Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Intanet ya zo da hanyoyin neman kuɗi daban-daban. Kamar yadda aka tattauna a babi na biyu na wannan littafin, akwai hanyoyi masu yawa na neman kuɗi a duniyar intanet. Wannan nau’in damfara yana fakewa a inuwar ire-iren kasuwancin neman kuɗi da ake da su a intanet domin ida baƙaƙen manufofinsa. Wannan yana nufin ‘yan damfara sukan fake da ƙarancin ilimin da mutane suke da shi game da yadda harkokin kasuwancin duniyar intanet suke gudana domin damfarar su.
Damfarar saka hannun jari ɗaya ne
daga cikin nau’o’in damfarar da suka fi zama ruwan dare a kan intanet. Ya ƙara yaɗuwa musamman yanzu da harkokin kuɗaɗen duniyar intanet suke daɗa bunƙasa. Manazarta irin su
Kuo & Tsang (2023) da Ramli et al. (2023) sun yi bincike dangane da wannan
nau'in damfarar. Yana ɗaya
daga cikin nau’o’in damfarar kan intanet wanda Hausawa masu yawa suka faɗa komarsu.[1]
Manyan makaman da masu wannan nau’in damfara suke amfani da su, su ne:
1. Sukan tsara kafar intanet mai
kyau ɗauke da bayanai
da hotuna da bidiyoyi masu jan hankali.
2. Sukan fito da tsarin
kasuwancin da akan gina a kan biyan lada ga duk waɗanda suka yi gayyata (referrals). Bugu
da ƙari,
sukan saka bayanan riba mai kauri da za a samu a kasuwancin sannan su riƙa tura
wannan ribar ga waɗanda
suka yi rajista. Abin lura a nan shi ne, sukan yi amfani da kuɗaɗen rajistar sababbin mambobi ne wajen biyan waɗannan kuɗaɗe.
Ɗaya daga cikin ire-iren waɗannan kasuwancin damfara da yanzu haka ake
yi shi ne 52U. Wani abin ban mamaki shi ne yadda har aka fassara
kafarsu ta intanet zuwa Hausa. Hakan yana nuni ga yadda Hausawa da dama suke
cikin harkar. A duba misali cikin hoton da aka kawo a ƙasa:
Hoto Na 3.8: Kafar intanet ta 52U cikin harshen Hausa
Madogara: Kafar 52U (https://www.52u.today/index.php)
Wani misalin damfarar saka hannun jari da aka yi a baya wanda ya ritsa da
Hausawa masu yawa shi ne Dubai Gold Souk.[2] Ko bayan su akwai ire-iren waɗannan da aka yi da dama a baya. Dukkanninsu sun kafu ne a
kan manufar ƙarya ta kasuwancin zamani wanda ake
gudanarwa a duniyar intanet. Yawanci sukan fake da cewa, ana gudanar da
kasuwancin ne da taimakon ƙirƙirarriyar basira.
[1] M.M.
Manga (keɓantacciyar tattaunawa,
21 ga watan Agusta 2024) da A.M. Manga (keɓantacciyar tattaunawa, 21 ga
watan Agusta 2024) da A. Sani (keɓantacciyar tattaunawa, 24 ga
watan Agusta 2024).
[2] Y.
Idris (keɓantacciyar tattaunawa,
Janairu 2019) da A. Sulaiman (keɓantacciyar tattaunawa, 20 ga
watan Agusta 2024) da A. Bello (keɓantacciyar tattaunawa, 20 ga
watan Agusta 2024) da I.A. Isa (keɓantacciyar tattaunawa, 20 ga
watan Agusta 2024).
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.