Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausawa: Ma’anarsu da Yadda Suke

Hausawa al’umma ce fitacciya, kuma suna ɗaya daga cikin mutane mafiya shahara a doron ƙasa. Shaharar su da amon sunansu ya karaɗe farfajiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya. Hausa ita ce harshensu na uwa da suke amfani da shi wajen sadarwa.

Hausawa wankan tarwaɗa ne, ba baƙaƙe ne ƙirin ba. Akan samu farare a cikinsu, sakamakon auratayya da wasu baƙin al’ummomi, kamar Larabawa da Fulani da Azbinawa da makamantansu. Ba su da dogon gashin kai, ƙirar jikinsu da kamanninsu daidai yake da na al’ummar Aryaniyawa (Aryan), waɗanda suka zauna a tsakanin ƙasashen Turai da na Asiya, kamar yadda Adamu (2011 p. 16) ya nuna.

Hausawa suna da nagartattun halaye da suka shahara da su. Suna ɗaya daga cikin shahararrun ƙabilun da ake girmamawa a farfajiyar Afirka. Su manoma ne, masu ƙwazon noma da tanadin abinci. Jarumai ne masu juriya da ɗa’a a fagen fama. ƙwararru ne a sha’anin sana’o’i da sauran ayyukan ƙwadago.

Hausawa haɗuwar ƙabilu ne daban-daban da suka zo daga sassan duniya mabambanta, suka cuɗanya da juna, suka kasance masu magana da harshe ɗaya da ake kira Hausa, wanda ya zama harshen sadarwa da addini a tsakaninsu, kamar yadda Adamu (2011 p. 6) da Adamu (1997 p. 48) suka ayyana.

Mafi yawan haifaffun ‘yan ƙasar Hausa sukan bayyana nau’in ƙabilar da suka fito. Wasu sukan ce su Larabawa ne, wasu Fulani, wasu Barebari, wasu kuma Buzaye. Kodayake wasu ba su san ko zo–in–kashe–ka ba na wancan harshen, sai dai da’awar ce kawai. Misali, Malam Adamu Nama’aji mai ɗinkin takalmi na Unguwar Alfindiƙi da ke cikin birnin Kano, iyayensa Larabawa ne mutanen Ghadamus (Libiya). Sun zo Kano ne suka yi auratayya da Hausawa, suka zama Hausawa, kamar yadda Adamu (2011 p. 15) ya bayyana.

Haka kuma waɗanda suke riƙe da sarautar Sarkin Sharfai na Kano, zuriyar Shehu Magili ce, wanda ya zo Kano daga Madina tun a zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, domin ya ƙarfafa addinin Musulunci. Da zai koma, sai ya bar ɗansa Malam Isa da ake kira Sidi Fari, kamar yadda Dokaji, (1978 p. 21) ya nuna. Su ma sun yi auratayya da Hausawa, suka zamanto sun saje da su. Haka Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da ƙaninsa Shehu Abdullahin Gwandu, Fulani ne daga ƙabilar Toroɓɓe, kamar yadda Talata Mafara, (1999 p. 1) ya nuna. Sun jaddada addinin Musulunci a farfajiyar ƙasar Hausa, zuri’o’insu sun yi auratayya da Hausawa, sun hayayyafa, sun koma abu ɗaya, ta hanyar riƙon al’adunsu na gargajiya, waɗanda suka haɗa da: Tufafi, da abinci, da lamurran da suka danganci aure da haihuwa da mutuwa da sha’anin mu’amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni da neman ilimi da sana’o’i da sauransu, kamar yadda Gusau (2021 p. 49), da Adamu (1997 p. 49) suka ayyana.

Yayin da muka dubi gidan sarautar Kano, za a ga cewa Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo Bafillatani ne. Kamar yadda Sufi (1993 p. 106) ya nuna, amma zari’arsu sun zama Hausawa a bisa dalilan da aka bayyana a baya.

Idan aka karkata a Masarautar Zazzau da take da magada har gida huɗu. Za a ga cewa, gidan sarautar Katsinawa ne kaɗai ya kasance na jinsin Hausawa. Sauran ukun kuwa sun fito ne daga jinsuna daban-daban kamar haka: Mallawa, waɗanda Malam Musa ne farkon wanda ya hau karagar sarautar Zazzau ɗin, ya kasance ɗan asalin ƙasar Mali ne, kamar yadda Fagaci, (2014 p. sh 15) ya nuna. Shi kuwa Malam Yamusa, wanda shi ne ya kafa gidan sarautar Barebari a Zazzau, ya fito ne daga jinsin Larabawa daga ƙasar Bagdada, kamar yadda Fagachi, (2014 p. 18) ya nuna. Shi kuma Malam Abdulsalam wanda ya kafa gidan Sarautar Sulluɓawa a Zazzau, dangi ne na ƙabilar Fulani da ake yi wa Laƙabi da Iba, kamar yadda Fagachi, (2014 p. 23) ya nuna. Idan aka natsu za a tarar cewa, duk zari’o’insu sun rikiɗa sun zama Hausawa. Sakamakon auratayya da karɓar al’adu da ɗabi’o’insu har ma da harshen Hausa, wanda ya kasance ya zamar musu harshen farko (harshen uwa).

Bisa ga waɗannan bayanai za a iya cewa, Hausawa haɗuwa ce ta taron al’ummomi daban-daban da suka fito daga wurare mabambanta, suka zauna a farfajiyar ƙasar Hausa; tare da rungumar al’adu da ɗabi’u da yanayin rayuwar al’ummar Hausawa da uwa-uba harshen Hausa a matsayin harshen farko.

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments