Ticker

6/recent/ticker-posts

Fitattun Hanyoyi Uku Na Damfara a Kan Intanet (Fitar Kudi Daga Akawun, Kadaitarwa, Amfani Da Muhimman Abubuwa)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Fitar Kudi Daga Akawun a Matsayin Tarkon Damfara a Kan Intanet

Ɗaya daga cikin tarkon yaudarar da ‘yan damfara a kan intanet suke kafa wa mutane shi ne nuna cewa kuɗi ya fita daga akawun ɗinsu (akawun ɗin waɗanda ake son damfara). Wani lokaci kuma za su nuna cewa wasu kuɗaɗe suna shirin fita daga akawun ɗin. Sukan yi hakan ne domin ruɗa mutum tare da cusa masa tunanin cewa wasu ‘yan damfara suna ƙoƙarin amfani da katinsa na banki ko wata lalitarsa ta kan intanet domin yin sayayya a kan intanet.

Idan mutum bai yi hattara ba, ruɗewa da gaggawan ganin ya shawo kan matsalar za su rufe masa idanu. Daga nan zai yi ƙoƙarin tuntuɓar kamfanin da aka ce an sayi kaya a wurinsu domin dakatar da odar. A zahiri kuwa, kamfanin na basaja ne. A duba misali a hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 3.11: Saƙon Basaja Na Fitar Kuɗi Zuwa Kamfanin McAfee

Madagara: Saƙon damfara da aka tura zuwa abuubaidasa5@gmail.com

McAfee kamfani ne sananne da ya shahara wajen samar da kariya daga baros ɗin kwamfuta da na’urori. Kwastomomi sukan biya kuɗi domin su samu wannan fasahar kariya. Waɗannan ‘yan damfara sun nuna cewa ana ƙoƙarin biyan kuɗi daga wannan email (abuubaidasani5@gmail.com) zuwa kamfanin McAfee. Daga nan suka bayar da lambar wayar da za a tuntuɓe su idan ana son bayar da rahoto game da wannan sayayya.

A zahirin gaskiya kuwa, basaja ce kawai suka yi da sunan wannan kamfani domin ruɗa waɗanda suke tura wa saƙon ta yadda za su kira lambar wayar. Idan an kira lambar wayar, za su iya tambayar bayanan bankin wanda ya kira, ko kuma bayanan lalitarsa ta kan intanet. Suna iya amfani da waɗannan bayanai domin satar kuɗi daga akawun ɗinsa ko lalitarsa.

Kwaɗaitarwa a Matsayin Tarkon Damfara a Kan Intanet

Kwaɗaitarwa babban tarkon damfara ne wanda ‘yan damfara a kan intanet suke ɗana wa mutane. Suna bin hanyoyi daban-daban domin kwaɗaitar da mutane game da wata garaɓasa da za su samu. Tana iya kasancewa samun wani kuɗi ko data ko katin waya. A duba hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 3.12: Kwaɗaitarwa Zuwa Ga Garaɓasar Data

Kwaɗaitarwa Zuwa Ga Garaɓasar Data

Madogara: Saƙon damfarar da aka yi ta yawo da shi a kafar WhatsApp wajajen 2024-2025

A wannan hoto, za a ga cewa ‘yan damfarar suna kwaɗaitar da mutane ne zuwa samun garaɓasar data daga kamfanonin sadarwa na MTN da Airtel. Abin lura na farko shi ne, kafar intanet ɗin da aka kawo a cikin liƙau ɗin, ba ta da alaƙa da kamfanonin sadarwar.

Amfani Da Wani Muhimmin Abu Da Yake Faruwa a Matsayin Tarkon Damfara a Kan Intanet

Da zarar duniya tana fuskantar wani muhimmin al’amari, to ‘yan damfarar kan intanet sukan yi amfani da wannan damar domin fito da wasu sababbin hanyoyin damfara. Duk lokacin da bukukuwan duniya suka taso kamar bukukuwan addini (salla ko kirsimeti), ko bukukuwan shekara, da sauransu, saƙonnin damfara sun rinƙa yawo ke nan a shafuka da zaurukan kafafen sada zumunta. Haka lamarin yake kasancewa yayin da aka fuskanci wata annoba, misali annobar Korona da makamantansu. A duba misali a hoton da aka kawo a ƙasa:

Hoto Na 3.13: Amfani da zuwan Kirsimeti domin yaɗa saƙon damfara

Amfani da zuwan Kirsimeti domin yaɗa saƙon damfara

Madogara: An yaɗa wannan saƙo a zaurukan WhatsApp

An ɗauko wannan ne daga wani zaure a WhatsApp ranar 17 ga watan Disamba, shekarar 2024. Za a iya lura da cewa, a lokacin ana fuskantar bukukuwan Kirsimeti. Kasancewar Kirsimeti yakan zo da shagali mai yawa ciki har da kyaututtuka da bonanza iri-iri, da wannan dama ‘yan damfara suke yin amfani domin ƙirƙiro hanyoyin gwada saarsu a kan mutane.

Za a iya lura da cewa, wannan liƙau ɗin da suka bayar (https://cut-ly.com/Opay-Xmas-Bonus) kwata-kwata ba shi da alaƙa da kamfanin Opay. Haka kuma, bayanan da suke cikin kafar ba daga kamfanin Opay suke ba. Yan damfarar sun samar da bayanai da suke alaƙanta su da wannan kamfani domin jan hankalin mutane.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments