Ticker

6/recent/ticker-posts

Fahimtar Tarkon ‘Yan Damfarar Kan Intanet

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Damfara ta shafi yin amfani da dabarun yaudara domin karɓar wani kuɗi ko wani abu mai daraja irin ta kuɗi daga hannun wani. Idan aka ce abu mai daraja a duniyar intanet, bai taƙaita ba ga nau’o’in abubuwa masu daraja a duniyar zahiri dangin zinare da azurfa da tufafi da sauran abubuwan amfani. Abubuwa masu yawa a duniyar intanet suna da daraja, sannan za a iya sarrafa su domin samun kuɗaɗe daga gare su. A bisa wannan, yayin da aka karɓi ɗaya daga gare su daga hannun mutum cikin yaudara, to an damfare shi ne. Damfarar kan intanet ya haɗa har da:

a. Karɓar keɓantattun bayanai (personal information)

b. Ɓata wa mutum lokaci

c. Sauya wa mutum tunani ko daƙushe masa fahimta

d. Saka mutum wani aiki a kan intanet babba ko ƙari (misali hawa kan wata kafar intanet domin danna wani talla (advertisement)) da sauransu.

‘Yan damfarar kan intanet suna amfani da wasu dabaru a matsayin tarkon da mutane za su yi saurin faɗawa. Sukan karanci wani al’amari da yake da jan hankali wanda zai iya kawar da tunanin mutum tare da sanya shi yanke hukunci cikin gaggawa ko zumuɗi. A wannan ɓangare na littafin an kawo wasu misalan tarkon da ‘yan damfarar kan intanet suke amfani da su.

Damfara a duniyar intanet tana zuwa cikin sigogi daban-daban. Akwai waɗanda suka shafi tura saƙon yaudara (malicious message) wanda yake ɗauke da liƙau ko wasu fasahohi da za su iya tatsar bayanan wanda aka turawa. Akwai kuma waɗanda suka shafi yaudarar mutum ta hanyar kwaɗaita masa wata garaɓasa ko rahusa, a inda kwaɗayi yana iya jan sa zuwa sayen kayan boge ko sanya lambobin katin kuɗi ko bayanansa a kwandon ‘yan damfara. Sakamakon tsarin intanet na game-duniya, babu wata hukuma ko ƙasa da za ta iya dakatar da ayyukan damfarar kan intanet. Hasali ma, ko su kansu gwamnatoci da hukumomi ba su tsira daga fuskantar barazanar ‘yan damfara da masu kutse a kan intanet ba. A bisa haka, babbar hanyar wanyewa lafiya ita ce amfani da rigar zamani wajen cigaba da neman ilimi dangane da wannan ƙalubale da zamani ya zo da shi. Fahimtar sigogin damfarar kan intanet da matakan kauce musu za su taimaka matuƙa wajen tseratar da ‘yan ƙwadago da ‘yan kasuwar kan intanet har ma da sauran al’umma daga faɗawa komar ‘yan damfara.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307 

Post a Comment

0 Comments