Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfara Online: Tatsar Bayanai Daga Kafafen Sada Zumunta

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Babu wata manhajar sada zumunta da ta tsira daga damfara. Mafi yawan manhajoji da kafafen intanet na sada zumunta suna bakin ƙoƙarinsu wajen fito da matakan daƙile damfara da zamba. Duk da haka, ba a samu wata hanya taƙamaimai ingantacciya ta daƙile ayyukan damfara a kan wata kafar sada zumunta ba ya zuwa yau. Akwai kafafen da suke yunƙurin daƙile ayyukan damfara ta hanyar fito da tsare-tsare irin su:

a. Kai Rahoto (Reporting): Wannan tsari yana bayar da damar kai rahoton wani mai akawun ko wani saƙo da aka turo. Tura rahotanni masu yawa game da wani mutum yana iya sa a rufe akawun ɗinsa. Idan saƙo ne kuma, yana iya sa kafar ta ayyana wannan nau’in saƙo a matsayin na damfara. Yawanci akan buƙaci mai kai rahoto ya zayyana dalilinsa na kai wannan rahoto. Za ta iya yiwuwa saboda an dame shi da saƙonnin da ba ya so, ko saboda an turo masa saƙon damfara, ko an ci zarafinsa, da dai dalilai makamanta waɗannan.

b. Katangewa (Blocking): Wannan tsari ne da yake bayar da dama ga mai akawun ya katange wanda ba ya son mu’amala da shi. A kafafe irin su WhatsApp, akan bayar da zaɓin Katangewa da Tura Rahoto (Block and Report).

Wani ƙalubale da yake tattare da tsarin Kai Rahoto da na Katangewa shi ne, alƙaluman manhajoji suna iya kulle mai akawun alhali bai yi wani laifi ba. A shekarar 2023 zuwa 2024 an kulle wa Hausawa masu yawa WhatsApp a dalilin rahotannin da ba na damfara ko zamba ba ne. Misali, an kulle wa wasu daga cikin jagororin zauren WhatsApp akawun a dalilin sun yi ƙoƙarin sanya wasu mambobi a ciki. Zauren kuwa ba na damfara ba ne. Zaure ne na Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa Da Ƙasa a Kan Rayuwa Da Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru wanda Sashen Harsuna Da Al’adu ta Jami’ar Tarayya Gusau ta shirya a shekarar 2024.[1]



[1] International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa’idu Faru, organized by the Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Zamfara, Nigeria (2024)

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments