Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwadagon Kan Intanet Da Suka Shafi Intanet Da Na’urori

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Ƙwadago a fannin intanet da na’urori yana nufin nau’o’in ayyukan da ake gudanarwa masu alaƙa da samar da wani abu ko gyara wani abu mai alaƙa da intanet ko naurori. Akwai nau’o’in ƙwadago daban-daban da suka shafi intanet da na’urori waɗanda Hausawa suka runguma a yau. A ƙasa an kawo misalan wasu daga cikin ƙwadago masu alaƙa da intanet da naurori.

A - Gina Kafafen Intanet (Website Design)

Idan aka ce kafar intanet, ana nufin website ko blog a Ingilishi. Gini ne da ake yi a kan intanet bisa tsari na musamman wanda yake ɗauke da shafi (ga kafa mai shafi ɗaya) ko shafuka (ga kafa mai shafuka da yawa).

A kullum kafafen intanet ƙara yawa suke yi a duniya. A duniyar intanet, kafafe sun kasance tamkar gine-gine da ake da su a duniyar zahiri. Binciken Reboot Online (2024 para. 4) ya bayyana cewa, a shekarar 2024, akwai kimanin kafafen intanet da suka kai biliyan ɗaya da miliyan ɗari da talatin (biliyan 1.13).

Hausawa da dama a yau sun riƙi gina kafafen intanet a matsayin hanyar cin abinci. Wani abin lura shi ne, ba sai waɗanda suka karanci ilimin kwamfuta da intanet a jami’o’i ko kwalejojin ilimi ba ne suke iya cin abinci a wannan fanni. Kowa zai iya shiga a dama da shi idan dai ya mayar da hankali wajen samun ƙwarewar da ake buƙata a fannin.

B - Gina Manhajoji (Software Programming)

Manhaja aba ce da take da siffar kafar intanet. Ana iya sauke ta a kan na’ura kamar waya ko kwamfuta domin amfani da ita. Wannan yana nuna cewa, ta bambanta da kafar intanet kasancewar ita kafar intanet, dole ne a hau ta kan burawuza kafin a iya buɗe ta. Ita kuwa manhaja tana cin gashin kanta a inda za a iya buɗe ta kai-tsaye yayin da aka sauƙe ta a kan na’ura.

A yau, buƙatar samar da manhajoji tana ƙara yawaita a duniya. Hausawa da dama sun koma amfani da wayoyin hanu wurin sauraron labarai. Lura da hakan ya sa gidajen rediyo da na talabijin suka samar da manhajojin da za su ba da damar kallo ko sauraron shirye-shiryensu ko da an riga da an kammala gabatarwa. A nan sai a lura da cewa, duk gidan rediyo ko talabijin da suka yi saken kasa sanya rigar zamani, lallai sai dai su ga ana yi.

Ko bayan waɗannan, akwai wasu nau’o’in ƙwadagon kan intanet masu yawa da suka shafi intanet da na’urori. Sun haɗa da:

a. Zana gini (UI UX designing)

b. Bayar da tsaro ga kafafen intanet da na’urori (cyber security)

c. Gwada inganci manhajoji da kafafen intanet (beta testing)

d. Gwada kutse (penetration testing)

e. Tsara manhajojin wasanni (games developing)

Akwai ƙarin nau’o’in ƙwadagon kan intanet waɗanda Hausawa suke gudanarwa bayan waɗanda aka tattauna a sama. Daga cikinsu akwai waɗanda suka shafi gyara hotuna da bidiyoyi (photo and video editing). Akwai kuma aikin tsara hotuna da zane-zane (graphic design and illustration).

A fannin bincike ma akan gudanar da ƙwadagon kan intanet a yau. A ƙarƙashin rukunin bincike ne ake samun ƙalailaice bayanai (data analysis) da kuma masu neman bayanai (data sourcing).

Bugu da ƙari, mutum yana iya ƙwadagon kan intanet a matsayin jami’in talla’ (marketing agent) ko ‘jami’in watsa labarai’ (media agent). Ana kuma iya yin aiki a matsayin ‘ƙwararren jamii mai ba da shawarwari da suka shafi kuɗaɗe’ (finance expert). Yana kuma iya kasancewa ‘jami’i mai bayar da shawarwari da suka shafi doka (legal expert) ko ‘mai jigila’ (gig work) da dai makamantansu. Da yawa daga cikin waɗannan nau’o’in ƙwadago akan same su a duniyar zahiri. Sai dai na duniyar zahirin sun yi ƙaranci sosai idan aka kwatanta da yadda hadahadar kasuwancin take a duniyar intanet. Akwai dalilan da suka sa aka fi samun su a duniyar intanet kamar haka:

A. Domin Taƙaita Kashe Kuɗi Ga Kamfanoni: Idan kamfani na aiki da ma’aikatan firilancin, to ya huta biyan su albashi kowane wata. A maimakon haka, zai riƙa biyan su ne kawai yayin da ya ba su aiki.

B. Domin Nisan Ƙwararru A Fannonin Da Ake Buƙata: Kamfanonin fassara da suke nahiyoyin da suke nesa da ƙasar Hausa, ya fi musu sauƙi su riƙa aiki da ‘yan ƙwadagon kan intanet don yi musu fassarori ta kan intanet a maimakon zuwa ƙasar Hausa domin samun mai fassara ko kuma buƙatar mai fassarar ya je can domin samun su.

Duk waɗannan nau’o’in ƙwadagon kan intanet da aka zayyano a sama, a yau akwai Hausawa da suka rungume su.[1] Daɗin daɗawa ma, har an samu maaikatu da kamfanonin Hausawa waɗanda suke gudanar da ire-iren ayyukan nan na ƙwadagon kan intanet. Daga cikinsu akwai Amsoshi Language Services (https://www.amlas.amsoshi.com)[2] da Shawsec (https://shawsec.com)[3] da 3logy (https://3logy.com.ng)[4].

Duk wanda aka ɗauka daga cikin nau’o’in ƙwadagon kan intanet da aka zayyano a sama, zai iya samun kuɗin shiga sosai (duk da ya dogara ga alƙaluma daban-daban kamar su lokaci da yanayi da ƙwarewar ɗan ƙwadago da sauransu). Binciken Nicol (2022) ya tabbatar da cewa kuɗin hadahadar kasuwar duniyar fassara kaɗai ya haura dalar Amurka miliyan arba’in ($40,000,000). Yana da wuya a fitar da ƙididdigar kason da Hausawa suka ɗauka daga cikin alƙaluman.



[1] An tabbatar da wannan bayani ta hanyar tattaunawa da waɗansu Hausawa gogaggu a harkar ƙwadagon kan intanet, da kuma bincikawa a waɗansu manyan kafafen baje kolin ƙwadago na intanet da suka haɗa da Fiverr (https://www.fiverr.com) da LinkdIn (https://www.linkedin.com) da ProZ (https://www.proz.com) da Upwork (https://www.upwork.com).

[2] Sun shahara a fannin ƙwadagon da ya shafi kimiyyar harshe da bincike.

[3] Sun shahara a fannin ƙwadagon da ya shafi tsaron kafafen intanet da na’urori.

[4] Sun shahara a fannin koyar da ilimummukan zamani kamar na’urori, intanet, saƙago da sauransu.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments