Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfarar Kasuwanni Da Shagunan Bogi a Kan Intanet (Online Shopping Scams)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

A yau akwai kasuwanni da shaguna masu yawa a intanet. A cikinsu ana gudanar da harkokin saye da sayarwa cikin sauƙi da sauri bisa tsarin zamani mai ban sha’awa. Mafi yawan abubuwan da ake kasuwancinsu a duniyar zahiri, akan same su a duniyar intanet. Sun haɗa da littattafai da kayayyakin ayyukan gida da na’urori da injuna da tufafi da sauransu. Haka kuma, akwai kasuwannin da suka shafi kasuwancin kuɗaɗe da kadarorin intanet. Wasu daga cikin fitattun kasuwannin kan intanet su ne:

1. Amazon (www.amazon.com): Babbar kasuwa ce ta kan intanet wadda a cikinta ana sayar da abubuwa masu tarin yawa. A ciki har da kayan wuta da tufafi da kayan abinci da na’urori da littattafai da sauransu.

2. AliExpress (www.aliexpress.com): Kasuwar kan intanet ce da ake samun kaya cikin farashi mai rahusa. Kayayyakin da suke sayarwa sun haɗa da na wuta da na’urori da na ayyukan gida, da sauransu.

3. Forever 21 (www.forever21.com): Sun shahara a ɓangaren kayan kwalliya da kayayyakin ƙawa na maza da mata da yara.

‘Yan damfara sukan yi amfani da wannan dama a inda suke buɗe kasuwanni ko shagunan sayar da kaya na boge a kan intanet, sannan su tura liƙau ɗin ga mutane. Waɗanda suka yaudaru za su biya kuɗaɗen kaya a kan intanet. Duk wanda ya faɗa komar wannan nau’in damfarar ana iya yi masa illa ta fuskoki guda biyu:

1. Za ta iya yiwuwa damfararsu ta taƙaita ne kawai ga karɓar kuɗaɗen da aka turo ba tare da sun tura wa wanda ya yi sayayyar kaya ba. Wannan yana nufin, idan mai sayayya ya biya kuɗi, za a cinye kuɗinsa sannan ya ji shiru ba tare da an tura masa kayan da ya saya ba.

2. Za ta iya yiwuwa damfararsu ta haɗa har da tatsar bayanan katin kuɗin da mutum ya yi amfani da su domin aikata wani nau’in damfara na daban.[1]

Ayyukan Cotitu (2022) da Jin (2023) sun nuna yadda wannan nau’in damfara yake ƙara yaɗuwa, musamman yanzu da hulɗoɗin cinikayya a kan intanet suke ci gaba da bunƙasa. Bugu da ƙari, mutane suna ƙara faɗawa tarkon ire-iren waɗannan damfarar sakamakon yawan sayayya a kan intanet. Sayayya a kan intanet abu ne da zamani ya zo da shi, wanda yake ƙunshe da sauƙi da hutun jiki. Ya zo ne domin ya dawwama, sannan ya ci gaba da bunƙasa. A bisa haka, abin da zai kyautu shi ne mutane su faɗaka, su samu ilimi dangane da hanyoyin kare kai daga damfarar duniyar intanet domin tsira daga gare shi.



[1] An tattauna nau’in damfarar da ya shafi tatsar bayanai a sama, a ƙarƙashin 3.3.1.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments