Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Na Kwata Bacci Sai Na Yi Mafarkin Saduwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum. Dan Allah inada yar tambaya ta ne. Malam ni budurwace kuma kusan ko dayaushe idan na kwata bacci sai nayi mafarki an yi amfani dani dan Allah me hakan yake nufi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Yawan yin mafarkin saduwa kan faru ne sakamakon tsananin sha'awar jima'i, da tsananin tunani game da abokin aure. ko kuma a matsayin wata hanya ta halitta da jiki ke fitar da tsohon maniyyi (wanda aka fi sani da wet dreams a turance). Jiki yana cigaba da samar da maniyyi; idan ya cika kuma ba a fitar da shi ba, jiki kan zubar da shi da kansa ta hanyar mafarki. Matasa da matan da ke gab da al'ada (period) kan fuskanci hakan saboda karuwar sinadaran sha'awa.

Wasu lokutan kuma, abinda kika sanya azuciyarki harma kike yawan yin tunaninsa, shi ne kikafi ganinsa a barci. Wato idan kina yawan tunanin Jima'i acikin ranki, to babu mamaki don kinyi mafarkin abinda ke zuciyarki. Shagaltuwa da tunanin jima'i ko kallon hotuna da bidiyoyin batsa kafin barci yana sa kwakwalwa ta dawo da su a mafarki.

A wasu lokutan kuma yawan mafarkin saduwa yana da alaqah da shafar Shaiɗanun Aljanu. Wato Aljanun soyayya (JINNUL AASHIQ) ko abin da aka fi sani da Namijin Dare, shi ne aljanin da yake shiga rayuwar mace ta hanyar soyayya, saduwa da ita a mafarki, ko hana ta yin aure. Shi irin wannan mafarkin wani lokacin yakan zo ne ta sanadiyyar rashin kwanciya da alwala ko kuma rashin yin azkar kafin kwanciya.

Idan irin wannan mafarkin ya faru kuma mutum ya farka ya ga alamun maniyyi, wajibi ne ya yi wanka na tsarki kafin ya gabatar da sallah ko wasu ibadu.

Don magance wannan matsalar, yana da kyau kiyi waɗannan matakai kafin ki kwanta:

1. Ki tabbatar kina da alwala kafin ki kwanta bacci. Yin alwala kafin barci yana hana shaiɗanun aljanu su kusantarki da irin wadannan munanan mafarkai.

2. Ki Karanta addu'ar kwanciya barci, tare da tofa addu'a a tafin hannunki (kamar Ayatul Kursiyyu da suratu Al-Ikhlas, Al-Falaq, da An-Nas) ki shafa jikinki. Kuma ki yawaita karanta ko kunna Suratul Baqarah a cikin gida ko a daki kafin ki kwanta bacci.

3. Ki nesanta kai da kallon abubuwan motsa sha'awa. Ko saka tunanin jima'i a cikin ranki domin hakan na iya sa kwakwalwarki ta dinga gina miki shi a matsayin mafarki yayin da kike bacci.

4. Ki Guji cin abinci mai nauyi sosai da daddare kafin barci.

5. Ki Sanya kaya masu kyau da kaurace wa kwanciya tsirara.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments