Ƙasar Hausa ta asali tana cikin farfajiyar Afirka ta Yamma ne. Ta kasance a muhallin da yake tsakanin Hamadar Sahara da dazuzzukan da suka doshi Gaɓar Tekun Atalantika daga kudu. Ana kiran ƙasar da sunan Sudan ta yamma. Wato, tsakanin Tafkin Chadi daga gabas da guiwar Kogin Kwara daga yamma. Adamu, (1978) ya nuna cewa, ƙasar Hausa ta asali ta faro ne tun daga Lalle da Asodu, can arewa maso-gabas da Agadas. Daga can ne Gobirawa suka taso, sannu-a-hankali har suka zo inda suke zaune yau a Nijeriya.
Yanzu kuma ƙasar Hausa tana yaɗuwa ne; don
haka take ƙoƙarin komawa har zuwa muhallinta na jiya. Ƙarshen iyakar ƙasar Hausa daga kudu kuwa, shi ne Yawuri
da Zariya da muhallin da
Bauchi ta yi iyaka da Kano. Garun-Gabas (Birom) nan ne iyakar ƙasar
Hausa daga gabas.
A yamma kuwa bakinta Filinge.
A taƙaice dai, ƙasar
Hausa ita ce ƙasar
da ba buƙatar naɗa Sarkin Hausawa. Don haka yayin da aka duba taswirar za a ga cewa tana shimfiɗe ne
a Arewacin Nijeriya da kuma wani sashe na Jamhuriyar Nijar, tamkar yadda Alhassan, da wasu
(1988 p. 2) suka bayyana.
Ƙasar
Hausa galibinta a shimfiɗe take, tana da sarari mai yawa.
Tana da tsaunuka da tudunnai jefi-jefi.
Kuma manyan koguna biyu suka ratsa cikinta,
wato: Kogin Rima, da Kogin Haɗeja.
Kogin Rima shi ne ya taso daga ƙasar Zamfara ya gangara ya yi arewa zuwa Nijer,
sannan ya karkata
kudu ya bi ta Yamma da Sakkwato ya faɗa cikin Kogin Kwara.
A yau kuwa, ƙasar Hausa na kan ƙara bunƙasa da faɗaɗa. Hakan yana faruwa ne sakamakon saurin mamaya da harshen yake yi wa sauran ƙananan harsuna da suke kusa da shi. Misali, yankuna da dama na Bauchi da Gombe a yau ba su da wani harshe in ba Hausa ba. Hausa a ire-iren waɗannan yankuna ta koma harshen kasuwanci da tarukan addini da na siyasa da sauran hada-hadar yau da kullum.
Manazarta
Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.