Ticker

6/recent/ticker-posts

Kai Daga Gare Ni Kake, Ni Kuma Daga Gare Ka Nake

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Mallam Khamis da fatan ka wuni lafiya gaskiya muna jin dadin wannan channel ko groups naka mai tarin albarka. Allah ya saka maka da alkahiri. Malam khamis tambayata itace; wani sahabi ne Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace masa "Kai daga gare ni kake, ni kuma daga gare ka nake"?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Wannan Hadisi (magana) ya zo ne game da Sayyidina Ali bn Abi Talib (RA) da kuma Sayyidina Ja’afar bn Abi Talib (RA). Da Sayyidina Julaybib (RA).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fada musu wannan kalamai ne a lokuta daban-daban don nuna tsananin kusanci, soyayya, da hadin kai a tsakaninsa da su.

SAYYIDINA ALI BN ABI TALIB (RA); Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce masa: "Kai daga gare ni kake, ni kuma daga gare ka nake" (ANTA MINNI WA ANA MINKA). A wani ruwayar kuma, ya ce: "Ya Ali! Kai ne ni, ni kuma kai ne". A wani hadisin kuma, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce masa: "Kai ne dan'uwana kuma abokina".

Wannan hadisi ne ingantacce, wanda aka ruwaito a cikin Sahihul Bukhari. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fada masa haka lokacin da suke jayayya da wasu sahabbai kan wacce za ta rike 'yar Sayyidina Hamza. A wancan lokacin, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce wa Aliyu: «Kai daga gare ni kake kuma ni daga gare ka nake».

Wannan matsayi ne na tsantsar soyayya, hadin kai, da kuma cikakkiyar biyayya, wanda ya sa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana cewa: "Babu mai son ka sai mumini, kuma babu mai ƙinka sai munafuki".

Wasu malaman tarihi da hadisi sun yi bayanin cewa wannan furucin yana nuna tsananin kusanci, soyayya, da hadin kai ne tsakanin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da Sayyidina Ali (RA), sakamakon dangantakar jini (dan'uwa ga mahaifinsa), surukanta, da kuma taimakon da Ali (RA) ya baiwa addinin Musulunci tun yana matashi.

SAYYIDINA JA’AFAR BN ABI TALIB (RA); Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya taɓa kwatanta shi da halittarsa da kuma dabi'unsa inda yace masa: "Ka yi kama da ni a halittata da kuma dabi'ata." Haka zalika, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce masa: "Kai daga gare ni kake, ni kuma daga gare ka nake".

A wani ɓangare na wannan hadisin, Manzo (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi masa bushara da cewa zai shiga Aljanna, kuma a ranar kiyama zai zama shugaban masu tashi da fuka-fukai guda biyu (wato Ja'afar al-Tayyar).

SAYYIDINA JULAYBIB (RA). Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya furta wannan kalma ta soyayya ga wani Sahabi mai suna JULAYBIB. Bayan wani yaki da aka yi, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nemi JULAIBIB, aka gano ya yi shahada. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya tsaya a kansa ya ce: «Ya kashe su, sannan suka kashe shi, kai daga gare ni kake kuma ni daga gare ka nake».

Wadannan hadisai da dama sun tabbatar da irin matsayi mai girma da wadannan sahabbai suke dashi wurin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) na dangantaka ta jini da ta addini.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments