Ticker

6/recent/ticker-posts

Alakar Neman Kudi a Kan Intanet Da Damfarar Kan Intanet

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Tarihin duniya yana cike da labaran damfara da rashin gaskiya musamman a ɓangaren neman kuɗi. Kamar yadda Johnstone (1998 p. 107) da Franceschini et al. (2023 p. 575) suka nuna, lamarin damfara kullum ƙara ƙamari yake yi a duniya. Samuwar intanet da bunƙasarsa ya buɗe sabon babi a wannan fage, wato damfara a kan intanet. ‘Yan damfarar kan intanet da suke amfani da dabarun yaudara ko ilimin kutsen na’urori da manhajoji a kullum suna gwada sa’arsu a kan al’umma.

Duk da damfarar kan intanet tana iya shafar kowa, musamman masu amfani da intanet, mutanen da suke harkokin neman kuɗi a kan intanet sun fi kasancewa cikin haɗarin fuskantar ta. Wannan yana da nasaba da yadda bayanansu suke kan kafafe daban-daban a intanet, ciki kuwa har da bayanan tuntuɓa da tarihin karatu da makamantansu. Ƙalubalen damfara da ya dabaibaye hanyoyin neman kuɗi a duniyar intanet sun jefa shakku a zukatan wasu Hausawa. Waɗansu kuwa sun tafka munanan hasarori a sakamakon faɗawa tarkon damfara.

Wannan babin ya mayar da hankali kan tattauna nau’o’in damfarar da ake samu a kan intanet. Fahimtar su ciki da waje zai yi matuƙar taimaka wa masu neman kuɗi a kan intanet domin su kauce musu.

Akwai dalilan da suka saka damfarar kan intanet ta fi shafar masu harkokin neman kuɗi a kan intanet. Duk da yake hanyoyin samun kuɗi a intanet sun zo da alfanu mai yawa (Ray et al., 2024 p. 2275-2297), to amma suna dabaibaye da ɗimbin ƙalubale.[1] Samuwa da bunƙasar hanyoyin neman kuɗi da adana kuɗaɗe da kadarori a duniyar intanet sun sake buɗe wasu sababbin ƙofofi ga yan damfara. Manyan kasuwannin duniya na kan intanet da sauran masu kafofin intanet da manhajoji suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen toshe ƙofofin da yan damfara za su iya shigo da zamba. Su ma kuwa a ɓangarensu, har kullum ‘yan damfara suna ƙoƙarin fito da sababbin dabarun gwada saarsu.

Abin da ya alaƙanta neman kuɗi a kan intanet da ‘yan damfara shi ne yadda bayanan masu ire-iren hulɗoɗin suke kasancewa a kan intanet. Babban misali a nan shi ne, ‘yan ƙwadagon kan intanet ba sa samun shahara har sai sun sanu sosai a kan intanet (strong online presence). Wannan mataki ya haɗa har da yaɗa bayanan tuntuɓa (contact information) a kan kafafe daban-daban. Yaɗuwar bayanan tuntuɓar mutum kuwa a har kullum suna ƙara buɗe ƙofofi ga ‘yan damfarar kan intanet, waɗanda suke amfani da bayanan domin yunƙurin damfarar masu su ta hanyoyi daban-daban.

Damfara ga ɗan ƙwadagon kan intanet takan zo ta fuskoki daban-daban. Akwai waɗanda za su yi ƙoƙarin damfarar mutum domin samun kuɗi ko wani abin duniya daga gare shi. Akwai kuma ‘yan damfarar da za su bai wa mutum aiki alhali ba za su biya shi ba. Ire-iren ayyukan sun haɗa da na kimiyyar harshe (fassara da gyaran rubutu da makamantansu) ko waɗanda suka shafi kwamfuta da na’urori (kamar ƙirƙirar manhaja da makamantansu).



[1] Domin samun ƙarin bayani game da ƙalubale da matsalolin da suke tattare da biɗa da tanadi a kan intanet, ana iya duba Shevchuk & Strebkov (2018) da Ansari (2020) da Sani da wasu (2023) da Sani & Yusuf (2024).

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments