Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfarar Cin Kyauta a Kan Intanet (Prize Scams)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Akwai nau’o’in damfarar da suka shafi turo wa mutum saƙon cewa ya ci wata kyauta sakamakon harƙallolinsa a kan wasu kafafen intanet na musamman. Wani abu da yake sa a yaudaru da irin wannan damfara shi ne nau’in saƙon da ake turowa. Yawanci akan turo shi a matsayin sanarwar kan na’ura (push notification). Danna ire-irensu zai kai ga ko dai yin kutse zuwa na’urarsa, ko kuma tatsar bayanai daga gare shi.

A wasu lokutan sukan kasance cikin tsarin kyautar shekara-shekara ko saboda wata nasara da wani kamfani ya samu. Da zarar wani sabon al’amari dangin nasara ya faru da wani kamfani, kamar zagayowar shekarar kafawa ko buɗe sabon reshen kasuwanci, to ‘yan damfara za su yi amfani da wannan damar domin gwada sa’arsu. Misalan waɗanda aka yi a baya-bayan nan sun haɗa da:

a. Bonanzar tsofaffin layukan waya (MTN, Airtel, 9mobile, GLO)

b. Bonanzar kamfanin Ɗangote a sakamakon buɗe matatar man fetur

c. Bonanzar godiya daga Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a matsayin godiyar cin zaɓe da ya yi[1]

Akwai abubuwan da ya kamata masu amfani da intanet su riƙa tunawa a koyaushe waɗanda za su taimaka musu wajen kauce wa faɗawa tarkon ire-iren waɗannan damfarar. Babu hikima a ce wani kamfani ko wata mai’aikata ko gwamnati ta turo saƙon gama-gari ga mutane cewa su bincika ko suna daga cikin waɗanda suka dace da wata kyauta. Yayin da ma’aikata ko kamfani suka tashi yin ire-iren waɗannan kyaututtuka, sukan bi tsararrun hanyoyi ne domin gudanar da hakan.

Wani ƙarin abin lura shi ne, duk wanda ya hau liƙau ɗin da aka bayar domin bincikawa, za a nuna masa cewa yana daga cikin waɗanda suka yi nasara. Ko da zai sake hawa da wani imel na daban, za a sake taya shi murnar cewa ya samu nasara.

Ko bayan waɗannan, yawanci akan buƙaci ya tura liƙau ɗin zuwa wasu zauruka a kafafen sada zumunta kafin a ba shi damar cire kyautarsa. A lura da cewa, ta haka ne ake ƙara samun waɗanda za su iya faɗawa tarkon damfarar. Yayin da mamban wani zaure wanda ake girmamawa ya turo irin wannan sauƙo, akwai waɗanda za su iya tunanin cewa na haƙiƙa ne.



[1] An tattaro misalan waɗannan daga zaurukan WhatsApp daban-daban na Hausawa. An tattauna batun a zauren Sa'idu Faru Conference (FUGUS, 2024) a watan Yulin shekarar 2024.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments