Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Wasu halaye ne waɗanda al’ada tana kallon cewa mata ne kawai ke ɗabi’antuwa a kan su, amma saboda zuwan yanayi da kuma zamani ya sanya waɗannan halayen ko ɗabi’un su ma maza sun shiga an dama da su.

1. Darajar mace miji.

2. Gwatsine, aikin mata.

3. Haɓaka, namiji da niƙa.

4. Ina ruwan maza da wankan jego.

5. Juriya namiji ce, raki ko mace.

6. Kallabi tsakanin rawunna!

7. Ƙarfin mace sai yawan magana.

8. Kowa ya ce namiji uba ne, zai mutun maraya.

9. Kowa ya ci shinkafar mace, tasa ya ci.

10. ƙundumi ga mace ƙasƙanci ne.

11. Lamari sabo, namiji da surfe.

12. Mace da kamar maza, kwari ne babu.

13. Mace da takobi, abin tsoro.

14. Mace darajar namiji ce.

15. Maganin mace kuɗi, a bar kisan jemage.

16. Maso mace wawa bai san za ta ƙi shi ba.

17. Mata haja ce, kowa da tayin da ya karɓe ta.

18. Mata in ba ku ba gida.

19. Mata suna suka tara, amma halinsu ya bambanta.

20. Maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na ƙwarai.

21. Maza kama suka tara, amma halinsu ya bambanta.

22. Maza ma’aminta kowa ya ba ku gaskiya ya faɗi.

23. Me za mu cewa, namiji da rancen saɓi.

24. Murnar mata tana ga tafi.

25. Namiji barkono ne, sai an tauna akan san yajinsa.

26. Namiji darajar mace ne.

27. Namiji ƙanen ajali.

28. Namiji kwaɗo ne, mai share tsakar gida.

29. Namiji zabo ne, ba a shafuwar bayansa.

30. Namiji zakara ne, ba da ƙwaya ka ci tsakuwa.

31. Sabon Salo, namiji da gazal.

Waɗannan karin magana guda 31, suna magana a kan halayyar namiji da macce ko miji da mata a al’adar Bahaushe.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449