𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mallam Khamis Shin idan namiji ta taɓa Azzakarinsa ko mace ta taɓa farjinta sai sun sake alwala? Misali kaman mutum ya kammala wankan janaba sai ya taɓa Azzakarinsa sai ya sake yin alwala kafin yayi Sallah?
SHIN TAƁA AL'AURA YANA
WARWARE ALWALA?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan namiji ya taɓa azzakarinsa ko mace
ta taɓa farjinta kai tsaye
ba tare da shamaki (tufa) ba, alwalarsu ta warware kuma wajibi ne su sake ta.
Misali: Idan mutum ya kammala wankan janaba sannan ya taɓa azzakarinsa kafin
sallah, dole ne ya sabunta alwalar sa. Haka zalika idan mace ta taɓa fatar farjinta
(waje), alwalarta ta karye.
Wankan Janaba ya kan
maye gurbin alwala ne kawai lokacin da mutum zai shiga yin sallah bayan ya
kammala tsarki. Amma kuma, bayan an kammala wankan, idan wani abu ya faru da
zai karya alwala (kamar fitsari, tusa, ko taɓa gaba tsirara), to sai an sake yin sabuwar
alwala kafin a gabatar da sallah ko ya taɓa Alkur'ani.
Idan namiji ya taɓa Azzakarinsa ko mace
ta taɓa farjinta ba tare da
shamaki ba akwai zance biyu wanda suka fi ƙarfi na Maluma:
1. Idan mace ta shafi
farjinta ko namiji ya taɓa Azzakarinsa ba tare
da shamaki ba to alwalansa ya karye sai ya sabunta alwala. Wannan Shi ne
Mazhabar Malikiyya da Shafi’iyya da Hanabila.
Dalilan su: sun kafa
Hujja da Hadisin da aka rawaito daga Annabi (Tsira da Amincin Allah su tabbata
a gare shi) Yace: Wanda ya shafi Azzakarinsa to yayi alwala. Abu dawud: 181.
Tirmidhi: 83
Sannan sukace lokacin
da mutum ya shafi azzakarinsa sha’awar sa zata iya motsawa wataƙila wani abu ya fito
masa ba tare da ya sani ba. Sharhul Mumti’ Na Ibn Uthaymeen:
1/280
2. Idan namiji ya
shafi Azzakarinsa ko mace ta shafi farjinta ba tare da Shamaki ba to alwalarsa
bata karye ba. Wannan shi ne mazhabar Hanafiyya, da wasu daga cikin Ƴan Malikiyya Da wasu
daga cikin Magabata. Hakanan wannan shi ne Ra’ayin Sheikhul Islami
Ibnu Taimiyya da Sheikh Ibnu Uthaymeen.
Sheikhul Islam Ibnu
Taimiyya yace: Abinda yafi bayyana shi ne Shafan Azzakari baya warare alwala,
sai dai mustahabbi ne wanda ya shafi azzakarinsa ya sabunta alwala, amma wanda
yayi sallah bai sabunta alwala ba Sallarsa tayi amma idan ya sabunta to hakan
shi yafi. Majmu’u Fatawa: 21/222.
Dalilan wa’inda
sukace Shafan Azzakari ko shafan farji baya warware alwala Shi ne Hadisin da
aka rawaito daga ɗalk bin Ali (Allah ya
ƙara
masa yarda) yace: Munje wurin Annabi (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare
shi mukayi masa mubaya’a, mukayi Sallah tare dashi. Lokacin da ya
kammala sallah sai wani mutum yazo kaman mutumin ƙauye sai yace Ya
Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) me kake gani game
da Mutumin da ya shafi Azzakarinsa a Sallah? Sai Annabi (Tsira da Amincin Allah
su tabbata a gare shi) Yace masa Shin Azzakarinka menene in ba Wani ɓangare ne na jikin ka
ba? Abu dawud: 182. Annasa’i: 165.
Wannan Hadisi yana
nuna cewa idan mace ta shafi farjinta ko namiji ya shafi Azzakarinsa da
hannunsa to alwalar sa bai karye ba, domin Azzakarin sa kaman sauran gaɓɓan jikinsa ne. Kamar
yadda Annabi (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) yayi bayani a
wannan hadisi.
Wurin haɗa wannan hadisi da
wanda ya gabace shi wasu Maluman sun ɗauki umarni da Annabi (Tsira da Amincin Allah
su tabbata a gare shi) yayi kan sabunta Alwala idan mutum ya shafi azzakarinsa
a matsayin Mustahabbi ne ba wajibi ba saboda wannan hadisi na ƙarshe.
Wasu kuma sun
banbance tsaƙanin shafan farji ko Azzakari, idan mutum ya shafa da Sha’awa
to zai sake alwala idan kuma bai shafa da sha’awa ba, ba sai ya
sake alwala ba. Wannan Hukunci da muka ambata ya shafi Ramin dubura. Duka
Hukuncin su ɗaya.
A taƙaice abinda wannan
Amsa ya ƙunsa shi ne: Wacce ta shafi farjinta ko Wanda ya shafi
Azzakarinsa Da sha’awa To ya sake alwala, wanda kuma ya shafa ba
da sha’awa ba to yana da kyau ya sake alwala. Idan
kuma wacce ta shafi farjinta ko wanda ya shafi Azzakarinsa kuma akwai shamaki
kaman ya shafa akan saman wandonsa to babu komai a kansa.
WALLAHU A'ALAM
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.