Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Saɓanin Ma’aurata a Karin Magana
Kasancewar rashin jituwa ko samun saɓani a tsakanin ma’aurata wani yanayi ne wanda ba za a iya kauce masa ba a zamantakewa. Akwai jerin karin maganan Hausa da aka samu masu nuni ga wannan yanayi kamar haka:
1. Kai ma can, mace ta rena miji
Wannan karin magana tana ɗauke
da saƙon lafazi daga lafuzan da mace
kan yi amfani da su a wajen mayar da martani ga mijinta da ke nuna al’amarin raini a lokacin da wani tsantsami ke gudana a
tsakaninsu. Galibi hakan yakan faru ne sanadiyyar ko dai miji bai sauke
nauyinsa ba, ko kuma bai kama girmansa ba.
2. Tantarakwai mata ta turke miji
Tantarakwai kalma ce ta nuna gwanintar harshe da hikimar
zance wadda ba ta da takamammiyar ma’ana, sai dai tana nuni ne da cewa, mutum
ya yi shiru, ya tsaya cak, ya rasa abin da zai faɗa.
Ita kuwa kalmar ‘turka’ an bayyana ta a ƙamusun
Hausa (CNHN, 2006 sh. 446) da cewa, an ƙure
ƙaryarsa (maƙaryaci).
Wannan karin magana tana nuna cewa saɓani da rashin jituwa ya yi tsamari tun da har ta kai ga
tone-tonen asiri, wanda hakan bai dace da irin wannan zamantakewa ba. Tana nuna
Hausawa mata, suna da al’adar tsare miji ko su turke shi a yayin neman wata
biyan buƙata ko
domin fayyace wani abu, ko kuma idan tsiyarsu ta tashi. Ana samun irin wannan
yanayi inda mata za ta turke miji, ya kasa cewa komai ko da kuwa gaban ‘ya’ya da wasu makusantansa ne.
Wannan yanayi da ya zo cikin karin magana, nuni yake da wata ɗabi’a ta mata ga miji a duk lokacin da ta so yin tsiya ko faɗa, ko takan neman tilasta a yi mata wani abu da take so.
3. Magana ta ƙare, mata ta ce wa miji shege
Wannan karin magana tana nuna irin yadda wani lokaci yanayin
zamantakewar aure yakan taɓarɓare
tsakanin mata da miji, har abin ya kai ga zage-zage, wanda idan ya yi muni,
mace takan yi wa miji mafi munin zagi ta kira shi da mummunan suna. Idan ba a
yi hattara ba, ƙarshen
zamansu tare ke nan, ko kuma ba za su ƙara
yin kyakkyawan zamantakewa ba.
4. Son a sani, yaji da kwarin miji har da ɗan maigida
Wannan karin magana tana nuna cewa saɓani da rashin jituwa sun yi ƙamari har mace ta yi yaji ta bar gidan miji ta koma gidan
iyayenta, amma kuma saboda son a sani cewa duk da ta yi yaji tana da sauran ƙauna da soyayyar mijinta, da ta
tashi yin yaji zuwa gidansu sai ta haɗa da kwarin miji da ɗan mijinta, wata ƙila
don tana neman a sulhunta su ta koma gidan miji.
A gargajiyance, kwari ana yin sa ne da
fatan shanu ko raƙumi. Daga
baya ana amfani da duma domin samar da kwari. Kwarin duma wani jallo ne wanda
mahalba ke amfani da shi domin saka kibau, yana da ɗan
tsawo, wanda ana yin shi kamar da duma, sannan yana da faɗi
kamar dai zunguru na ɗaurin lalle na mata, amma ya ɗan
fi shi faɗi, haka kuma ana rataye shi kamar jaka don sauƙin ɗauka.
5. “Wannan don wannan,” an tura wawa biko[1]
Wannan karin maganar tana nuna al’adar biko. Biko na nufin
neman dawo da matar da ta yi yaji. Karin maganar tana bayyana cewa, idan
matsalar neman biko ta taso, ba kowa ne mutum ake aikawa ba, matuƙar ana so a cimma nasara, dole
ne a samu mutum natsattse mai mutunci kuma mai hikima, wanda zai yi ƙoƙarin samar da mafita ga matsalolin da aka bijiro masa da su,
ba wanda zai dagule lamarin ba.
6. Santarantan, yajin wata tara ba biko
Santarantan kalma ce mai nuna rashin abu, musamman na kuɗi (CNHN, 2006 sh. 399). Wannan karin magana tana juyayi game
da cewa mace ta share lokaci mai tsawo da yin yaji, amma har yanzu ba a aiko
neman biko ba daga ɓangaren miji ko kuma an aiko
neman biko, amma ba a ba da bikon ba daga ɓangaren mata. Bisa ga al’ada,
ana tura neman biko ne da wuri, kuma ana bayar da biko ne da wuri, matuƙar daidaita da auren ake so ba mutuwar
auren ba.
[1]
Akan kuma ce: "Da wannan don wannan" an aiki tsohon banza biko
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.