Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
A yau, duniya ta kai wani matakin da ana iya cewa babu wani babban kamfani a duniya wanda ba ya amfani da kafar intanet da imel. Tallata haja da bayyana manufofin kamfanoni yakan kasance a kan intanet a yau. Da dama daga cikin manyan kamfanoni suna da tsarin biyan ma’aikata da gudanar da hadahadar kuɗi masu yawa a kan intanet. Kamfanoni suna matuƙar bayar da muhimmanci a kan tsaron kafafensu na intanet da imel da sauran na’urorin kamfani.
Yawanci ba a iya kutsawa cikin na’urori da manhajojin kafaffun kamfanoni
har sai idan an samu ganganci ko haɗin kai ko kuskure daga ɗaya daga cikin jami’ansu. Yayin da ‘yan
damfara suka samu damar yin kutse a akawun ɗin imel ko wata hanyar sadarwa na ɗaya daga cikin jami’an wani kamfani, hakan
yakan zo da mummunar illa. ‘Yan damfara suna iya yin amfani da wannan damar
domin damfarar ma’aikata ta hanyoyin da suka haɗa da:
1. Neman su biya wasu kuɗaɗe
2. Neman su tura wasu bayanan
sirri
Waɗanda
suke da matuƙar lura ne suke iya kauce wa wannan nau’in damfarar kasancewar saƙonnin
za su je gare su ne daga akawun ɗin
sanannen jami’i.
A shekarar 2019 ne wata kotu a Amurka ta tabbatar da wani mutum mai suna
Evaldas Rimasauskas a matsayin ɗan damfarar kan intanet wanda ya damfari Google da
Facebook kuɗin da ya haura dalar Amurka miliyan ɗari
(sama da miliyan $100). Ya yi hakan ne kuma ta hanyar amfani da kamfani da imel
na boge. Sannan ya yi ta tura takardar boge ta biyan kuɗin
aiki (invoice).[1] Idan har za a iya yin irin
wannan damfara ga manyan kamfanoni irin su Facebook da Google, lallai akwai buƙatar a sake mayar da hankali tare da yin takatsantsan don
kauce wa faɗawa tarkon ‘yan damfarar kan intanet.
[1] Domin
samun ƙarin bayani ana iya duba: Huddleston (2019) da
Rome (2019).
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.