Daga

Adamu Rabi’u Bakura, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Arbakura62@gmail.com & adamubakura@fugusau.edu.ng

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Wasu sunayen Hausawa na iya kasancewa waɗanda aka alaƙanta su da wani zamani da aka haifi abin haihuwar a cikinsa. Wannan ne dalilin da mai sunan kan karɓa laƙabin. Irin waɗannan sunaye sukan danganci jinsin maza da na mata. Misali:

a. Ɗankaka: Shi ne wanda aka haifa a lokacin da ake girbin (cire) amfanin gona.   A wasu wurare akan kira shi Ƙosau. Mace kuwa akan kira ta da laƙabin Kaka, ko Nakaka, mace kuwa a kira ta Kakale. A wasu sassan ƙasar Hausa akan kira namiji da laƙabin Yalwa, haka ita ma mace takan karɓa wannan sunan.

b. Ganau: Shi ne wanda aka haifa a lokacin da sabon wata ya fita (tsaya). A wasu yankunan ƙasar Hausa akan kira shi da laƙabin Magawata.

c. Sallau: Shi ne wanda aka haifa a lokacin biki.

d. Shanono: Shi ne wanda aka haifa a lokacin da saniya ta haihu.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083