Ticker

6/recent/ticker-posts

Samar Da Lakabin Sunayen Kanuri (Barebari) Ta Amfani Da Sunayen Mala’iku

Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Mala’iku halitta ce da Allah Ya ƙage su daga haske. Ya zo cikin hadisi cewa:

An halicci Mala’iku daga haske, Aljannu kuma an halicce su daga tataccen harsashen wuta, Adamu kuma daga abin da aka wasafta muku (a Ƙur’ani), (Muslim ne ya ruwaito shi).

Ya kuma ɗabi’antar da su a kan yi masa ɗa’a. Ba sassaɓawa umurninSa, suna aikata abin da ya umurce su da aikatawa. A cikin Suratul Tahrim, Allah Yana cewa:

… Ba su saɓa wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma suna aikata abin da ake umurninsu (66:7).

Suna tsarkake Shi (da tasbihi) dare da rana ba su gajiya. Kuma babu wanda ya san adadin yawan Mala’ikun Allah. A cikin Suratul Muddasir Allah Yana cewa:

… Kuma babu wanda ya san mayaƙan Ubangijinka face Shi… (74:31).

Allah Ya ɗora musu ayyuka daban-daban da suke gudanarwa.

Imani da Mala’ikun Allah, rukuni ne na biyu daga cikin rukunonin imani waɗanda bayar da gaskiyar Musulmi ba ya inganta sai da shi. Musulmai sun yarda da samuwarsu, kuma su nau’o’in halittun Allah ne da Ya halicce su don su bauta masa.

Ana iya ganin Mala’ika, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata gare shi ya ga Mala’ika a cikin siffarsa (kamannunsa) ta haƙiƙa har sau biyu. Ya tabbata a cikin littafin Imam Ahmad mai suna “AL- MUSNAD” inda aka ruwaito hadisi daga Abdullahi ɗan Mas’ud (R. A.) ya ce:

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ga Jibril a surarsa, yana da fukafukai ɗari shida (600), kowane ɗaya daga cikinsu ya doɗe sasanni.

Haka kuma Sahabban Annabi S. A. W. sun ga wasu Mala’iku a lokacin da suka rikiɗa zuwa siffar ‘yandam, kamar yadda ya zo a cikin hadisi cewa:

Jibril ya zo da surar wani mutum mai tsananin farin tufafi mai tsananin baƙin gashi, ba wata alamar tafiya tare da shi, kuma babu wanda ya san shi a cikin sahabban da suke wajen (Muslim ya ruwaito shi).

Sakamakon irin matsayin da Allah Ya ba Mala’ikunSa da yadda suka kasance masu biyayya ga umurninSa. Shi ne ya sa wannan al’umma ta rinƙa sa wa ‘ya’yansu sunayen wasu daga cikin Mala’iku. Suna yin haka ne domin sunayen da halayyarsu ta yi tasiri ga su masu karɓa sunan. Akwai sunayen Mala’iku guda goma da suka fi shahara. Waɗannan sunayen sun haɗa da:

Jibril: Shi ne yake kai wahayi ga Annabawa. Ya zo a cikin Alƙur’ani a inda Allah Yake cewa:

Gaya (musu) wanda ya kasance maƙiyi ne ga Jibrila, haƙiƙa shi ne ya saukar da shi(manzanci) a zuciyarka da izinin Allah, mai gaskatawar abin da ya rigaye shi(na littattafai), kuma shiriya ne da bushara ga muminai (2:97).

Mika’ila: Shi ne mai kula da lamarin ruwan sama, sai dai ba a ambaci aikinsa a cikin Alƙur’ani maitsarki ba. An ambace shi ne tare da Mala’ika Jibrila, da suka kasance matsayinsu ɗaya a wajen Allah, kamar yadda Alƙur’ani ya bayyana (2 p. 98).

Izra’ilu: Shi ne mala’ikan mutuwa(mai karɓar rayuka), ba a faɗi sunansa ba a cikin Alƙur’ani, sai dai Allah Yana cewa:

Ka ce: “Mala’ikan mutuwa, wanda aka wakkala a gare ku shi ne ke karɓar rayukanku. Sa’an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku (32:11).

Israfilu: Shi ne wanda aka ɗora wa aikin busa ƙaho ranar tashin Ƙiyama. Shi ma ba a ambaci sunansa a cikin Alƙur’ani ko Hadisan Annabi S. A. W. ba. Kodayake an kawo bayanin busa ƙahon da zai faru don dukkan rayuka su mutu; da kuma wanda zai yi na biyu domin tayar da matattu. Allah Yana cewa:

Kuma bar sashensu, a ranar nan, yana garwaya a cikin sashe, kuma aka busa a cikin ƙaho, sai muka tara su, Tarawa (18:99).

Maliku: Shi ne yake kula da gidan wuta (Jahannama/Hawiya). Allah Yana cewa:

Kuma suka yi kira: “Ya Maliku! Ubangijinku Ya kashe mu mana. (Maliku) Ya ce: “Lalle ku mazauna ne(43:77).

Munkara da Nakiru: Su ne aka ɗora wa aikin ziyartar mamaci a kabarinsa a daren da aka rufe shi. Za su yi masa tambayoyi game da imaninsa da abubuwan da ya aikata a rayuwarsa ta duniya. Idan managarci ne, daga lokacin zai soma jin daɗinsa a cikin kabarin, idan kuma mugu ne, sai ya soma ɗanɗanar azaba. Ba ɗaya daga cikin waɗannan Mala’ikun da aka zo da sunansa ko aikinsu a cikin Alƙur’ani. Duk da haka, malaman tauhidi sun tsamo bayanansu daga hadisan Annabi da kuma ma’anar da imani da ita daga Alƙur’ani, kamar inda Allah Yake cewa:

Wuta, ana gitta su a kanta, safe da marece… (40:46).

Raƙibu da Atidu: Su ne masu rubuta lada da zunubi na kowane taliki (Binji, 1985 p. 7-8).

Kasancewar Mala’iku halitta ce mai ɗa’a da biyayya ga bin umurnin Allah sau da ƙafa, ba su saɓa masa ga dukkan umurninSa. Shi ya sa al’ummar Kanuri ke sanya wa ‘ya’yansu sunayen Mala’iku. Domin su zamanto masu samun albarkar masu sunayen tare da kwaɗayin halayyarsu ta yi tasiri ga abin haihuwar. Daga cikin sunaye goma na Mala’ikun da aka ambata, al’ummar ta fi mayar da hankali wajen sanya wa ‘ya’yansu suna Jibrila, mala’ikin da yake karɓo wahayi daga Ubangijiya kai wa Annabawa. Suna furuci sunan da Jiwurla ko Jibrin kamar yadda Wazir (2000 p. 18). Ke nan wannan ya nuna cewa al’ummar ta fi shahara wajen amfani da sunan JIBRILA.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083 

Post a Comment

0 Comments