Kalmomin Aikatau Na Hausa: Don Koyo Da Koyarwa a Makarantun
Masar
(Bisa Turbar Koyarwar Farfesa Ahmed
Halliru Amfani)
Na
Farfesa Muhammad Ali Noufal
Da
Malam Abdulrahaman Ado
Wannan ɗan littafi, an shirya shi domin a samar da wata makama wadda za a riƙa koyar da nazari a kan aikatau na Hausa ga ɗaliban Hausa na Cibiyar Nazari kan Afirka, Sashen Koyar da Harsunan Afirka na Jami’ar Alƙahira ta Masar.
2015
GABATARAWA
Bincike ya
tabbatar da cewa ana koyar da harshen Hausa a ƙasashen duniya
da yawa, kama daga Afirka da Asiya da Turai da makamantansu (Wurma,2006:1).
Kazalika, akan sami Hausawa da yawa a irin waɗannan wurare da ake koyar da Hausa. A wasu wuraren,
kamar ƙasashen Turai da Asiya da Afirka, bayan da 'yan ƙasashen suka
koyi Hausa a wajen Hausawa, sai suka shiga hidimar koyar da harshen ga
mutanensu da kuma Hausawan da ke zaune a can ƙasashen nasu.
Alal misalai, a ƙasar Masar, baya ga koyon Hausa da Larabawan Masar
suke yi, sai kuma suka shiga koyar da harshen ga 'yan'uwansu Larabawan Masar da
na Libiya da makamantansu da kuma Hausawan da ke zaune a Masar da kuma masu
zuwa ƙarin karatu. Bugu da ƙari, ana watsa
labarai a cikin harshen Hausa a gidajen rediyo na irin waɗannan ƙasashe (Ahmad,2012:53). Ke nan, ya zama wajibi ga
malamai da ɗalibai su agaza
wa waɗanna ƙaashe da
littafai da maƙalu da ƙasidu da mujallu da sauran duk wasu kayan aiki waɗanda za su bunƙasa nazarin
harshen Hausa a ƙasshen duniya.
Wannan ɗan littafi, an tsara shi saboda buƙata ta gaugawa
da ake da ita a kwalejoji da jami'o'in da ake koyar da harshen Hausa a Masar. A
yanzu, Misira ba ta da tsari na aikawa da ɗaliban Hausa zuwa ƙasar Hausa
domin koyo da daddalewa da daddaƙa nazarin harshen Hausa. Larabawan Misira, waɗanda harshensu Larabci ne, sukan koyi harshen Hausa a
cikin Larabci. Kuma nazarin da suke yi wa harshen Hausa a jami'o'insu, zanari
ne wanda ya yi daidai da yadda ake yi a jami'o'in Nijeriya, ba ma kamar na
Jami'ar Bayero ta Kano da Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya da Jami'ar Usman Ɗanfodiyo ta
Sakkwato. Akasarin Jami'o'in da ke cikin birnin Alƙahira, kamar su
Jami'ar Alƙahira da Jami'ar Al-Azhar da Jami'ar Ain Shams suna da
alaƙar yarjejeniyar
yin hulɗa da juna, a
hukumance (M.O.U) wadda suka sanya hannu. Saboda da haka, jami'o'in sukan
tabbatar da yin nazarin harshen Hausa kamar yadda ake yi a Nijeriya.
Matsalar da ake
samu, ita ce ta koyawa da harshen Hausa kamar yadda ake yi wa Hausawan
Nijeriya, domin malamai sun bar rubuta littafai a kan nahawun Hausa, kamar
yadda suke a adabi da al'ada. Alal misali, a fannin nahawun Hausa, malamai na
iya koyar da dukkan rukunonin nahawu, amma, bayanan da akan bayar a wajen
azuzuwan aikatau yana da ɗan wuya, wanda
kan kawo barazanar fahimta ga ɗalibai. Domin
kauce wa wannan matsala, sai aka rinƙa ɗaukar Hausawan
Nijeriya domin su koyar a cikin jami'o'in Masar, domin su bayar da cikakkun
bayanai na wasu fannonin da kan yi shigar-gizo, a wajen koyo da koyarwa.
To, abin da
kamar wuya, domin Hausawan da akan ɗauka ɗalibai ne waɗanda suka yi ilimi a fannin Larabci da ilimin addinin
Musulunci a Jami'ar Azahar ko kuma wata jami'ar ta Masar. Su ma kansu, ba su yi
nazarin Hausa ba a Jami'o'in Nijeriya. Saboda haka, koyar da wasu fannoni
"jeka-na-yi-ka" ne. Ke nan, domin ceto al'amarin daga gurgunta, ana
buƙatar wani
malami wanda ya yi nazarin harshen Hausa daga Jami'o'in Nijeriya, ya kuma san
harshen Larabci, domin ya bayar da ilimin harshen Hausa, a nan Jami'o'in Masar,
kamar yadda ake koyarwa a Jami'o'in Nijeriya.
Bugu da ƙari, malaman da suka zo Masar domin yin digiri na uku,
ba su da cikakken ilimin harshen Larabcin da za su iya koyar da harshen Hausa a
cikin Larabci. Ganin haka, Malam Abdulrahaman Ado (ɗalibin Jami'ar Alƙahira, a
matakin digiri na uku) da Farfesa Muhammad Aliy Nofal (malami a Jami'ar Alƙahira) suka yi
haɗin guiwa da haɗin ƙarfi da ƙarfe, suka fid do da wannan ɗan littafi domin ya bayar da jagoranci ga malalmai da ɗalibai, masu koyo da koyar da harshen Hausa, a Kwalejoji
da Jami'o'in ƙasar Masar.
A bisa tsarin littafin, Malam Abdulrahaman Ado
ya fara shirya bayanai na nazarin azuzuwan nahawu guda bakwai a cikin harshen
Hausa. Shi kuma Farfesa Muhammadu Ali Noufal ya fassara shi zuwa harshen
Larabci. Hakazalika, an sami bayanai da dabarun da aka yi amfani da su a cikin
wannan littafi ta yin amfani da bayanai da dabarun koyarwar malaman harshen
Hausa na Jami'o'in Nijeriya da littafan harshen Hausa da aka rubuta a Nijeriya
ko kuma waɗanda malaman
Jami'o'in Nijeriya suka rubuta. Kaɗan daga cikin malaman sun haɗa da Farfesa Ahmed Halliru Amfani da Farfesa Dauda
Bagari da Farfesa Hambali Jinju da makamantansu. Allah ya saka masu da alheri,
ya ƙara inganta
rayuwarsu, ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarsu.
BABI NA FARKO
1.0 WAIWAYEN MA'ANAR AIKATAU DAGA MASANA
Aikatau kalma
ce wadda ake yin amfani da ita a wajen nazarin kalmomi masu yin nuni aiki.Abin
nufi shi ne, kalma ce da ake yin amfani da ita a nahawun Hausa domin bayyana
aiki (Jami'ar Bayero, 2006:6). Wasu masana, sun ari kalmar Larabci ta
"fi'ili" wadda suke yin amfani da ita domin nazarin kalmomi masu nuni
da kalmomin aiki a cikin nahawun Hausa (Skinner,2007:203).To, amma duk da haka,
a mafi rinjaye, masana da manazarta Hausa sun fi yin amfani da kalmar
"aikatau" domin yin nazarin rukunin kalmomi masu yin nuni da aiki.
Saboda haka, kafin a yi bayanin a kan nazarin kalmomin aikatau, ya fi kyau a ɗan yi bitar yadda wasu masana nahawun harshen Hausa
suka bayan da ma'anarsu ta kalmomin aikatau da kuma yadda ake iya gane su idan
an gan su a cikin jimlolin Hausa. Hausawa na cewa: "Waiwaye, adon
tafiya."
1.1 Bitar Ayyukan Wasu Masana
Nahawun Hausa
Masana da manazarta Hausa sun kawo
bayanai da yawa masu yin nuni da ma'anar kalmar aikatau, kamar haka:
Da farko, Bagari (1986:105)
ya nuna ma'anar kalmar aikatau a matsayin kalmar da ke yin nuni da aiki. Kaɗan daga cikin misalan da ya kawo sun haɗa da "kama" da "duba" da
"ci" da "sha" da tafi" da makamantansu. Domin a gane
irin waɗannan kalmomi masu yin nuni da "aiki",
masanin ya bayyana cewa duk wata kalmar da ta biyo bayan kalmomin
"lamirai" masu yin nuni da "lokaci"(manunin lokaci) da ake
ce ma "aspects/tence markers" da Turanci. Misalin waɗannan kalmomi na "alamar lokaci/manunin
lokaci" sun haɗa da: "sun",
"suna", "sukan" da makamantansu.
Idan aka lura da ra'ayin wannan
masani za a ga cewa ya kawo wani "Karin-Gwaji" wanda za a iya ɗora kalmomi a kai domin a gane cewa kalma ta aikatau
ce ko ba ita ba ce. Wannan karan-gwaji kuwa shit a hanyar ɗora kalmomin a gaban kalmomin ""lamiran
lokaci", irin su "sukan" ko "sun". Idan kalmomin suka
dace……….
Sani (2007:65), ya kawo ma'anar aikatau a
matsayin kalmar da ke "ƙunshe da
aiki" wadda aka yi amafani da ita a cikin jimlar Hausa. Misalansu sun haɗa da "wanke" da "dafa" da
"soma" da makamantansu. Bugu da ƙari, ya kawo rabe-raben aikatau iri biyu dangane da
yadda ake sarrafa su a cikin jimla. Waɗannan kuwa su ne ""Aikatau
So-Karɓa" da "Aikatau Кi-Karɓa".A wajen bayanansa, ya nuna
cewa "Aikatau-So-Karɓa" shi ne wanda kalmar
"karɓau" ke karɓar ko amsar
aikin da yake a cikin jimlar da aka zanta. A cikin bayaninsa, ya nuna cewa,
kalmar "karɓau" ita ce wadda aiki ke faɗawa a kanta.Misalan da ya kawo sun haɗa da "kama" da "yanka" da "ɗebo". Shi kuwa "Aikatau Кi-Karɓa" shi ne wanda aiki bay a faɗawa a kan karɓau kai tsaye. Misalan irinsu sun haɗa da "gudu" da "cika" da
"rasu" da "ɓace" da makamantansu.
Wannan marubuci, idan aka lura, bai kawo wani
karan-gwaji ba a wajen bayar da ma'anar aikatau da yadda za a iya gane kalmomin
aikatau. Ya dai nuna cewa kalmomin aikatau suna ɗauke da aiki a
cikin jinla.
Yahaya (2008:18), ya kawo tasa
ma'anar ta aikatau a matsayin kalma mai yin nuni da aiki a cikin jimla. Yahaya
(1992:2), ya sake kawo ma'anar kalmar aikatau a matsayin kalmar da ke ɗauke da aiki a cikin jimlar Hausa. Ya kawo misalan
irinsu, kamar "share" da "ƙare" da "dafa" da "ɗumama”. Kazalika, ya kawo ire-iren aikatau dangane da irin
aikin da kalamar ke yi a cikin jimla. Abin nufi shi ne, aikin iya ɗaukar karɓau da kuma rashin iya ɗaukarsa. A don haka, ya kawo kason aikatau iri biyu,
wato "Aikatau So-Karɓa" da "Aikatau Кi-Karɓa". A cikin bayanansa, ya ce
"Aikatau So-Karɓa" shi ne irin wanda kalmomin
da aikin ke faɗawa a kansu ke biyo bayansu. Misalansu sun haɗa da "kama" da "wanke" da
yanke" da "gina" da makamantansu. Shi kuwa kason na biyu, wato
"Aikatau-Кi-Karɓa", shi ne
wanda kalmomin aikatau waɗanda aikinsu bay a faɗawa a kan wani abu. Misalansu su ne, "sanu' da
"ɓace" da "fusata" da "rame" da
makamantansu.
Shi kuwa Zarruƙ (1987:37) (an sake buga littafin a shekarra 2009), ya
ƙara bayyana ma'anar kalmar aikatau a
matsayin kalmar da ke zance a kan "aiki".
Shi ma, kamar Bagari (1986:105), ya
ce duk kalmar da ta biyo bayan kalmar "sun" to aikatau ce.Ke nan,
idan mutun na son ya gane cewa kalma aikatau ce ko ba aikatau ba, sai kawai ya
santa a cikin jimla wadda ta haɗa da kalmar "lamirin" na
"sun", to daga nan zai gane. Kaɗan daga cikin
misalan day a kawo na kalmomin aikatau sun haɗa da:
aiki,dawo, dafu, dariya, fitar, gyarawa,halaka, himma, kuka, karanto, mamaki,
magana. Maƙale,rubutu, shirya, taɓa, wartsake, zabura, da makamantansu.
Kazalika, Zarruƙ (2005:), ya kawo ma'anar kalmar aikatau a matsayin
kalma mai yin nuni da "aukuwa" ko "wakana", wadda a
koyaushe ake samunta a bayan kalmomin wakilan sunaye waɗanda ke cikin
rukunin "sun" ko "sukan" ko " za su" da
makamantansu. Ya kawo misalan irinsu a cikin jimlolin Hausa, kamar "……sun taru"
da "…..sukan wahala" da "……za su dawo" da
"…ta cika" da "….ya waye". Kazalika,
marubucin ya sake bayyana kalmomin aikatau a matsayin kalmomi masu yawan
sassauyawa (cancanzawa). Abin nufi, rukunin waɗannan kalmomi
na aikatau sun fi yawan cancanzawa fiye da sauran rukunonin kalmomin nahawu.
Ita ce kalmar da take cancanza Karin sautinta da haruffan ƙarshenta.
Bayanin wannan marubuci ya yi daidai da na
Bagari cewa akwai "Karan-Gwaji" na wasu kalmomi da ke sanya ake gane
kalmomin aikatau a Hausa, irin su "sun" da "sukan" da
makamantansu. Kuma ya kawo bayanai na “sassauya” kamanni da irin wannan kalma
ta aikatau kan yi a cikin jimla
Zarruƙ (2009:37), ya
kawo ma'anar "aikatau" a matsayin kalmomi "masu zancen
aiki". Ya ci gaba da cewa duk wata kalmar da ta biyo bayan kalmar
"sun" to kalma ce ta aikatau. Wato kalma ce mai yin nuni da aiki. Kaɗan daga cikin misalan da ya kawo sun haɗa da "ci" da "fita" da
"mutu" da "halaka" da "himmatu" da
"watsar" da "maƙale" da
"rubuta" da "zabura" da makamantansu da yawa.
Idan aka lura da wannan marubuci za a ga cewa
shi ma ya kawo kalmar "Karan-Gwaji" ko "Sikelin" da akan
iya aza kalmomin da ake kokwanton zamansu aikatau. Shi ma ya kawo misalan irin
kalmomin da ka iya zama "Karan-Gwajin" da aza a iya ɗora kalmar da ake kokwanton zamanta aikatau. Wannan
kalma kuwa ita ce "sun". Idan zancen da aka gina da ita ya yi daidai
a nahawun Hausa, to wannan kalma ce ta aikatau.
Ita dai kalmar
aikatau, kamar yadda nazari ya nuna, kalma ce mai yin nuni da abubuwa uku a
cikin nahawun Hausa, kamar haka:
Da farko, kalmar na iya yin nuni da irin
abin da wani ko wani abu ko wata ko wasu ke aikatawa. Alal misali:
Nabil yana karatu
2. Muhamud yake magana da Malam
3. Heba ce take tsaye a bakin ƙofa.
Na biyu, kalmar aikatau takan iya
yin nuni da halin da wani ko wani abu ko wata ko wasu suke ciki. Misali:
1. Samir ya ɓace a daji
2. Ado ya sagale a kan itaciya
3. Sakinatu ta haihu a asibiti
Na uku, kalmar aikatau na iya nuna wani abin
da yake faruwa a kan wani ko wani abu ko wata ko wasu. Misali:
1. Taya ta fashe a kan hanyar zuwa
Manufiyya.
2. Ayaba ta ruɓe a cikin ganyenta
3. Sanyi yana kashe mutane a Masar.
A nan, ana iya
cewa dukkan kalmomin aikatau da ake da su a cikin Hausa, za su iya kasancewa
cikin ɗaya daga cikin
waɗannan mazubai
guda uku, dangane da irin aikin da kalmar take nunawa na aiki ko irin aikin da
take aikatawa.
Daga ƙarshe, idan aka dubi waɗannan ma'anoni tare da misalan da aka bayar, za a iya
cewa, aikatau kalma ce ta nahawun Hausa mai nuna aiki a cikin jimla. Akan iya
tantance kalmomin aikatau idan aka yi amfani da kalmomin karan-gwaji, irin su:
"sun" da "suna" da "sukan". Kalmar duk da ta biyo
bayan ɗaya daga cikin
waɗannan kalmomi
da aka zayyana, na "karan-gwaji", to kalmar aikatau ce. Kazalika, ana
iya gane irin waɗannan kalmomi
ta hanyar aza su ka sikelin mazubai uku masu nuni da irin aikin da kalmar take
yi a cikin jimla.
BABI NA BIYU
2.0 TARIHIN NAZARIN KALMOMIN AIKATAU
A harshen Hausa, ajin kalmomi na
aikatau shi ne ya fi birge mazarta Hausa tun a zamanin da har zuwa yanzu.
Manyan malamai masu koyarwa a jami'o'i, sun kasa lokutan da aka yi na nazarin
kalmomin aikatau na Hausa, kamar haka:
2.1 Tsarin Farko Na Nazarin Aikatau Na Hausa
Bincike ya
tabbatar da cewa, akwai wasu Turawa da Hausawa da suka yi nazarin aikatau na
Hausa tun kafin zuwa shekarar 1960, waɗan da a nazari ake kira da sunan Manazartan
Farko.
Manzartan farko,
su ne suka zauna, suka tattara kalmomin aikatau na Hausa, suka yi nazari a
kansu. Misalansu sun haɗa da Abraham,
R.C. (1947) da Bargery (1934), waɗanda suka yi
nazarin a cikin Кamus (Dictionary) nasu. Haka kuma Bahaushe, Muhammadu
Hambali Jinju (1960)[1],
wanda ya yi nasa nazarin a cikin kundin bincikensa na digiri na uku (PhD).
Dukkan waɗannan Turawa da
Bahaushe, sun yi nazarin aikatau na Hausa ta hanyar jingina nazarinsu a kan
mizanin nazarin harshen Ingilishi, wato Turanci. Abin nufi shi ne, sun bi salon
ko tsarin da Turawa ke bi a wajen nazarin harshe. Shi ma kansa Turancin, an
jingina nazarinsa a bisa tsarin harshen Latinanci, wato Latin. Wannan al'amari
yana mishkila (matsala). Alal misalali, a harshen Turanci, idan aka kalli yadda
ake bayar da ma'anar wasu kalmomi, abin ba ɗaya ba ne da yadda suke ɗaukar ma'anarsu a harshen Hausa, kamar misalign waɗannan kalmomi:
A Turanci akwai
kalmomi irin su "Fishes" (ire-iren kifaye) da "Waters"
(ire-iren ruwaye) da makamantansu, amma a harshen Hausa, fassarar waɗannan kalmomi guda biyu na nufin "kifaye da
yawa" da "ruwaye da yawa". Ke nan, idan aka ce za a jingina
nazarin wani harshe da wani, to abin ba zai yi daidai ba, domin ana iya samun
bambanci fassarar ma'ana da makamantansu.Misali: A lokacin da Abraham (1947),
ya yi aikinsa a kan aikatau na Hausa ya tabbatar da cewa akwai aikatau na Hausa
masu "Cancanzawa". To, amma a wajensa, aikatau masu cancanzawa, ya ɗauka a cewa kalma ɗaya ce mai canzawa zuwa launi daban-daban, kamar haka:
1.Kalmar:
"shig-", tana iya cancanzawa zuwa: "shigii",
"shigaa", "shigee", "shigoo" da
"shigar".
2.Kalmar
"say-", tana cancanzawa zuwa: "sayii", "sayaa",
"sayee", "sayoo" da "sayar".
3.Kalmar:
"karɓ-", tana
iya cancanzawa zuwa"karɓii",
"karɓaa",
"karɓee",
"karɓoo" da
"karɓar"
Kenan, abin
lura a nan shi ne, kafin shekarar 1960, duk wani fasalin nazarin nahawun Hausa
ana jingina shi da tsari irin na Turanci
2.2 Tsari Na
Biyu Na Nazarin Aikatau Na Hausa
Bayan shekarar 1960, an sami wasu manazarta
nahawun Hausa suka shigo da wani tsari na nazarin kalmomin aikatau na Hausa.
Bincike ya tabbatar da cewa, wani Bature mai suna F.W. Parsons shi ne ya fara
fito da nazarin ajin kalmomin aikatau a harshen Hausa (Kraft da Kirk-Greene,
1973:145). Shi ne ya fara kauce wa binciken da Turawa manazarta harsuna suka yi
na jingina nazarin kowanne harshe a bisa gadon ko sikelin nazarin harshen
Turanci. Abin nufi shi ne, Malam Person ya ce kada a jingina nazarin aikatau na
Hausa da duk wani tsari da manazartan farko suka ɗauko yi. Ya ce ya kamata a bambanta tsarin aikatau na
Hausa da na Turanci. A cikin wata takarda da ya gabatar a kan
"Afirka", ya ce ya kamata kowanne harshe a yi nazarinsa a yadda yake
ba tare da jinginawa da wani harshe ba. Abin nufi shi ne, kamata ya yi idan za
a yi nazarin harshe, kamar na Hausa, to a yi nazarinta ita kaɗai kawai, ba tare da jingina tsarin nahawunta da na
Ingilishi ko wani haeshe ba. Abin da duk nazari ya bayar na tsarin harshen da
ake nazari, to sai a yi amfani da shi, a wajen nazarin nwannan harshi shi kaɗai.Wannan ra'ayi ya canza kuma ya bambanta daga masana
na farko.
Daga baya kuma,
aka samu wasu waɗanda suka tofa
albarkacin bakinsu a kan wannan sabon tsari na nazarin aikatau na Hausa.
Wasunsu Turawa ne, wasu kuma Hausawa ne, kamar su: Kraft da Kirk-Greene (1973)
da Jaggar (1977) da Tuller (1986) da Amfani (1996).
2.3 Fasalin
Nazarin Kalmomin Aikatau Na Persons
F.W. Persons
(wanda ke a Jami'ar da ake kira da sunan "School of Orientalist and
African Studies, Uniɓersity of London), ya gabatar da wata takarda a cikin
wata mujallar Afrika, mai taken: "Ɓerbal System of
Hausa". A cikin takardarsa, ya yi bayanin sabon tsarin nazarin aikatau
wanda ya bambanta da na waɗanda wasu suka
yi, a shekarun kafin 1960.
Da farko,
Person ya gano cewa akwai zancen "Gaɓa" a wajen nazarin kalmomin aikatau na Hausa.
Abin nufi shi ne, a cikin aikatau da ya tattara, akwai masu gaɓa ɗai-ɗaya da kuma masu gaba bi-biyu. Saboda haka, sai ya zaɓi yin nazarinsa a kan aikatau masu gaɓa bi-biyu.
Bayan nan kuma,
Persons ya sake ganowa cewa, aikatau na Hausa suna da abubuwan da ake kira
"Nau'i" (forms) da "Aiki" (function) da "Azuzuwa
Bakwai" (Seɓen Grades). Wannan sabon
ilimi da ya gano, na nazarin aikatau na Hausa, ya kawo rikici da ka ce-na ce a
wajen masana masu yin nazarin harsunan Afirka. Fitacce daga cikin waɗanda suka kawo husuma ga wannan sabon tsari shi ne
Baturen nan mai suna Arnolt. Shi kuwa ya yi haka ne, domin a lokacin a ya fara
yin nasa nazarin a kan harshen Fulfulɗe, wato Fulatanci, wanda ya fara aiki a kan azuzuwan
giredi na aikatau nasa.
A bisa wannan
tafarki, Person ya raba dukkan kalmomin aikatau na Hausa zuwa gida biyu. Akwai
waɗanda ake kira
da sunan "regular", wato waɗanda suka dace da tsarin azuzuwa bakwai da kuma waɗanda ake kira da suna "irregular", wato fanɗararru waɗanda ba su dace da tsarin azuzuwa bakwai ba. Abin nufi
a nan shi ne, idan aka ɗauki kalmar
aikatau aka aza ta bisa tsarin azuzuwa bakwai, idan kalmar ta dace, ta yi
daidai da mizanin da aka aza ta a kai, to shi ne nan, sai a kira tad a sunan
"Wadda Ta Dace" ko "Daidaitattu" (regular ɓerb). Idan kuwa
kalmar aikatau da aka aza a bisa sikelin azuzuwa ba ta dace da tsarin azuzuwa
bakwai ba, sai a kira tad a sunan "Fanɗararra" ko "Wadda Ba Ta Dace Ba"
(irregular ɓerb).
Kazalika, Person ya gano cewa,
"Daidaitattun Aikatau" ko "Miƙaƙƙun
Aikatau" (regular ɓerbs) su ne suka yi yawa a cikin harshen Hausa. Abin nufi
shi ne, su ne "Aikatau Sha-Rinjaye". Su kuwa, "Guragun
Aikatau" ko "Fanɗararru
Aikatau" (irregular ɓerbs) su ne waɗanda ba su hau tsarin giredi ba. Abin nufi shi ne,
irinsu ba a iya raba su bisa tsarin "Tushe" da "Giredi" ba.
Kazalika, irin waɗannan kalmomi
da su cika yawa ba a harshen Hausa. Abin nufi shi ne kalmomi ne na
"Aikatau Ɗaiɗaiku", waɗanda ba su da yawa a harshen Hausa.
Yanzu za mu
fara yin nazarin aikatau waɗanda suka fi
yawa a harshen Hausa. Wato, waɗanda suka hau
"gadon-karan-gwaji" na Persons, na "Daidaitattun Aikatau"
ko "Miƙaƙƙun Aikatau", kamar haka:
BABI NA UKU
3.0 NAZARIN
DAIDAITATTUN AIKATAU
Daidaitattun
Aikatau (regular ɓerbs) su ne aikatau waɗanda suke ƙunshe da sassa biyu: "Tushe" da
"Wasalin Кarshe". Abin nufi shi ne, duk wata kalmar aikatau
ta Hausa da za a iya aza ta bisa mizanin "Tushe" da "Wasalin Кarshe", idan
ta yi daidai, ko aka same tad a su, to, irin t ace ake kira:
"Daidaitacciya" (regular ɓerb). Idan kuwa
aka sami kalmar aikatau bat a bi wannan tsari ba, sai a kira tad a sunan
"Fanɗararra" (irregular).
Misali:
1."sayi"
(daidaitacciya)= say-i, say-a, say-o, say-ar.
2. "zaɓi" (daidaitacciya)= zaɓ-i, zaɓ-u, zaɓ-a, zaɓ-o, zaɓ-ar.
3."shigi"
(daidaitacciya)= shig-i, shig-u, shig-a, shig-o, shig-ar.
Bayan nan kuma,
Person ya sake gano cewa, duk wata kalmar aikatau mai gaɓa, to tana ɗauke da al'amarin da ake kira: " Tsarin Karin
Sauti".
Kenan, idan
kalmar aikatau tana da "Tushe" da "Wasalin Кarshe" da
kuma "Tsarin Karin Sauti", to za ta kasance cikin wani
"Aji" (Giredi) na azuzuwan giredi na aikatau na Hausa.
3.1 Azuzuwan Daidaitattun Aikatau Na
Hausa
A babin da ya gabata, an yi nazarin
yadda ake samun aji na aikatau, wato "giredi" a fasalin da F.W.
Persons ya bayar, na cewa dukkan wata kalma ta aikatau mai gaɓa biyu ana iya sanya ta a cikin wani aji, ta hanyar
yin la'akari da "tushenta" da "wasalinta na ƙarshe" da kuma "tsarin karin sauti".
Abin lura a nan shi ne, shi "Tsarin Karin Sauti" muhimmi ne ga dukkan
kalmomin aikatau masu gaɓa biyu-biyu, domin yana tafiya tare
da "ma'ana" ta irin aikin da aikatau ke aikatawa. Duk Bahaushe yana
iya gane irin ma'anonin da kowane aikatau ke ɗauke da shi a
cikin sauƙi.
To, a bisa irin wannan tsari ne shi
Person ya ce za a iya fitar da tsari "aji"(giredi) guda bakwai. Sai
dai kuma, akwai wasu wurare a sikelin aza kalmomin aikatau, wanda idan aka
sanya aikatau a cikin giredi, ba za su iya shiga ba. Kazalika, da wuya a iya
samun wani aikatau wanda zai iya shiga duka azuzuwan (giredi), sai dai ya shiga
wani.
Kazalika, Persons ya kasa waɗannan azuzuwan aikatau bakwai, zuwa gida biyu. Akwai
ajin da ake kira da sunan, "Ajin 'yan asali" ko "Ginshiƙai"da kuma "ajin 'yan rakiya" ko "
'Yan Haye" ko "Samammu". Abin nufi shi ne, kalmomin aikatau da
ya sanya a aji na ɗaya zuwa na uku, kalmomi ne masu
asali, waɗanda ke da tuse na asali a harshen Hausa.Wannan ne ya
sanya ake kiransu da sunan "Masu Asalai" ko " 'Yan Asali"
(basic). Su kuwa kalmomin aikatau da aka sanya a cikin rabon ko kasan aji na huɗu zuwa na bakawai, an samar da su ne daga kalmomin da
ke cikin azuzuwa na ɗaya zuwa na uku. Wannan ne ya sa aka
ba su sunan "Samammu" (deriɓed). Idan mai nazari ya tsunduma
cikin rabe-raben azuzuwan zai ƙara gane abin
da ake nufi, domin zai ga yadda aka samar da wasu kalmomin aikatau daga wasu.
Ya gabatar da kason azuzuwan kalmomin aikatau, kamar haka:
3.1.1 Ajin Aikatau 'Yan Asali ko
Ginshiƙai
Wannan aji shi ne wanda yake ɗauke da kalmomin aikatau "Muhimmai" ko
"Ginshiƙai" ko "'Yan Asali",
waɗanda babu wani ƙarin na ma'anar da suke ɗauke da ita,
fiye da yadda aka san su. Idan kuwa aka sami wani ƙari, to wani abu zai shiga. Ga yadda suke:
3.1.1.1 Aji Na Ɗaya
Aji na ɗaya shi ne yake
da "Tushen Kalma" da "Wasalin Кarshe" na: -à/-àà da "Karin
Sauti" na "Sama- Кasa" (S/К / H/L), waɗanda ke bayar da "ma'ana"
Misali:
a).Káám-à/àà (to catch):
kaama/kaamaa (to catch).
b).Zúb- à/àà (to put): Zuba/Zubaa
(to put).
A waɗanan misalai,
kalmomin da suka ƙare da gajeran wasali, kalmonin da
za su biyo bayansu a cikin jimla, kan kasance "Suna". Amma kalmomin
da kan ƙare da dogon wasali, kalmomin
nahawun da kan biyo bayansu "Wakilin Suna" ne.
3.1.1.2 Aji Na Biyu
Kalmomin aikatau da kan kasance a wannan aji su ne waɗanda baya ga "Tushen Kalma", to, "Wasalin Кareshe" da suke ƙarewa da shi yana ɗaukar fasali uku, kamar haka: -áá/-éé/-íí. Kuma,
"Karin Sauti" na wannan aji, yana kasancewa "Кasa-Sama". Misali:
a). Sàyáá= Ado ya sayaa
b).Sàyéé= Ado ya sayee ta
c).Sàyíí= Ado ya sayii mota
A wannan Aji
(giredi), wasu kalmomin aikatau ba su iya shiga ko hawa sikelin ko mizanin
awonsu. Misali, kalmar: Kààm-. Alal misali, a harshen Hausa, Hausawa ba su
cewa: Ado ya kaami akuya.
3.1.1.3 Aji Na Uku
Bugu da ƙari, a bisa kason da Person ya kawo, ya ce akwai kalmomin
aikatau na Hausa masu ɗaukar
wani tsari kamar haka:
a) "Tushen kalma".
b) "Wasalin Кarshe" na –a.
c) "Tsarin Karin Sauti" na Кasa-Sama (К/S).
d) Ma'ana:
Misalan irin kalmomin da kan iya hawan wannan Aji sun haɗa da waɗannan:
1) "Bur-": Bùrá (to ripen)
2) "Nun-":Nùná(to ripen)
3) "Ruɓ-":
Rùɓá (fermented/decayed)
4) "Zub-": Zùbá (poured)
5) "Ɗìg-":Ɗìgá (drop)
3.1.1.4 Aji Na Huɗu
Aji na huɗu
yana da siffofi na waɗannan:
a). Tushe: Kar-, Say-, d.s.
b). Wasalin Кarshe na: -e/-ee
c). Karin Sauti: Sama-Кasa (S/К)
d). Ma'ana: Hamdama/Kammalawa (totality).
Misalan irin kalmomin aikatau da za su iya shiga cikin
wannan aji sun haɗa da
waɗannan:
1."Say-: Sáyèè/ Sàyéé. Kabiru ya sàyéé shi
2. "Kar-:Kárèè/Kàréé = Samir ya karee mutuncinsa
3.1.1.5 Aji Na Biyar
Wannan aji yana da siffofi masu ban sha'awa kamar haka:
a) Tushe Kalma:Shig-, Say-, d.s.
b) Wasalin Кarshe na: -ar
c) Karin Sauti na: Sama-Sama ( ̸ ̸ )
d) Ma'ana: Dalili (causatiɓe)
e) Suna nuna motsi zuwa ga wani wanda mai magana yake magana
da shi ko wajen muhallin da ake magana (Motion toward the society).
Misalan kalmomin aikatau waɗanda kan iya shiga cikin wannan aji sun haɗa da waɗannan:
1).Say-: Sáyár= Noufal ya sáyár da keken Ado
2).Zub-: Zúbár= Nabil ya zúbár da furar Muhammad
3).Shig-: Shígár=Huda ta shígár da jarrabawa cikin
littafi.
4).Wats-: Wátsár= Hammad ya wátsár da aikinsa.
5).Sar-: Sárár = Ali ya sárár ma A'isha goro
3.1.1.6 Aji Na Shida
Kamar sauran azuzuwa, shi ma aji na shida ana bin salo iri ɗaya da sauran a wajen fitar da siffofinsa, kamar haka:
a). Tushen Kalma: Misali: Kaw-,Say-,Daw-, etc
b). Wasalin Кarshe: -oo
c).Karin Sauti: Sama-Sama (S/S)
d). Ma'ana: An zo da.., An taho da.. (motion toward the
speaker). Abin nufi shi ne, wannan Aji na 6, yana nuni da ma'anar "an sayo
wani abu, an taho da shi. Idan aka ce "Sáyí", yana nufin a can wani
wuri aka yi aikin, amma bai taho da shi ba.
Misalan kalmomin aikatau da kan iya shiga cikin wannan aji
sun haɗa da waɗannan:
1). Tah- : Táhóó = Bilkisu ta táhóó gida
2). Kom- : Kómóó= Nabil ya kómóó daga garin
Manufiyya
3). Jay-oo : Jáyóó = Bashir ya jáyóó igiya
4). Kaw-oo : Káwóó= Ibrahin ya káwóó alheri.
5). Kwantoo- : Kwántóó= Aliyu ya kwántóó shanu.
3.1.1.7 Aji Na Bakwai
Aji na ƙarshe a wannan nazari shi ne Aji na bakwai. Shi me salon
fitar da siffofinsa ɗaya ne
kamar sauran. Akan fara fitar da tushe da sauran kayayyaki kamar haka:
a) Tushen Kalma; Misali: Burk-u, Bah-u,etc
b) Wasalin Кarshe: -u (gajere)
c) Karin Sauti: Кasa-Sama (К/S)
d) Ma'ana: Yin abu yadda ya kamata/ Yadda ake buƙata (Passiɓe).
e) Misalan kalmomin da kan iya shiga a cikin wannan aji sun
haɗa da waɗannan:
1). Say-u:Sàyú = Akuyar ta Sàyú
2). Dah-u: Dàhú =
Abincin ya dàhú
3). Kaɗ-u: Kàɗú
= Кwan ya
kàɗú
3.1.2 JADDAWALIN
AZUZUWAN AIKATAU BAKWAI
|
AJI |
ƊAFI/ ƊORIYA/ WASALIN КARSHE |
KARIN- SAUTI |
MA'ANA |
KARƁA
|
MISALAI |
|
ƊAYA |
-a/aa |
S/К ( ̸ \ ) |
Gwargwadon Yadda Kalmar Ta Zo |
Mafi Yawa So-Karɓa |
Yánkàà Kátsàà, Cíkàà, Tsárgàà |
|
BIYU |
-aa/ee/i |
К/S (\ ̸ ) |
Raba Wani Abu Daga Muhallinsa |
So-Karɓa/ Raunana |
Ròƙáá, Yànkáá, àráá, |
|
UKU |
-a |
К/S (\ ̸ ) |
Wanzarwa/ Gudanarwa/ |
Кi- Karɓa/ Кarfafa |
Cìká, Nùná, Bùrá |
|
HUƊU |
-e/ee |
S/К ( ̸ \ ) |
Kammalawa Duka/ Nuna Gama Aiki Sarai |
So-Karɓa/ Raunana |
Káshèè Búɗèè Kárɓèè Múrɗèè |
|
BIYAR |
-ar (da) |
S/S ( ̸ ̸ ) |
Musabbabi / Haddasa /Dalili/ Sanadi |
So-Karɓa / Raunana |
Cíyár (da) Sáyár (da) Jéfár (da) Shígár(da) |
|
SHIDA |
-oo |
S/S ( ̸ ̸ ) |
Motsi Mai Tunkarar ko Doso Mai Magana |
So-Karɓa/ Raunana |
Kárɓóó, Yánkóó, Ɗébóó, Кwátóó |
|
Bakwai |
-u |
К/S ( \ ̸ ) |
Gamawa ko Kammala Aiki Yadda Ake Buƙata |
Кi-Karɓa / Кarfafa |
Yànkù, Tsóótsù, Bùùɗú, Bùgú |
Abin lura a nan, shi ne misalan da aka bayar ba iyakarsu ke
nan ba. Kalmomin aikatau na Hausa suna da yawa. Abin dai da ake so shi ne, idan
mutum na son ya gane ajin da wata kalmar aikatau ta kamata ta kasance, shi ne,
sai ya sanya ta cikin mizanin kason da Persons ya yi, idan ta shiga, sai a
lissafa ta a cikin ɗaya
daga cikin ajin da ta shiga. Mai nazari na iya duba littattafai da takardu na
Jinju (1980) da Bagari (1986) da Amfani (2004) da Kraft (1973) da makamantansu
domin samun ƙarin
bayanai.
BABI NA HUƊU
4.0 NAZARIN
GURAGUN AIKATAU
Guragun aikatau
su ne kalmomin da nazarinsu bai yi daidai da tsarin da ake bi na nazarin
aikatau ba. Abin nufi shi ne, kalmomin aikatau ne dab a a iya raba su zuwa
"tushe" da "Aji" (giredi), kamar yadda aka yi nazarin
"daidaitattun kalamomin aikatau, a baya. Kazalika, irin waɗannan kalmomi, yawancinsu suna ɗauke da gaɓa ɗaya.
Tambayoyi
1.Kawo sunayen
mutanen da suka yi nazarin aikatau na Hausa kafin shekarar 1960.
2. Kafin
shekarar 1960, masana harshen Hausa sukan aza nazarinta a bisa wani mizani.
Tattauna.
3.Kawo bayani
na juyin-juye-halin da nazarin harshen Hausa ya shiga bayan shekarar 1960.
4. Me masana
nahawun Hausa ke nufi da "Giredi"
5. Manazarta
aikatau na Hausa sun kasa su zuwa biyu. Caccaki wannan zance tare da ɗauraye shi da kyawawan misalai.
MANAZARTA
Abraham, R.C. (1978). Dictionary of Hausa language. Hodder and Stoughton
Educational Ltd.
Ahmed, I. B. (2012). Ɗimbin
muhimmancin harshen Hausa, Muryar Arewa. Fitowa Ta 9. Northern Communication
and Media Services LTD.
Sa'id da wasu (editoci) (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami'ar Bayero. Cibiyar Nazarin
Harsunan Nijeriya.
Skinner, N. (2007). Ƙamus na Turanci
da Hausa. English-Hausa Illustrated Dictionary. Babban Ja-gora ga Turanci. The
Northern Nigerian Publishing Company.
Wurma, A. G. (2006). Daidaitacciyar Hausa Da Ƙa'idojin Rubutu. Olatunde Rasheed Publishing Works,
Kaduna-Nigeria.
Yahaya, I.Y. Da Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun
Sakandare. Littafi Na Biyu. University Press Plc, Ibadan, Nigeria.
Zarruƙ, R.M. (2005). Bishiyar Li'irabi A
Nazarin Jumlar Hausa. Bugu Na Biyu. Institute of Education, Ahmadu Bello
University, Zaria-Nigeriya.
Zarruƙ, R. M. (2009). Sabuwar Hanyar
Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare. Littafi
Na Biyu. University Press Plc, Ibadan-Nigeria.
[1] An sami bayanai daga Farfesa Ahmed Amfani, a lokacin da yake yin laccarsa ga manyan ɗalibai masu neman digiri na biyu a Hausa, a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, a shekarar 2006. Jinju shi ma ya bi tsarin Turawa a kundinsa na biyu da ya yi a Masko, a 1960)

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.