Ticker

6/recent/ticker-posts

Damfara: Fitattun Hanyoyin Tatsar Bayanai a Kan Intanet (Phishing Scams)

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Duk wani keɓantaccen bayanin mutum yana iya zama makamanin da za a iya amfani da shi domin damfarar mutumin. Yayin da mutane suke bakin ƙoƙarinsu wajen kare bayanansu, yan damfara kuma suna bin duk wata hanya da za su iya samun bayanan. Hanyoyi da dabarun da yan damfara suke amfani da su domin tatsar bayanai a kan intanet suna da yawa. Za a iya kasa su zuwa manyan rukunoni guda uku:

i. Tatsar bayanai ta amfani da kafafen intanet

ii. Tatsar bayanai ta amfani da manhajoji

iii. Tatsar bayanai ta hanyar kiran waya

iv. Tatsar bayanai ta hanyar kutse a na’ura

i. Tatsar Bayanai Ta Amfani Da Kafafen Intanet

‘Yan damfara suna iya gina kafar intanet da za ta ba su damar tatsar bayanai. Yana da kyau a lura da cewa, yayin da mutum ya sanya ‘sunan mai akawun’ (username) da ‘kalmar sirri’ (password), to sukan tafi rumbun bayanan kafar intanet ɗin ce. Kafafen da ba su da tsarin tsaro na musamman sukan bayyana waɗannan bayanan sirri ga masu kafafen.

‘Yan damfara sukan samar da ire-iren waɗannan kafafe sannan su ja hankalin mutane domin sanya bayanansu a kafafen. Yayin da suka sanya bayanan nasu, su kuma za su ɗauke su domin yin amfani da su a matsayin makamin damfara.

Babbar dabarar da ‘yan damfara suke amfani da ita domin tatsar bayanai ta wannan hanyar ita ce kwaɗaitar da mutane game da samun wani abu. Wannan abin zai iya kasancewa kuɗi ko datar waya ko katin waya ko wata kyauta ko wata dama. Daga nan za a nemi mutum ya sanya bayanansa domin samun garaɓasar. Da zarar ya kwaɗaitu har ya kai ga saka bayanan nasa, shi ke nan zance ya ƙare! A duba misali a ƙasa:

Hoto Na 3.6: Liƙau ɗin damfara a kan intanet

Liƙau ɗin damfara a kan intanet

Madogara: An yaɗa shi a WhatsApp a shekarar 2024

A wannan hoto, za a ga cewa kwaɗaitar da mutane ake yi zuwa ga aikin Hajji a kyauta. Za a iya lura da cewa, sun yi amfani da fitaccen sunan da yayin da aka ji shi, za a yi tunanin tallafin gaskiya ne (wato Mohammed Bin Salman Hajj Sponsorship).

Ga duk wanda yake ankara da harkokin damfara kuwa, kai-tsaye zai tambayi kansa, don me Sarkin Saudiyya zai biya wa har mutane dubu ɗari bakwai da hamsin (750,000) aikin Hajji? Wanda yake da ilimi game da intanet kuwa, zai fahimci cewa:

a. Babu abin da ya haɗa wannan liƙau ɗin da gwamnatin Saudiyya.

b. Kafar intanet ɗin (trny.ke) ba ta yi kama da amintacciya ba.

Domin yanke shakku, wannan littafin ya bibiyi liƙau ɗin. A ƙarshe sai ya ‘sauya akalar neman’ (redirect) zuwa wata kafar intanet ta damfara wadda aka buɗe da suna kamfanin MTN. A duba hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 3.7: Kafar intanet ta damfara da aka buɗe da sunan MTN

Kafar intanet ta damfara da aka buɗe da sunan MTN

Madogara: An ɗauko ranar 14 ga Disamba 2024 daga https://ng-app.com/DoMedia/nairarain-Landing-en-doi-web?origin_banner=1&trxId=7219419&trfsrc=DOMEDIA

A hoton da yake sama, za a lura da yadda aka kwaɗaitar da mutane cewa za su samu naira dubu goma (N10,000) yayin da suka sanya naira ɗari (N100) kacal. Waɗanda suka yaudaru har suka kai ga ƙoƙarin yin hakan, za a nemi su saka keɓantattun bayanansu. Da zarar sun saka kuwa, ‘yan damfarar da suka ƙirƙiri kafar za su yi caraf da su![1]

Wata babbar hanyar da ake bi domin tatsar bayanan mutane daga kafafen intanet ita ce ‘basajar kafar intanet’ (website/blog cloning). Masu wannan salo za su kwaikwayi wata amintacciyar kafar intanet sak yadda take yadda idan mutane suka hau kanta, za su yi tunanin wancan amintacciyar da suka sani ce. Ko bayan siffar cikin kafar, sukan sanya masa sunan kafar intanet (domain name) mai matuƙar kama da na ainihin (misali ams0shi.com ko amsashi.com a maimakon amsoshi.com).[2]

Yayin da suka sanya bayanansu na shiga akawun (login details), to za su tafi hannun masu wannan shirin damfara. Haka ma abin zai kasance ga duk wasu bayanai da suka sanya a kan kafar.

‘Yan damfarar kan intanet da suka yi basajar wata kafa sukan yi amfani da wasu dabaru da za su kai ga mutane sun shiga wannan kafar basaja. Fitattu daga cikinsu su ne:

a. Suna iya tura saƙo ga mutum ta imel ko wata kafar sada zumunta (da sauransu) ɗauke da liƙau ɗin kafar basajar.

b. Suna iya bin matakan ƙwarewa a intanet domin kafar basajar ta samu babban matsayi a injunan nema a kan intanet (wato ta bayyana a sama sosai) ta yadda mutane za su gan ta a farko-farko, har a samu masu shiga.

c. Suna iya amfani da tsarin sabis ɗin Wi-Fi na kyauta a wani wuri. Duk wanda ya yi amfani da wannan Wi-Fi ɗin, za su ga duk abubuwan da yake gudanarwa da na’urar a kan intanet. Suna iya amfani da wannan damar wajen sauya akalar nema da ya tura zuwa kafar intanet ɗinsu ta basaja.

Akwai wasu fasahohi da ake amfani da su yayin yin basajar kafafen intanet. Waɗannan fasahohi su ne:

a. HTTrack (https://www.httrack.com/)

b. Social-Engineer Toolkit (SET) (https://github.com/trustedsec/social-engineer-toolkit)

c. BlackEye (https://github.com/An0nUD4Y/blackeye)

d. HiddenEye (https://github.com/DarkSecDevelopers/HiddenEye)

e. Evilginx2 (https://github.com/kgretzky/evilginx2)

f. Wget (https://www.gnu.org/software/wget/)

g. Weeman (https://github.com/evait-security/weeman)

ii. Tatsar Bayanai Ta Amfani Da Manhajoji

Manhaja aba ce da take da siffar kafar intanet, wanda ake iya saukewa a kan na’ura kamar waya ko kwamfuta domin amfani da ita. Wannan yana nuna cewa, ta bambanta da kafar intanet kasancewar ita kafar intanet, dole ne a hau ta kan burawuza kafin a iya buɗe ta. Ita kuwa manhaja tana cin gashin kanta a inda za a iya buɗe ta kai-tsaye yayin da aka sauƙe ta a kan na’ura.

Manhajojin da suka kasance amintattu, an fi samunsu a ɗaya daga cikin fitattun rumbunan manhajoji da ake da su. Wannan ya danganta da nau’in na’urar da mutum yake amfani da ita. Fitattun rumbunan manhajoji su ne:

a. Google Play Store (https://play.google.com/store)

b. Apple App Store (https://www.apple.com/app-store/)

c. Amazon Appstore (https://www.amazon.com/appstore)

d. Samsung Galaxy Store (https://www.samsung.com/global/galaxy/apps/galaxy-store/)

e. Microsoft Store (https://www.microsoft.com/store)

Ko bayan waɗannan akwai wasu amintattun rumbunan manhajoji. Amintattun rumbunan manhajoji sukan yi ƙoƙarin tabbatar da inganci da amincin manhaja kafin sanya ta cikin rumbun. Sukan bincika domin tabbatar da ba ta illatar da na’urori, sannan ba ta damfara ba ce.

A ɓangare ɗaya kuwa, ‘yan damfara sukan samar da manhajojin da za su iya amfani da su domin tatsar keɓantattun bayanan mutane. Suna iya basajar wata sananniyar manhaja, ko kuma su ƙirƙiri wata bisa yaudarar cewa za a amfana da ita. Sau da dama yayin girke ire-irensu a kan na’ura (misali wayar salula), gargaɗi yakan bayyana da yake nuna cewa manhajar tana iya illata na’urar.

iii. Tatsar Bayanai Ta Hanyar Kiran Waya

Damfara ta hanyar kiran waya ba baƙon al’amari ba ne ga Hausawa. Wannan salo ya yi matuƙar yaɗuwa. Duk da haka, a kullum ‘yan damfarar suna ƙara yi masa kwaskwarima. Wasu daga cikin fitattun misalai sun haɗa da:

a. ‘Yan damfara sukan kira mutum a waya da sunan cewa daga bankinsa ne ko kuma su nuna daga wani kamfani ne da yake mu’amala da shi. Daga nan za su buƙaci da ya tura musu wasu bayanai keɓantattu. Bayanan da sukan neman za su iya kasancewa lambar katinsa na ATM ko wani abu mai kama da haka. A bisa haka ne ma bankuna suke yawan turo saƙon gargaɗi cewa ba za su taɓa tambayar bayanan mutum ta waya ba. Duk wani bayanin da suke buƙata, za su nema ne yayin da kwastoma yake gabansu a cikin banki.

b. ‘Yan damfara sukan kira a waya da sunan cewa iskoki/aljanu ne. Yayin da mutum ya yaudaru, za su bi wasu dogin tsararrun hanyoyin da za su kai ga samun abin da suke buƙata daga gare shi.

c. ‘Yan damfara sukan kira a matsayin cewa tsofaffin abokai ne da aka daɗe ba a haɗu ba. Za su iya hakan domin damfara kai-tsaye (idan sun riga da sun tattara bayanan da suke buƙata domin gudanar da damfararsu), ko kuma domin tatsar bayanai.

iv. Tatsar Bayanai Ta Hanyar Kutse a Na’ura

Ƙwararru a fannin kutse a na’ura suna iya tatsar bayanai daga na’urar mutum ko da bai hau wata manhaja ko kafar intanet ɗinsa ba. Akwai hanyoyi masu yawa da suke iya bi domin yin kutse. Duk da haka, da yawa daga cikinsu suna iya yiwuwa ne kawai yayin da aka samu wani naƙasu ko sakaci daga ɓangaren mai na’urar. Suna iya samun nasara yayin da:

a. Mai na’ura ya yi sakacin da aka gano ko aka samu bayanansa na shiga akawun

b. Mai na’ura ya yi sakacin danna wani saƙon da yake ƙunshe da ɓoyayyiyar manhajar kutse

c. Mai na’ura ya yi sakacin amfani da Wi-Fi na ‘yan damfara



[1] An damfari Hausawa da yawa ta amfani da salo makamancin wannan a sanadiyyar 2go a shekarun 2009 zuwa 2015 a lokacin da yake matuƙar tashensa. An tattauna wannan batu a ƙasa a ƙarƙashin 3.2.1.2.

[2] A nan za a iya lura da cewa bambancin da yake tsakaninsu kaɗan ne. A na farko an yi amfani da sifili (0) domin ya maye gurbir /o/. A na biyu kuwa, an yi amfani /a/ domin maye gurbin /o/.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments