Ticker

6/recent/ticker-posts

Rashin Nasarar Sulhu a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Ga al’ada, idan aka samu rashin jituwa ko saɓani ko rikici a cikin sha’anin zamantakewa, ana ƙoƙarin ganin cewa an yi yunƙurin sasantawa da kuma shiryawa da daidaita tsakanin masu saɓanin, sai dai ba kowane lokaci wannan yunƙurin kan yi nasara ba. Akwai wasu karin magana masu nuni game da wannan kamar haka:

1. Tuwon fari bai yi kyau ba, na yau ne zai yi

Wannan karin magana tana nuna cewa idan an so a sake yin wani abu, irin wanda aka riga aka yi a baya, to amma, bai yi daɗi ba ko kyau, to idan aka ga ana shirye-shiryen sake ƙulla wannan mu’amalar. Misali, aure ga masu shirin yin sulhun kome, akan yi amfani da wannan karin maganar a matsayin gargaɗi ko hannunka-mai-sanda da nufin cewa, tun da auren da suka yi da farko bai yi kyau ba, to, in sun koma ma, ba a kyautata zaton zai yiwu (Yunusa, 1989 sh. 118).

2. Auren baya shi ne sadakin na gaba

Sadaki kalma ce wadda Hausawa suka aro daga harshen Larabci da take nufin kuɗin da shari’ar Musulunci ta yanke wa mai aure ya biya ga wadda zai aura ta hannun waliyyinta (CNHN, 2006 sh. 380). Ana amfani da wannan karin magana a nuna cewa halayyar da mutum abokin mu’amala ya nuna a zamantakewar aure ko wadda ba ita ba, a cuɗanyar da aka yi da shi a farko, to idan har wata matsala ta yi sanadiyyar yankewar wannan dangantaka, to irin halayen da abokin mu’amalar ya nuna a baya, kyawawa ko munanan ɗabi’u, su ne za su kasance musabbabin ginuwar sake ƙulla irin wannan dangantakar ko rashin yiwuwar haka.

Naɗewa

Wannan babin ya kawo jerin karin magana da suka shafi saɓani da sulhu. Hausawa sukan yi amfani da su a gurabun karin magana daban-daban domin isar da saƙonni cikin hikima. Wannan ya shafi gargaɗi game da taka-tsantsan da halin wasu mutane (maza ko mata). Ya kuma shafi bayyana hoton sasanci ko yadda sasanci yake faskara a wasu lokuta. Haka kuma, akwai karin magana da suka shafi sulhu da sasanci, waɗanda suke nuna amfanin haƙuri da zaman lafiya da bin rayuwa a sannu.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments