofar
mace laya kowa sai ya rataya
199. Ƙwalisa amarya ta ga ango ba riga
200. Ƙaryar banza ga amarya ba tsaba
201. Ƙeta mai ɓata
zama
202. Kishiya mai ban haushi, ana ganin ki kan zagi miji
203. Komai son rai ne, ƙawa da makauniya
204. Kowa ya ce miji uwa ne, sai ya mutu ba a yi masa gara
ba
205. Komai daɗin
ki da miji, kishin uwar gida ya tashi
206. Komai daɗinki
da kishiya inji babbar ƙawar Amarya
207. Kyuya ba ta haifar ɗa
mai ido
208. Kakarsa ta yanke saƙa
209. Kalan magana, ance da gwauro ya iyali
210. Kowa ya so uwa ya so ‘yarta
211. Kayan magaji ai na magajiya ne
212. Ƙaƙa za a yi da abin da ya gagari wuta, inji kishiyar ƙonanniya
213. Kishi, kumallon mata, in ya motsa sai an haras
214. Kowa ya ce zo mu zauna, ya ce zo mu ɓata
215. Karkarwa kamar tsohon da ya auri budurwa
216. Kishin kishiya ba zai hana miji aure ba
217. Kai waye ke nan, bazawara da jaka
218. Ƙaƙalan gulamaɗi,
gai da uwar saurayi a kasuwa
M:
219. Mai son ɗan
ƙwarai,
ya auri isassa
220. Mai karɓa,
surukin mai kyauta
221. Matar mutum ƙabarin sa
222. Mai uwa a murhu ba ya cin tuwonsa ba miya
223. Mai uwa gindin murhu ba ya cin tuwonsa gaya
224. Mai uwa gindin murhu ba shi kukan yunwa
225. Mai uwa gindin murhu ba shi da haushi
226. Macce mai ƙwazo, za ta haihu ko ba miji
227. Magana ta ƙare, mata ta ce wa miji shege
228. Mai yawan magana yakan biya bashin kakansa
229. Mai ci da uwa ba shi kukan suɗi
230. Mace da takobi abin tsoro
231. Mata haja ne, kowa ce da tayin da ya karɓe ta
232. Masu ba mu, ana ba su, mata ta ga ana ba miji kashi
233. Mai wuya ta ƙare, uwar ɗiya
ta sayi kuyafa
234. Mai mata ɗaya
aminin gwauro
235. Matan zamani ba tukane ba ne, balle a kwankwasa a ji mi
ƙwari
236. Me za mu ce wa? Namiji da rancen saɓi
237. Maikoda ba ta son mai koda
238. Maraya ba ya gudun mutuwar uwar kowa
239. Mai uwa a murhu ba shi kukan abinci
240. Matar na tuba ba ta rasa miji aure
241. Matar na tuba ba ta laifi ga mijinta
242. Me zan ce? Zanen aro ya ƙone
243. Murna ta koma ciki, na haifu ɗa ya koma
244. Mace ba ta ikon jikinta sai miji
245. Mace darajar namiji ce
246. Mai zane ɗaya
ba ta ba da aro
247. Mata, ba a ba da aronki, ko an yi shawara a fasa
248. Maso mace wawa bai san za ta ƙi shi ba
249. Maganin mace kuɗi,
a bar kisan jemage
250. Mahaukaci ka kishin mata tana gidansu
251. Me uwa takan yi da ɗanta
sai kallo
252. Mu ‘yan matan gara ne in an ce mu ɗauka mu ɗauka
253. Matan zamani, tsoho ya ga budurwa
254. Matar fansa sai gobe ga Allah
255. Mulkin mallaka biyan bashi da ɗakin kishiya
256. Marar wuni yana gani, uwa tasa kan kwana kasuwa
257. Matar ina so ba ta wuyar shiga ɗaki
258. Matar na –ƙi mijinta na kwana zullumi
259. Mata ta rena miji, kuma ba ta yi sai da shi
260. Matar mutum abin zarginsa
261. Maganin mace mijinta
262. Mai ‘ya’ya ba matsiyaci ba ne
263. Mijin mace ya fi iyayenta
264. Matar da ba ta da amre mushiya ce
265. Mutuwar sarakuwa gajarta tafiya ce
266. Maza ba mata ba
267. Mata kuwa ba maza ba
268. Mata mance su yi maƙa gayya
269. Matar da ka amra, kuka yi shekara ukku ba ku yi ukku ba
ka saketa
270. Mace da kamar maza kwari ne babu
271. Mai dama ka shege
272. Muna ga Rasulu, an tsikari mai takaba
273. Mhm, inji matar barawo
274. Me ya fi raina? Cin tsiren mata
275. Me kuma ake jira? Bagwari ya yi toshi
276. Maraya ba ya shakkar mutuwar uwar wani
277. Matar wani ba ta wani ba ce
278. Murnar mata tana ga tafi
279. Mai hannu da yawa, baya zagin ɗan
wani
280. Mantai ba ta saba da kishiya ba, ni kuwa ban saba da
mata biyu ba.
N:
281. Namiji dangin gujiya, sai an fasa akan san na ƙwarai
282. Namiji dutse, mace sakaina
283. Nan nike son ɗan
masu gida ya tarar da bawa
284. Namijin zakara, tura mata garka ka koma da kuyanga gida
285. Namiji tonka ne, sai an tauna akan san mai yaji
286. Namiji zabo ne, ba a shafuwar bayansa
287. Na ga abin da ya ishe ni, kishiya tara ɗai rana
288. Nesa ta zo kusa an sa wa saurayi ranar baiko
289. Namiji wanda ya fi zama na ƙwarai wanda ya fi iya
magana
290. Naci tamkar kwarton kusa
291. Na taɓe
ki da alheri, an taɓi
kishiya da bakin wuta
292. Niƙa, daka, mafalkin gwauro
293. Ni a su wa kare da ɗaukar
gara
294. Namiji tabarmar ƙashi inji wacce mijinta ya ɓata wa rai
295. Namiji ba ɗan
goyo ba ne, inji wacce mininta ya saketa
296. Na shiga zinɗe,
kishi da maras hankali
297. Namiji kwaɗo,
mai share tsakar gida
298. Ni wa! Kare da waƙar gara
R:
299. Rabo, maƙwabci ya biya wa matar maƙwabci
kujerar makka
300. Rashin uwa kan sa a yi uwar ɗaki
301. Rashin haƙuri shi ya sa budurwa ta yi ciki
302. Rashin uwa hasara ne
303. Rashin kunya, mace ta auri miji
304. Raba matarka da mazaje
305. Raina, abin da mace take so
306. Rena girma kuka, bagaruwa ta fi ta
307. Ruguduma an kama kurma da kwartanci
308. Rana ba ta ƙarya, sai don uwar ‘ya ta ji kunya
309. Ribiɗin
leɓo shawara da uwar
kishiya
310. Rashin haƙuri shi ka sa budurwa farka
311. Ramin kura sai ‘ya’yanta
312. Ranar bikin farar kaza, balbela ba gayya ce ba
313. Rashin kunya, mace ta auri mace
S:
314. Son a sani, ya yi kwarin miji
315. Son kira kamar bazawara
316. Shiga ukku gwauro da yaye
317. Sukunin banza, gwauro
da baraya
318. Suruki maganin kumallo
319. Shiga uku shi ya sa suruka yin takaba
320. Somin aure, tsarince
321. Son kira kamar autar karuwai
322. Sa ni in fi ka, an sa bara tsaron gida
323. Sa ni in fika, ɗan
amarya ya hau doki
324. Sai uwa ta ƙoshi, ɗa
yake maƙoƙo
325. Sabo da yi, amarya ta haye ango
326. Son uwa shi ya kawo son ɗanta
327. Sai an so uwa akan so ɗanta
328. Son maso wani ƙoshin wahala ne
329. Sabuwar amarya ba kasafai takan yi aibu ba
330. Sai ci, maye ya yi aure
331. Saɗaka
ba mata ba sai da iyali
332. Saurayi namijin sa maza gudu kirawo ‘yan mata
333. Samanci, namiji da zuwa taron buki
334. Salula, shawara da uwar kishiya
335. Sharri takin masoya inji sabon ango
336. Sharri takin so inji sabuwar budurwa
337. Sharri takin so inji sabon ango
338. Son a sani yaji da kwarin miji har da ɗan masu gida
339. Sa kai a uku, takabar suriki
340. Sauna, matar ‘yan cirani
341. Shege, yi da mai zina
342. Shinge gabanka samari
343. So ɗanka,
duniya ta ƙi
shi
344. So ba a yin sa da gangan
345. Somi, hatsin gara a buta
346. Soyayyar gamuwar jini
T:
347. Tun ana marmari, amarya kan yi goshi
348. Tuwona maina
349. Tsofo da kuɗi
yaro
350. Tuzuru wanda ya fi gwauro ɓarna
351. Turmin tsakar gida sha luguden mata
352. Tsohuwar gida hana walwalar iyali
353. Tsarince madakin zina
354. Ta fi babu kakar wajen uba
355. Tamɓele!
Zuwa bikin dangin miji
356. Tsautsayin takaba auren mai ƙararren kwana
357. Tambaɗar
zamani mata biɗar maza
358. Tantarakwai, mata ta turke miji
359. Ta jefa ta caɓe
matar talaka ta ga ta mai arziki
360. Tilas a gyara wa amarya ɗaki
361. Tsautsayin takaba, aure da majinyaci
362. Ta ina zan fara? An ba maye jiran jarirai
363. Ta mece ce? An ba tsohuwa fucika
364. Ta yaro kyau take, ba ta ƙarko
365. Tuwon fari bai kyau ba, na yau ne zai yi
366. To, me ake jira? Bagwari ya yi toshi
U:
367. Uwa ma ba ɗa
nono
368. Uwargida sarautar mata
369. Uwa mafi uba, ko da uban Sarki ne
370. Uwar maza daka ya kashe ki
371. Uwar biki ba ruwanta da baraka
372. Uwar wani matar wani! Yaro kaɗan ka yi musu ka kawo taka
373. Uwa mai ba ɗa
nono
374. Uwar mugu, mugu ce
375. Uwa ta fi uba wajen haƙƙi
376. Uba ya fi uwa wajen mulki
377. Uwar rago ake wa barka
378. Uwar wani kakar wani
379. Uhm! Masoyan zamani, tsohuwa ta ga saurayi da buduwa
W:
380. Wanda ya auri mace don kyawunta ya auri wahala
381. Wa ya isa shi faɗa
uwar Sarki da maƙoƙo
382. Wayyo Allah na! Inji yar wawa
383. Wanda ba shi da aure, ba shi amren yar dangi
384. Wanda bai ga uwatai ba ba shi biɗar kakatai
385. Waye zai auri jahila
386. Wanda ad da mata mai kyawu, shi tashi tsaye don tsaro
387. Wa ya isa ya faɗa?
Gyambon uwar Sarki na ɗoyi
388. Wannan ai kalen magana ne, an ce da gwauro ya iyali
389. Wayyo so inji mai yin soyayya
390. Wayyo kaina inji ɗan
yaudara
391. Wani kaya sai banufa, wace ayagi mai ɗan doro
392. Wata mata ta yi tusa bare mai ciki
393. Wayon Waniƙiƙi, toshi da kare ranar Sallah
394. Wasa, wasa ne, ban da tsikarar uwar miji da taɓarya
395. Wada da wadaƙa, ta da kai da ƙishiya
396. Wadata shifci gwauro
da turaka
Y:
397. Yaya zan yi da abin da ya gagari wuta inji kishiyar ƙonanniya
398. Yar ku bar kashin jemage, maganin mace kuɗi
399. Yunƙurin banza, namiji da naƙuda
400. Yada guda ɗauki guda inji budurwar
kauye
401. Yaya aka yi uwa ta guje wa ɗanta
402. Yaro ya san matan nema, daga ba gajeriya ba a funtuwa
maras zane
403. Yaron da ka riƙon gida, tun shina ƙarami
aka sani
404. Yaro ba shi sami zumu, sai kur uwatai ta nuna mishi
405. Yaro ya so amre gidansu babu godiya
406. Yaro ya so amre gidansu ba wuri
407. Yayi auki, uwar miji ta ƙi cin tuwo
408. Ya kamata auren na gida, yarinya da ta ga wanta da kuɗi
409. Yarinya, farkonta maɗaci,
ƙarshenta
zuma
410. Ya so raha, ubanta ya hana, in ba shegen uba ba wa zai
hana ya tasa raha.
411. Yaro bari zagina gobe zan amri uwarka, in ka aure ta ka
zama ubana
412. Yin kunnen uwar shegu, shiru
413. Ya na iya da raina? Mummuna ya ga mata Yaran zamani tun
ba su tafasa ba sun ƙone
414. Yaro ya san matan nemansa
415. Yaro ba mutum ba, sai ya girma
Z:
416. Zagwaɗi
ango shiga ɗakin
amarya
417. Zagwaɗin
zamani ɗa daga ciki roƙon uba
ƙwabo
418. Zaki namijin mace, kana gida matarka na wurin ƙoto
419. Zaƙin magana kamar miyar farko
420. Zaƙin zaƙafere mai gida fere kabewa
421. Zaƙui doron kishiya
422. Zaman lafiya ya fi gara
423. Zamu hau, inji baran mai doki
424. Zance ya ƙare, sai ɗaurin
aure
425. Zanen aro ba shi rufe katara
426. Zazzaɓi
ciwon so dama Budurwa da saurayi zuru zuru ne
427. Zo mu zauna shi ne zo mu ɓata
428. Zo mu zauna ya fi zo mu ɓata
429. Zumu mai haifa wa zumu ɗa
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.