Ticker

6/recent/ticker-posts

Amon Gwauranci da Zawarci a Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Gwauranci na nufin zama ba aure ga namiji wanda ya taɓa aure dadai da gwaurantaka (CNHN, 2006 sh. 180). Ita kuwa kalmar zawarci tana nufin zaman gida ga matar da ta taɓa yin aure kafin ta sami wani mijin.

Wato dai, gwauranci da zawarci suna nuna yanayi ne da namiji da mace suke shiga a cikinsa bayan mutuwar aurensu. Adabin Hausa ya taskace yanayin gwauranci da zawarci a cikin ɗimbin karin maganan Hausa, waɗanda suke nuna yadda al’adar Hausawa ta kalli halin da gwauro da bazawara ke samun kansu bayan mutuwar aure kafin a yi wani ko a gyara wanda ya ɓaci idan mai gyaruwa ne.

A ƙarƙashin wannan gaɓar an tattauna wasu karin maganan Hausa da suke ƙunshe da gamayyar Gwauro da Bazawara kamar haka:

1. Jinkirin jin kira, bazawara jiran karsa

‘Jinkiri’ na nufin nawa ko makara ko daɗewa ba a yi wani abu ba (CNHN: 2006 sh. 236). Wannan karin magana tana nuna yadda bazawara take matsuwa da jiran wanda yake daidai da ita na ya zo ya nemi aurenta. Ana amfani da wannan karin magana domin a yi shaguɓe ko tsokana ga bazawara da ma duk wani wanda ya taɓa mallakar wani abu da da can wani lokaci da ya wuce, amma yanzu ya ƙagara da jiran sake samun kansa cikin wannan yanayin rayuwar da ta wuce.

2. Aikin banza karen gwauro ya kori bazawara

Wannan karin magana tana nuna cewa karen gwauro ya yi aiki marar amfani kasancewar ya nisanta maigidansa (gwauro) da abin nemansa (bazawara) tun da har ya kore ta.

Ana amfani da wannan karin magana a duk lokacin da makusanci ko mataimakin wani mutum ya yi sanadiyyar nesanta abin da yake tsammanin nema da ƙaunar ya same shi ta hanyar wani aiki da makusancin nasa ya yi.

3. Da rashin sani, karen gwauro ya kori bazawara

Wannan karin magana tana ƙarin bayani ne ga wanda ya gabace shi, inda yake nuna cewa ba da ganganci ne karen gwauro ya kori bazawara ba, sai dai da rashin sani ne na muhimmanci ga maigidansa. A ɗabi’ar kare da halayyarsa, yana son duk abin da maigidansa yake so, kuma a koyaushe tsaye yake a kan ya kare muradan maigidansa.

Ana amfani da wannan karin magana a nuna cewa abin da makusanci ko mataimakin wani ya yi, wanda hakan, har ya kai ga jawo masa hasara, ya faru ne sanadiyyar rashin sani, amma ba don ganganci ba.

Naɗewa

Ya tabbata cewa karin magana bai bar wata al’adar gidan auren Hausawa ba face ya ɗauko ta cikin hikima da fasaha domin bayyana ta a cikin ƙunshiyarsa. Karin magana a Hausa sun taskace labarai da bayanai game da abubuwan da suka shafi zawarci da kishi da saɓani da maraici da sauran muhimman batutuwan da suka shafi aure. Wasu daga cikinsu suna faɗakarwa ne da wa’azantarwa. Wasu suna gargaɗi kan sakamakon wanda ya yi zalunci a cikin zamantakewar aure ko mu’amala da take da alaƙa da aure. Wasu kuwa suna nuna hoton halin ƙunci da wasu rukunin alumma sukan shiga kamar zaurawa ko marayu da makamantansu.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments