Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yawan Waswasi A Cikin Ibada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUHU. Mallam Khamis barka da yamma, da fatan ka yini lafiya. Ya aiki, ya iyalai? Muna rokon Allah Ya karawa rayuwa, Ilimi da iyalai albarka, ameen!

Mallam don Allah inada wata tambaya ne wanda na keso a warware min: "Da farko dai gaskiya ina fama da matsanancin ciwo na wasiwasi, ta yanda duk wani abu da nayi na Ibadah sai naga kamar banyi daidai ba, ko kuma bai inganta ba. Haka ina yawan samun wasiwasi da kokonto a dukkan wasu aiyukana na Ibadah kamar su tsarki, Alwala da kuma sallah. Idan nayi sai naga kamar baiyi ba, ko Alwalar ya karye, ko akwai kuskure a ciki.

Toh inata iya kokarina domin naga naki biyewa duk wasu wasiwasin a dukkan abinda zai fadamin dangane da Ibadah ta, toh sai gashi yau kuma ya sake billomin da wani abu mai sarkakiya.

Mallam dazu ne da nayi Alwala domin yin Sallah, toh a yayin chanja Tufafina, sai naji kamar hannuna ta Shafa/taɓa azzakarina cikin kuskure, amman banda tabbaci. (Nafi ganin kamar saman azzakarin wajen kasan mara ya taɓa cikin kuskure yayin chanja Kaya). Toh don gudun matsalata ta wasiwasi, sai na tafi nayi sallah ta tunda bawai na tabbatar azzakarin hannuna ya Shafa ba, ina tunanin kamar idan nayi sallar na idar zai tafi ya kyaleni.

Toh bayan na idar da Sallar kuma, sai wasiwasin ya dawomin sosai akan cewa nayi sallah babu Alwala, cewa ai tunda hannuna ya shafa azzakarina yayin chanja Kaya, toh Alwala ta ta riga ta karye. Kuma ni maganar gaskiya shi ne banda tabbaci akan cewa azzakarina hannuna ya shafa yayin chanja kayan, ko kuma kasan mara wajen gashi ta taɓa, shi ne nace bari na rubuta tambayar, domin neman fatawa wajen warware wannan matsalar kokonton tawa.. Nagode Mallam!

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace: "idan ɗayanku ya tayar da sallah, toh sheɗan zaizo yana masa waswasi acikin sallar, ko ya nuna masa cewa alwalarsa ta karye don ya ɓata maka sallah. Har wani lokacin ma ka kanji iska a tsakanin duburarka kamar kayi butu. Toh Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace idan kaji haka kada ka katse sallarka har sai kaji doyin tusar ko kaji sautin fitar tusar.

Sannan sahabbai sun taɓa samun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam suka ce dashi "mutum ne yana sallah zai dinga ji ana raya masa cewa 'yayi butu (tusa)' yaji ana ce masa alwalarka ta karye a zuciyarsa. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace idan ɗayan ku yaji haka toh yace KARYA NE!

Hadisi ya tabbata daga Usman ɗan Abul Ási (Allah ya qara masa yarda) cewa: Shi Usman ɗin ya zo wurin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) sai ya ce: Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) lallai shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata, yana rikita mini karatun sallata, sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: "Wannan wani shaiɗani ne da ake kiransa da KHANZAB, duk lokacin da ka ji shi ka nemi tsarin Allah a kansa, ka tofa a ɓangaren hagunka sau uku", sai Usman ɗin ya ce: Sai ko na aikata hakan, sai Allah ya tafiyar da shi daga gare ni. Muslim 2203.

Wannan sai ya nuna cewa duk lokacin da mai sallah ya yawaita jin waswasi da tunanin zuci a sallarsa, to ya yi 'A'UZU BILLAHI MINA SHAIƊANI RAJIM' ya tofa a ɓarin hagunsa sau uku, in Allah ya so, Allah zai tafiyar masa da wannan waswasin.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace "sheɗan ba zai kyale ɗayanku ba sai ya dinga zuwa yana yi masa tambayoyi a cikin zuciyarsa. "tambayoyin da zasu jefa ka cikin bala'i" yazo ya ce maka wa ya halicci sama? sai ka ce ALLAH, yace wa ya halicci kasa? kace ALLAH, wa ya halicci kaza? Kace ALLAH, toh a karshe fa zai ce ma toh shi kuma ALLAHN wa ya halicce shi?? Toh sai manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace idan kaji wannan sai ka ce:

آمنتُ باِللًهِ ورُسلُه

"Na yi imani da Allah da Manzanninsa"

ko kace:

هُوَ الْأَوَّلُ وَالْآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ

"Shi ne Na farko, Shi ne Na karshe, Shi ne Bayyananne, Shi ne Ɓoyayye, kuma Shi Masani ne akan komai.

Allah ya bamu ka'ida kwara ɗaya dangane da sha'anin waswasi wanda shi ne "isti'aza" wanda duk lokacin da kaji sheɗan yana taɓa maka zuciya acikin sallah toh sai kayi "isti'aza kace:

أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ

kayi sau uku kamar yadda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya koyar koda kuwa atsaye kake a sallar ko a zaune ko cikin sujadah.

Mai yawan waswasi acikin sallah yayi kokari wajan yin sallah cikin jama'a wato tare da liman, Sannan mutum ya rika yin bakin kokarinsa wajen fitar da waswasi ko kokwanton daga zuciyarsa.

Malamai suka ce "wanda kokwanto ya aureshi, to ya rika yin sujadah bayan sallama".

Wato ka lazimta ma kanka yin sujadah bayan sallama duk lokacin da ka idar da sallah. Amma ba sai ka sake sallar ba.

Idan mutum ya taɓa azzakarinsa da fatar hannunsa kai tsaye (ba tare da wani shamaki ba kamar riga ko wando), malaman fikihu irin su Malikiyya, Shafi'iyya, da Hanabila sun tafi a kan cewa alwalarsa ta warware, kuma wajibi ne ya sake sabuwar alwala kafin yin sallah.

Idan mutum ya taɓa al'aurarsa ta kan riga ko wando (ba tare da fatar hannu ta haɗu da fatar azzakari ba), alwalarsa ba ta warwarewa.

Idan ya shafa azzakarinsa domin neman jin daɗi (sha'awa) alwala ta warware ba tare da wani shakka ba. Idan ya taɓa shi ba da niyyar jin daɗi ba (kamar don gyara zama ko wanka), akwai malaman da suka ce alwalar tasa tana nan, amma mafi yawan malaman mazhabar sun tafi a kan cewa shafar gabaki ɗaya tana warware alwalar.

Malaman suna ba da shawarar cewa duk lokacin da aka samu haduwa tsakanin fatar tafin hannu da al'aura, to a kiyaye addini ta hanyar sabunta alwala.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments