𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Dan Allah mlm inada tmby wani mutume ne a kauye yake bada taimako amma kafin kafadi tambaya yafada ma kuma idan yabada magani yanayi shine nake so najiya shin zuwa wurinsa shirka ce ko ya abin yake ngd
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Waalaikumussalamu.
Baiwar Allah, Bai halatta kije neman magani gurinsa ba Domin wannan malamin
boka ne Kuma kafirine tantagarya Kuma zuwa wajensa shirka ne Domin dukkan wanda
zai fada maka abin da yake tafe dakai tun kafin ka fada masa Babu shakka boka ne
Saboda haka haramun ne zuwa gurin irin wadannan masu bada maganin Mutukar kika
je kika tambayeshi wani abu to Allah baze karbi sallarki ta kwana arba'in 40
ba. Idan kuwa kika gasgata maganar sa to kin kafircewa Abun da Annabin
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zo mana dashi.
Saboda haka shari'a
bata hana neman magani ba domin neman magani halal ne kuma musulunci ya tsara
hanyar da ake bi a nemi magani Saboda haka waccan hanyar batacciyar hanya ce
kuma haramtacciyar hanyar neman magani ce Kada ki rudu da cewa maganinsa yanayi
kawai ki tsarkake niyya ki yadda cewa Allah shine ke warkar da cuta tare da
neman taimakon sa ki garzaya cibiyoyin masu bada magani na musulunci ku nemi
magani idan ma cutar ta shafi jinnu zasuyi muku magani kuma su kori shaidanu da
Ayoyin Al'ƙurani ta hanyar ruƙiyya da addu'o'in da
suka tabbata a sunnah.
Sannan kuma babu lefi
kuyi mana bayanin cutar ko akwai wani taimakon da za a iya baku na addu'o'i
daga Al'ƙurani da sunnah.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.