Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Ga al’adar zamantakewar aure idan aka samu saɓani ko rashin jituwa tsakanin miji da mata, kuma aka yi ƙoƙarin sulhunta matsalolin da suke faruwa tare da yunƙurin daidaita tsakaninsu, to idan sulhun bai yi nasara ba, sai wannan saɓanin ya haifar da sakamakon mutuwar aure ta hanyar saki (shika). Akwai jerin karin magana waɗanda mata sukan yi amfani da su a wajen mayar da martani ga maza, idan aurensu ko na ‘yan’uwansu ya mutu. Ga wasu daga ciki kamar haka:
1. Namiji ba ɗan goyo ba ne, inji wacce
mijinta ya sake ta
Wannan karin magana, mata suna amfani da ita su yi arashi ga
maza don su nuna cewa ba a ba su amana ɗari bisa ɗari, domin lamarinsu ba ya da tabbas. Mace na iya ɗaukar lokaci tana shayar da su ruwan zuma, su kuma su yi
mata sakayya da shayar da ita ruwan maɗaci.
2. In aure bai kawo shi ba, saki ya kawo shi
Wannan karin magana tana nuna cewa idan zaman lafiya da lamuran
farin ciki da jin daɗi ba su sa mutum ya yi wani abu
ba, to tashin hankali da damuwa da matsuwa suna tilasta shi ya aiwatar da
wannan abun.
Idan aka saki mace, kuma ta san cewa mijinta yana tsananin
son ta, takan yi bugun gaba da cewa, Kodayake mijin ba yakan zo gidansu ba
saboda ana zaune lafiya, to yanzu lalurarsa ta tilasta shi ya zo, saboda tana
son ta nuna cewa sai ya yi nadama. Baya ga haka, wasu surukai ba su zuwa gidan surukansu sai da
dalili na rashin jituwa ko wani saɓani ko kuma zuwa na rashin
lafiya ko na zuwa a jawo hankalin ita matar ko kuma shi mijin, don a samu
daidaito da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakaninsu.
3. A rashin masoyi, akan zauna da maƙiyi
Wannan karin magana tana nuna cewa da soyayya da ƙauna ne kyakkyawar zamantakewa
take ɗorewa, amma duk wata mu’amala ko
cuɗanya da aka gina ta ba a kan
soyayya ba, to ba za ta ɗore ba, domin a al’ada da ɗabi’ar mutum ba ya cuɗanya da abin da yake ƙi, sai in bai samu abin da yake
so ba. Mata suna amfani da wannan karin magana su bayyana cewa tun da ba masoyi
suka rasa ba, me zai sa su ci gaba
da zama da maƙiyinsu!
Wannan karin magana tana nuna cewa, shi mutum ko mace ta rasa wanda take so,
misali idan a gidan su aka hana mata wanda take so ko wadda yake so, to yana
ganin ita wadda aka haɗa shi da ita, ko aka haɗa ta da shi, kawai za ta zauna ne zaman biyayya na iyaye, ba
don tana so ba, domin in ta ƙi
son shi to shi wanda take so ba za a ba ta shi ba, za ta yi ɓatanɓakatantan, ba wan ba wan karatun ɗankama. Da a ce ta ɓata wa mahaifanta rai, gwara ta yi
haƙuri ta zauna da shi a hakan, har
ranar da Allah ya raba su.
4. Kowa ya ce namiji uba ne, zai mutu maraya
Wannan karin magana, mata suna amfani da ita ne su nuna cewa
ba a dogara ga miji gaba ɗaya, tare da yi wa ‘yan’uwansu
mata hannunka mai sanda da cewa duk macen da ta damƙa lamuranta kacokam ga mijinta
kuma ta aminta da cewa shi ne kowa ga maganin matsalolinta da kuma biyan buƙatunta, to, sai ko ta wayi gari
wata rana ba ta da kowa, domin kuwa zamantakewarsu na iya kawowa ƙarshe, ta kuma rasa kulawarsa da
tausayinsa da ƙaunarsa.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.