Ticker

6/recent/ticker-posts

Kunci Da Azabar Kabari

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam dan Allah wane irin ƙunci ne da azaba ke tattare da ƙabari?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Ƙuncin kabari a addinin Musulunci ya ƙunshi abubuwa kamar matsawar ƙasa, tambayoyi masu tsanani daga mala'iku MUNKAR da NAKIR, da kuma azaba ga masu laifi.

Duk wani nau'i na ƙunci akwaishi aƙabari sedai kawai azabar lahira tafi tsanani ne, sunzo a ayoyi da hadisai daban-daban bari inkawo miki misalin, Allah S.W yace:

اَلنَّارُ يُعۡرَضُوۡنَ عَلَيۡهَا غُدُوًّا وَّعَشِيًّا ۚ وَيَوۡمَ تَقُوۡمُ السَّاعَةُ اَدۡخِلُوۡۤا اٰلَ فِرۡعَوۡنَ اَشَدَّ الۡعَذَابِ‏

"Wuta za a dinga sanyasu akanta yini da dare (a cikin ƙabari) kuma ranan tashin Alƙiyama za ace kushigarda iyalan fir'auna mafi tsananin azaba" (suratu gafir ayata 46).

Ibn kathir yace acikin tafsirinshi "haka Ahlissunnah suka yarda duk wanda beyin aiki na ƙwarai za a yimishi irin wannan azabar tun a ƙabari" 4/82.

An karbo daga barra'a dan azib R.A yace; "munfita tare da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) zuwa jana'izan wani mutun daga mutanen madina se mukakai maƙabarta, alokacinda za a yimishi ƙabarin lahadi ne se Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zauna se muka zauna agefenshi, kuma kaman kace akwai tsuntsuwa akawunan mu, kuma ahannunshi akwai sanda yana caccaka ƙasa da ita se yadaga kansa sama yace; Kunemi tsari Allah daga azaban ƙabari, kunemi tsarin Allah daga azaban ƙabari sau 2 ko sau 3 yana maimaitawa sannan sai ya fadi sannan se ya fadi yanda ake ansan ran mumini dakuma ni'iman da mumini yake samu acikin ƙabari. Sannan yace ammashi kafiri inyazo rabuwa da duniya kuma yazo fuskantan lahira, wasu mala'iku zasu sakkomishi masu baƙaƙen fuskoki taredasu akwai jaka sesu zauna tare da shhi  iya ganin idonshi har sai mala'ikan mutuwa yazo seya zauna agun kanshi se yace: Ke wannan Ran gurbatacciya, kifita zuwa tsinuwan Allah da fushin Allah, seta bubbugo daga jikinshi se ya fizgota kaman yanda ake fizgo tsinken tsire daga tsire seya dauketa, inya dauketa baya barinta ahannunshi dede da ƙiftawan ido harse ya sanyata acikin kwandonnan, kuma mummunan wari irin na mushe wanda aka tsinta abanƙasa yana fitowa daga cikinta, se suyi sama da ita, Aduk lokacin da suka haɗu da wasu taron Mala'iku sesu tambayesu: wannan wata raice gurbatacciya haka? Sesuce ai wannan wane ne ɗan wane suna kiranshi da mummunan sunan da suke kirnshi aduniya, har se ankawoshi zuwa sama ta farko, se anemi abudemishi iya se aƙi yarda abudemishi saman, sannan anan se Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya karanto ayan cikin suratu A'araf ayata 40 [wacce take bada labarin hakan].

اِنَّ الَّذِيۡنَ كَذَّبُوۡا بِاٰيٰتِنَا وَاسۡتَكۡبَرُوۡا عَنۡهَا لَا تُفَتَّحُ لَهُمۡ اَبۡوَابُ السَّمَآءِ وَلَا يَدۡخُلُوۡنَ الۡجَـنَّةَ حَتّٰى يَلِجَ الۡجَمَلُ فِىۡ سَمِّ الۡخِيَاطِ ؕ وَكَذٰلِكَ نَجۡزِى الۡمُجۡرِمِيۡنَ‏

"Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kofar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi. (Surah: Al-A'raaf, Ayat: 40)

Sannan se Allah SW yace kurubuta sunanshi acikin sijjin (littafin sunayen 'yan wuta) acikin sama ta ƙasa, se ajeho Ran nashi, anan se Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya karanto aya ta 30 cikin suratu Hajj:

ذٰلِكَ وَمَنۡ يُّعَظِّمۡ حُرُمٰتِ اللّٰهِ فَهُوَ خَيۡرٌ لَّهٗ عِنۡدَ رَبِّهٖؕ وَاُحِلَّتۡ لَـكُمُ الۡاَنۡعَامُ اِلَّا مَا يُتۡلٰى عَلَيۡكُمۡ فَاجۡتَنِبُوا الرِّجۡسَ مِنَ الۡاَوۡثَانِ وَاجۡتَنِبُوۡا قَوۡلَ الزُّوۡرِۙ‏

"Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shĩ ne mafĩfĩci a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbõbin ni'ima fãce abin da ake karantãwa a kanku. Sabõda haka ku nĩsanci ƙazanta daga gumãka kuma ku nĩsanci ƙazanta daga shaidar zur. (Surah: Al-Hajj, Ayat: 30).

Se Ran nashi ta dawo jikinshi. Se mala'iku biyu suzomishi suzauna agefenshi sesucemashi; Waye Ubangijinka ? Se yace; Hahh Hahh! Bansaniba, Meye addinika? Se yace: Hahh Hahh! bansaniba, Se sucemishi me kakecewa akan wannan mutumin da aka turomuku (wato Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam)? Se yace: Hahh Hahh! Bansaniba. (sahabbai suka tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: Aiko Mumini inyaga Mala'ika tare da shhi  baze iya ansa wannan tambayarba? Se Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yajawomusu ayata 27 na Suratu Ibrahim wacce take nuna Allah ze tabbatar da mumini ya Ansasu dedai:

يُثَبِّتُ اللّٰهُ الَّذِيۡنَ اٰمَنُوۡا بِالۡقَوۡلِ الثَّابِتِ فِى الۡحَيٰوةِ الدُّنۡيَا وَفِى الۡاٰخِرَةِ ۚ وَيُضِلُّ اللّٰهُ الظّٰلِمِيۡنَ ۙ وَيَفۡعَلُ اللّٰهُ مَا يَشَآءُ

"Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so. (Surah: Ibrahim, Ayat: 27).

Se wani me kira ya kira cewa Ƙarya yayi danhaka kuyimishi shimfida na Wuta, kuma ku budemishi wata ƙofa zuwa wuta, se zafinta da ƙunanta ta dinga zuwamishi kuma se ƙabarinshi ya haɗe dashi har sai ƙashin haƙarƙarishi ya haɗu da juna.

Daganan se Aturomishi da wani makaho kuma kurma yana riƙe da guduman Ƙarfe wanda ake fasa dutsedashi wanda inda za a duke dutsen dashi da dutsen se yazama Ƙasa, se adukeshi da wannan Gudumar duk duniya kowwa zeji ƙara amma banda mutun da Aljani, se yazama turbaya se aƙara dawomishi da Rai, se wani mutun me Mummunan fiska me mummunan kaya sannan me mummunan wari yazomishi se yace: Inamaka Bishara da abinda ze saka Ƙunci yaune Ranan da akayimaka Alƙawari, se yace kai waye domin fiskanka fiskace wacce zatazo da sharri? Se yace ai nine aikinka Gurbatacce (wanda kayi aduniya), se yace: Ya Allah karka kawo ranan tashin Alƙiyama. Ya Allah karka kawo Ranan tashin Alƙiyama. Ahmad ya ruwaito 17803, Abu daud 4753. Muhaddith ya ingantashi acikin ahkamul Jana'iz shafi na 156.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya wuce ta kusa da kaburbura biyu, sai yace: "Lalle ana azabtar da su, kuma ba a azabtar da su saboda wani babban abu ba (a tunaninku): Ɗaya daga cikinsu ya kasance ba ya kiyaye kansa daga fitsari (ya na shafa kazanta), shi kuma dayan ya kasance yana yawo da annamimanci (gulma tsakanin mutane)." (Sahih al-Bukhari da Muslim).

A Wani Hadiain Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace; annunamai mutane hudu wanda akemusu azaba aƙabari;

1. Wanda ake karo da dutse dakansa yana rugurgujewa yana ihu harzuwa ranan tashin Alƙiyama. Wanna mahaddacin Ƙur'anine se ya watsardashi kuma mara zuwa Sallan farilla.

2. Me yagan kumatunshi, Hancinshi da idanunshi harzuwa ƙeya da Lauje. Wannan kuma me ƙaryane.

3. Wanda aka tubesu tsirara aka sasu awata tukunya kaman tandan waina, ana yimusu azaba suna ihu. Wannan kuma masu zina Mata da Maza.

4. Wanda akasashi acikin wani abu Ja kaman jini, ana jifanshi da dutse yana shigewa bakinshi harzuwa cikinshi wannan kuma me cin ribane. Bukhari 1386, fathul Bari 12/445.

Sayyidina Usman bin Affan (RA) idan ya tsaya a kusa da kabari ya kan yi kuka sosai har sai gemunsa ya jike da hawaye, idan aka tambaye shi sai yace naji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: "Lalle ne kabari shi ne mataki na farko na gidan Lahira. Idan mutum ya tsira a cikinsa, abin da ke bayansa ya fi sauƙi; idan kuma bai tsira a cikinsa ba, to abin da ke bayansa ya fi tsanani." Sannan ya ce: "Ban taba ganin wani abin tsoro ba wanda ya fi kabari muni." (Tirmidhi da Ibn Majah).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana koyar da neman tsari daga kuncin da azabar kabari a karshen kowace Sallah kafin sallama:

اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ الْقَبْرِ، وَمِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ فِتْنَةِ الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ

Ya Allah! Lallai ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta ta Jahannama, da fitinar rayuwa da mutuwa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments