Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfarar Ayyuka a Kan Intanet (Job Scam)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Wannan nau’i ne wanda ya shafi yaɗa bayanai da liƙau ɗin boge dangane da ɗaukar aiki. Za ta iya yiwuwa a yi amfani da sunan wani kamfani amintacce kuma sananne. Za kuma ta iya yiwuwa a yi amfani da sunan kamfanin boge da adireshin boge.

Idan bayanai kawai ‘yan damfarar suke son tatsa, za su ja hankalin mutane zuwa ga yin rajista ko tura buƙatar neman aikin a kan intanet. A fom ɗin da za su cike, za a buƙaci su sanya dukkannin bayanan da ‘yan damfarar suke nema. Da zarar sun sanya waɗannan bayanai, shi ke nan zance ya ƙare. ‘Yan damfarar za su yi caraf da bayanan nasu.

A ɓangare ɗaya kuwa, tana iya yiwuwa ‘yan damfarar kuɗi suke son tatsa daga mutane. Idan haka ne, za su bi wasu matakan na daban domin cimma manufarsu. Wani lokaci sukan buƙaci a biya wani kuɗin yin rajista ko na zamowa mamba a kamfani da makamantansu. Suna kuma iya buƙatar a turo kuɗi domin nema wa mutum biza (visa) idan aikin a ƙasar waje ne. Wanda duk ya tura musu kuɗi, to kuɗaɗensa sun bi shanun sarki.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments